Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 47

Chapter 47

Garkuwa Book 1 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

muka iso sabida ya sani dole sai mun taho nan." Murmushi Ummi tayi kana tace. "To Haroona ka kiyaye batun tsaida salla kan lokacin ta, kaji ko?." Hararan Sheykh yayi tare da cewa. "To Ummi". Ita kuwa Jakadiyarsu cikin muryar kula tace. "Haroona yaushene bikin naku kam?". Kanshi ya ɗan shafa kana yace. "Uhum Ummi saura watanni bakwai in Allah ya yarda, Ni dai zanyi aure in bar babban tuzurun". Bai kulashiba saima tashi yayi ya nufi bedroom. Ita kuwa Jakadiyarsu cikin yin ƙasa da murya tace. "Yauwa ya dai-dai ta da Jazrah ko?". Baki ya ɗan turo tare da cewa. "Uhum Ummi gudowafa yayi, kuma wlh in ba dagewa kukayiba, wannan bauɗeɗɗen ɗan naku, ustazu bazaiyi aureba, mutun duk yadda akayi dashi sai ya kauce". Kai ta ɗan juya ta kalli ƙofar ɗakin daya shigan, cikin yin ƙasa da murya tace. "Uhum ga zahiri ko mgnar aure akayi sai ya bar wurin." Haka sukayi ta hira da yake akwai sabo tsakaninta dashi. A sashin Hajia Mama kuwa, ita da kanta da kuma, Batul suka shiga kitchin sai kuma yardaddun hadimanta mutun biyu. Breakfast mai kyau suka, haɗawa Sheykh. Yayinda Aunty Juwairiyya ma ta shiga kitchin da kanta, ta haɗa mishi breakfast. Jakadiyarsu kuwa da Jamil da Jalal da Affan Haroon suna falon sunata hirarsu. A tare hadiman Mama dana Juwairiyya suka kawo, abin kari. Suna fita ba da ɗewa, hadiman Gimbiya Aminatu kakarsu kenan. Suka shigo suma da abun kari. Suka jera komai kan babban dinning table dake dinning area'n dake falon. Bayan sun fitane. Suna cikin hira, sarƙin ƙofa, ya shigo, ya shaida musu, ga saƙo an kuma kawowa. Jamil ne ya bada daman a shigo. Nan ya juya ya fita, jim kaɗan, aka turo ƙofar. Cikin mamaki suka zuwa ƙofar ido. Ganin M....! *Wannan shafin nakine ke ɗaya MRS SARDAUNA, Sheykh yana godiya da soyayyarki gareshi. Domin duk masoyanshi bayanki sunka biyo* By *GARKUWAR FULANI* 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 🐄🕊️🌈🦚🐍🤴🏻💘 *GARKUWA* PAGE 14 NA *AYSHA ALIYU GARKUWA* 📝🍇🐄🌈🦚🤴🏻💘 *Daga gobe ne, FREE PAGE zai ƙare, in da zan saki page 15-16 daga su kuma in kin sake ganin littafin GARKUWA a woje ba cikin groups ɗin da na buɗe nasa wanda suka biya ba, To na satane, na waɗanda basu san darajar iyayenka da girman Allah da Manzonsa suka fitar ne, to ke kuwa in kin san darajan iyayenki da girman Allah da Manzonsa, kada ki karanta na sata, akwai group ɗin ɗari uku kacal ban tsauwala ba dan nasan halin TLC da muke ciki a ƙasar nan ga mai wadata wacce take da dama taga zata iya biyan na Special Group 1k ne rak. Zaki turo ta asusuna 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, sai ki turo shaidar biyanki ta wannan number dai 09097853276, kuma ƴan 300 zaku iya turowa ta ac na ɗin, in kuma baki da dama to turo katin mtn na ɗari uku kacal ta wannan number dai 09097853276. Dan Allah da Manzonsa in kin san zaki fitarmin da littafi biyoni PC ki gaya min wlh zan baki kuɗinki in fiddaki group salum-alum, ina kuma jin san saya zakiyi ki fidda na roƙeki da Allah da Manzonsa wanda bayansu babu wani kada ki saya ki riƙe kudinki ki barni in riƙe littafina🤗* FREE PAGE, daga gobe dai zasu ƙare ki biya kuɗin ki in kinada niyan saya. Ganin Mom ce, yasa fuskokinsu ya baiyana abinda ke cikin zuƙatansu. Cikin ƙasaita, Mom ke tafiya, hadimanta biyu na biye da ita da manyan kuloli na al'farma. Jakadiyarsu ce tayi murmushi mai kama da yaƙe, tare da rusunar da kai, cikin girmamawa tace. "Barka da shigowa, Gimbiyar ahlin masarautar Joɗa. Cikin isa da ƙasaita ta gyaɗa mata kai bayan ta zauna, gefen Jamil dake ruggume da waya kamar, abin masifa, Kanta ta ɗan juyo ta kalli Jalal daya haɗe fuska, Juwairiyya yace ta ɗan gyara zamanta tare da cewa. "Barka da safiya Mom". Murmushi mai wuyar fassarawa tayi, tare da taɓe baki, a gyatsine tace. "Barka dai". Sai ta kuma juya ta kalli inda Jakadiyarsu ke zaune, cikin isa tace. "GARKUWAN YA FITANE?". A daƙile Jalal yace. "Yana ciki kuma hutawa yakeyi". Ko inda yake bata kallaba tace. "Jakadiya ina buƙatar ganinshi, yanzu". Cikin biyeyyarta tace. "Ranki ya daɗe, in zaton bacci yakeyi". A taƙaice tace. "A tadoshi". Haroon dai ido ya zuba musu yana ganin ikon Allah, kowa ji da kai da ƙasaita. Juwairiyya ce ta ɗan kalli Haroon ɗin cikin sanyi tace. "Ukhti, shiga ka sanar mishi". To kawai yace, kana ya miƙe ya shiga bedroom ɗin, da Sheykh ya shiga mituna ashirin baya, kasake yayi a bakin kofar ganin babu kowa a cikin bedroom ɗin. A hankali ya tako ya shiga ciki, bakin ƙofar bathroom ya ɗan matso, kunnenshi ya kasa wai a lissafinshi ko zaiji mitsin ruwa. Shiru babu kowa a ɗakin da kuma bathroom ɗin. Ko ina yayi tsit sai wani fitinenne sanyi daya cika ɗakin, wanda sai sautin A/C dake busawa shuuuuu a hankali. Waige-waige yayi ganin babushi babu, motsinshi ne, ya sashi ɗan ɗaga murya yace. "Jabeer! Jabeer!! Jabeer!!!". Jin shirune yasashi sa hannunshin ya ɗan ƙonƙosa ƙofar bathroom, still shiru. Hakane yasa ya ɗan tura ƙofar, wayam baya ciki. Ganin hakane ya sashi juyawa, shima ɗin cikin takun ƙasaitar ya fito gefen Jalal ya zauna tare da kallon Juwairiyya,kana yace. "Baya cikifa". Wani irin kallo Mom tayi mishi, wanda yake nuna abinda ke bakinta, cikin ɗan sakin fuska yace. "Allah kuwa Mom baya ciki". Kanta ta gyaɗa tare da yunƙura ta tashi tsaye. Kana a hankali tace. "Uhummm". Sai kuma ta juya ta kama hanyar fita, hadimanta na biye da ita a baya. Har yaje bakin ƙofa ta juyo tare da cewa, Ga breakfast ɗin Garkuwa". Haroon ne yayi godiya kana ta juya ta fita. Cikin mmki Haroon ya kalli Jamil tare da cewa. "Jamil baya cikifa". Murmushi Juwairiyya tayi tare da cewa. "Kun dai haɗa baki, kunƙi ya fito, ya gaisa da Mamanshi". Jalal ne ya ƙara tsuke fuskarsa tare da cewa. "Mamarshi ko makirarshi". Jakadiyarsu ta ɗan gyara zama tare da cewa. "Uhummm, sanin halin mutum sai Allah". Sai kuma ta kalli Haroon tace. "Haroona kace mishi yazo yayi karin kumallo, kace mishi daga sashin Gimbiya Aminatu ce, ga kuma na Juwairiyya". Cikin jaddawa yace. "Allah kuwa Ummi baya cikifa". Da mamaki a fuskokinsu suka ɗan kalleshi, Jamil ne yace. "Bai fita bafa". Juwairiyya ce, ta amshi zancen da cewa. "To kuma dai bai biyo nanba, tunda ya shiga bai fitoba". Shi dai Haroon Ido ya zuba musu, ganin kamar basu yarda Jabeer baya cikiba. Kuwa hakanne, saida Jamil yaje ya duba babu shi a ciki babu alamarsa. Cikin tarin mamaki ya sanar musu, baya nan ɗinfa. Jalal ne ya ɗan kauda tunaninsu da cewa. "To kunata surutu, ta ina zakuga sanda ya fita, kai Jamil hankalinka duk na kan waya ina zaka ganshi." Cikin kula Jakadiyarsu tace. "Kaga fitarsane?". Baki ya ɗan taɓe tare da cewa. "Ni ban ganiba, na dai san shi ba kuɗi bane bare ya ɓata, ku jira zaku ganshi". Da haka sukayi amanna dan a zatonsu yaga fitarshi kawai bauɗewarshi ne yasa bazai sanar musuba. A can cikin fadar Masarautar Joɗa kuwa, falon sashin mai martaba Lamiɗo, cike yake da ƴaƴanshi maza, ziryan, wanda

Table of Contents

Chapters

185 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});