Chapter 124
Chapter 124
ka kontar da hankalinka. Tunda ka iya jure bulalin aiko tabbas dole ka aureta, babu shakka dole sai ka aureta, bazai yiwu a dakeka a kantaba sannan ka barmusu itaba." Cikin jin haushin wannan fitinenne tsohon ya kwace hannunshi daya riƙe tare da cewa. "Haka kenan kullum zanyi ta wahala a bisa wasu dalilanka da bana addiniba, me ruwanka da dukan da akayi min, ba dai kai-kasa dole aka dakeni ba". A hankali Galadima yace. "Eh da kuma bakayi kukaba, baka guduba, yau kuma kasa yayi kuka ya gudu ai dole ka aure matar da a kanta aka haɗaku gasar, tunda mu dai ba sakarkaru bane, bare ace bamu san dokar gasar Shaɗi ba." Wayyo Jabeer ji yakeyi tamkar ya mammake tsoffin nan dan tarin baƙin ciki. Rai a ɓace yace. "Bakufa fini sanin kainaba, tunda nace muku bana son aure, bazan kuma yi aureba, to ku barni mana, rayuwata ce ko taku, ko dole ne duk wata matsalata da sirrin rayuwata sai kun sani! Nace muku bana son wannan garin na tsani garin bana son mutanen garin karankatab ɗinsu. Bani babu su, in kuma kukayi gangancin cusa min wata muguwar yarsu, tabbas! lallai ilaihin! A kanta zan rama sauran bulali ashirin da wancan ƙaton gardin ya min, hamsin, ni a talatin ya gudu". Kai Jadda ya girgiza tare da cewa. "Ka rama mana kaida matarka, ka rama ka kuma jinyace ta". Shiru sukayi sabida jin muryar Dr Aliyu da kuma Galadima da Arɗo Bani da Bappa suna tabbar wa juna lfyar yaransu, cikin Mamaki ya kalli Galadima dake cewa. "Muma ɗanmu lfyarshi lau, Namiji ne". Cikin sanyi Jabeer yace. "Ji maƙaryacin tsoho, wai lafiyata lau, ko yaushe ya zama likita ya gwadani. Harda wani karkacewa yana zuba ƙarya ko farin gemunshi bai martaba-ba". Jin Abbanshi ya daki gefen ƙafarshi ne yasashi yin shiru. A nan a gabanshi a gaban mahaifinshi. A gaban dubban al'ummar fulani makiyaya daketa tsastsafo tako wani sashi na duniya, a kuma gaban Lamiɗo da tawagarsa hakama Jalaluddin da tawagarsa. Aka ɗaura auren Muhammad Jabeer da Aysha. Bisa koyarwan addinin Musulunci. Sosai su Jalal, Jamil, Hashim, Haroon, Sulaiman. Sukayi mamakin wannan aure na ba zata. Ba zato ba tsammani. Bayan an gama dai-dai-ta komai an ɗaura auren ne, kuma. Lamiɗo ya kalli Arɗo Bani, cikin girma da ƙasaita yace. "Yanzu zai tafi da matarshi." Cikin sanyi da al'hini Bappa yace. "Allah rene yanzu kuma!?". Galadima ne ya amshi zancen da cewa. "Haƙƙun yanzu zamu tafi da ita!". Arɗo Bani ne yayi murmushi mai cike da jin daɗin yace. "To ba laifi ai, muje a fito muku da ita". Shi kuwa Bappa ido ya zuba musu. Dan shi a zatonshi ba yau zasu tafin mishi da Shatunsa ba. Nan duk suka ɗunguzuma, suka shiga motocin. suka nufi ƙofar gidansu Shatu. Ya Salmanu kuwa, tuni ya shiga cikin gidan su. Ya shiga ɗakinshi yana ta kuka kamar yaro. Bai tsamci haka abin kan iya juyewa ba, Ba'ana ya rasa Shatu shima ya rasata. Suna isa ƙofar gidansu, duk motocin suka tsaya. A hankali Bappa da Arɗo Bani suka kutsa kansu cikin gidan. A tsakar gidan suka samu. Shatu na zaune dan dawowarta kenan, hannunta tasa ta tallabe haɓarta ta zubawa su Junainah ido, shigowarta gida kenan daga dawowarta. Cikin Ɓadamaya su Binto suka shigo gidan a guje suna ce mata wai an ɗaura aurenta da ɗan sarkin da akayi gasar Shaɗi dashi. Jin hakane yasata yin murmushi tare sauƙe dogon ajiyan zuciya na gajiyar tafiyar da tayi, ido ta lumshe tare da cewa. "Auren kuma wasane, da zai zama an aura min wani wanda ba'a san halinshi ba, ko ƴar tsana ma ai ba'a aurar da ita a hakaba bare ni". Ta faɗi mgnar cikin fargaban ganin yadda suketa rantse mata. Duk da bawai ta yarda da zancensu bane. Junainah kuwa dariya takeyi tare da ɗan tsalle-tsallenta tana cewa. "Yeeh Auren Addana yazo, zanyi gayyan fati muyi gaɗa". Cikin zuba musu ido, ta zauna gefen, Ummey dake ta Binta da ido, cikin sanyi tace. "Ummey na dawo! Ya jikin naki!?." Da sauri ta gyara zamanta tare da zubawa Ummey ido, cikin mamaki take kallonta ganin idanunta nata zubda hawaye ne, yasata cikin ruɗani da tashin hankali da fargabar abinda ke shirin faruwa da ita da rayuwarta. A kiɗime tace. "Ummey meya sameki? meya saki kuka? Jikin ne yake miki ciwo?." Sam Ummey bata iya mgna ba, sai kukan da takeyi, hakanne yasa zuciyar Shatu karaya, cikin rauni wasu hawaye masu ɗumi suka fara tsiyayo mata. Hakan ya ƙara ingiza kukan Ummey hakama, Junainah sai ta raɓa gefensu tayi, zurui a zatonta aure abun daɗi ne ba kukaba to gashi taga su kuma kuka sukeyi. Sosai Shatu takeyin kuka mai tarin dalilai. Suna isa Bappa yasa hannunshi ya kamo nata, cikin sanyi yace. "Taso kizo". Ido cike da hawaye ta mike tsaye bisa umarnin Bappa. Shi kuwa Bappa cikin sanyi ya kalli Ummey da Junainah yace. "Kada kuyi kuka, kuyi mata addu'o'in samun nasara a cikin wannan al'amari, muyi mata fatan aurenta ya zamo haske ne a rayuwarsa shi mijin da ahlinshin baki daya, fatanmu aurenta ya zamo ƙungiyar da zata jawo gskya cikin raminda aka binneta ya fito da ita kowa ya gani." Shiru Ummey tayi sai hawayen da suke kwaranya. Hakama Shatu hawayenta wani na korar wani. Ita kuwa Junainah faɗawa jikin Ummey tayi sukaci gaba da zubda hawaye. Bappa kuwa hannunta yaja suka juya suna nufi hanyar fita. Da kayanta na ɗazu wanda taje Genaral Hospital Ɓadawaya dasu, hatta hand bag ɗinta na rataye a kafaɗarta wayarta na ciki. Cikin mamaki take bin bayan Bappa, tare da yin taku a hankali tana bin bayanshi yadda yake jan hannunta. Arɗo Bani kuma na biye dasu a baya. Suna fitowa ƙofar gidan, Haroon da Jalal suka juyo suka kalli juna, Cikin tarin mamakin ganin kamar yarinyar ɗazuce. Shi kuwa Sheykh Jabeer yana zaune cikin motar, shi ɗaya dan duk sun fita. Da sauri ya dafe saitin ƙahon zuciyarshi jin ta tsananta bugawar da yakeyi. A hankali ya maida bayanshi ya jingina da sit ɗin tare da rufe idonshi. Yana mai jin sanyin A/C na ratsa mishi jiki da jini da zuciya. Amman duk da haka zuface ke tsastsafo mishi a jikinshi sabida bugun da Zuciyarshi keyi ya wuce misalin. A hankali ya juya kanshi ya kalli gefen hagunshi inda yaga motar Jadda da kuma Dr Aliyu ne da Barrister Kamal ke jere a wurin. Bappa kuwa a hankali yake taku, yana nufo inda Lamiɗo ke tsaye Dogari na riƙe masa da laima, Ɗanzagi da fadawa na zube a kasa. Ita kuwa Shatu cikin rawan jikin jin idanun mutane na yawo a jikinta dan ma Allah yasa akwai niƙab a fuskarta. Take bin bayanshi. Shi kuwa Sheykh Jabeer yadda suke ƙara matso inda yake haka bugun zuciyarshin keta tsananta. Suna isa gaban Lamiɗo Bappa ya miƙawa Lamiɗo hannunta cikin sanyi da nitsuwa da taushin lafazi yace. "Allah rene, ga Aishatu matar Muhammad Jabeer. Gata amana bisa jagoranci ka, nasabarka da yardarka. Da kamala da nitsuwa da na gani a fuskar yaron yasa naji ƙarfin guiwar baku aurenta. Ba tare da fargaba ba, yanzu kaine kaka kuma jagora a gareta". Sai ya kuma nuna Barrister Kamal da shima yana cikin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185