Chapter 16
Chapter 16
tayi ta iso tsakiyar Office ɗin, ido ya fara jujjuyawa kan table nashi yana mai jin wani masifeffen bugun zuciyarshin dayasashi hatsala cikin ɗan ɗaga murya yace. "Ke da Allah kiyi sauri". Jin hakane yasa ta kara saurinta, ai kuwa da sauri ya dafe ƙirjinshi lokacin da ta iso gab dashi, cikin ranshi ya kuma cewa. "Hasbunallahiwani'imanwakil". A zahiri kuwa, da kai ya nuna mata ta kuma matsowa, ba musu ta matso, yatsarshi ya jujjuya mata alamun ta juya mishi baya, still babu musu ta juya, a hankali ya murza kujerar da yake kanta, ya juyo ya fuskanci bayanta, dai-dai saman mazaunanta ta sama ta ɗan gefe kaɗan, ya saita, tsinin bakin allurar, cikin iyawa da gwarewa dan salonshi ne baya taɓa yarda ya kalli fatar jikin wanda zaiyiwa alluran ta saman tufafinka yake zira allurar, shiru tayi tana jin yadda, allurar ya ratsa dogon rigar jikinta ya bada sautin tub alamun ya huda rugar, a hankali ta kuma jin ya huda, dogon wondon jikinta tub, sai kuma taji ya sauƙa kan pantien jikinta, daga nan taji ya ɗisa bakin allurar kan fatarta, rumtse idanunta tayi da azaban ƙarfi sabida, wani zafi da taji yana ratsata, bawai tana tsoron Allurar bane, sai dai hannunshi yanada masifar zafine, kana shina ruwan alluran irin mai, mai-mai ɗinanne kuma duk cikin allurai yafi zafi. Da ƙarfi tace. "Wach Allah na zafi-zaffi." Wani irin azaba taji lokacin daya fara cusa mata ruwan allurar a jikinta, babu zato babu sammani yaji tasa hannu damanta ta cabki hannunshi dake mata alluran hannunta na hagu kuwa yarfashi take tare dasa kuka da sauti tace. "Wayyo Allah na, ka bari bana so zare Allurar nan zafi nakeji". Ta ƙarishe magar da zurma sakalin ihu". Bugawa da zuciyarshi keyi yana bada sautin dib dab dib dab dib dan shine ya kusan hallakashi lokacin data riko hannunshi, da sauri ya tura mata ruwan kana ya zare Allurar da ƙarfi. Sannan ya miƙe tsaye, sabida muddin yana kusa da ita babu makawa wata ƙil zuciyarshi zata faso ƙirjinshi ta fito woje. Wani dogon tsaki yaja tare da juyawa ya bi gefen Nos ɗin ya fice. Itama da sauri tabi bayanshi bayan tasa hannu ta amshi ledan magungunan. Shi kuwa da sauri yake tafiya sabid iya yedda yake nesanta da ita iya yadda kirjinshi ke dai-dai ta bugawa, sai kuma tsinƙewa da zuciyarshi keyi babu ƙaƙƙautawa. Ita kuwa AYSHA da sauri ta nufi sashin makwancin ɗaliban Hostel dake cikin makarantar sabida ta fara jiyo alamun bakonta ya iso. Baba Ado kuwa drevernshi yana hangoshi ya tashi ya buɗe mishi marfin motar, yana zuwa, ya shiga, maida kofar Baba Ado yayi ya rufe sannan ya shiga yaja motar suka fice daga harabar asibitin. Ita kuwa Aysha tana shiga Side ɗinsu ita da Rafi'a, ta samu Rafi'a bata falo da alamun tana kitchen nasu, dan tajiyo ƙamshi alamun tana ɗan dafa musu abinda zasuci ne. Kai tsaye bathroom ta wuce, tabbas kuwa baƙon ya iso, dan haka ta nitsu ta gyara jikinta, bayan ta gama ne ta miƙe a hankali ta kwance niƙabin tare da fara zare dukkan kayan jikinta dan yin wonka, Aysha farar ba fullatanace irin farare ƙal-ƙal ɗin nance, gashin kanta kuwa mai tarin yawa da tsawone baƙine sit mai sheƙi, yanada cika, jikinta ɗan fiyau, sai dai tanada welcome and bey bey masu girma da cika, cikinta kamar babu hanji a ciki ɗan fiyau dashi, breast ɗinta tirtsa-tirtsane masu cika tab-tab kuma irin mai gindin tasa ɗinnan wanda da alamun ba masu zubewa bane, domin suna nan cas dasu, kamar zasu tsone idon mai gani, tanada tsukekken ƙugu da kyawawan mazaunai, sawonta dai-dai musali baza'ace mata doguwa ba sam, kuma baza'a ce mata gajera sosaiba in tana kusa da dogo dai za'a iya kiranta da gajera. Fuskarta kekyawa ce irin kyan da babu namijin da zai gani ya cire ido, hancinta dogo har kan ɗan ƙaramin bakinta mai jajayen tausasan laɓɓa idonta manyane sai dai ba ƙattiba, zirin idonta wurinda akesa kolli jane mai kyau, shiyasa yake ƙara baiyana farin idonta bakin ciki kuwa bakine sitik sai dai ɗan ƙaramin ɗigon cikin bakin shi kuma ruwan ƙasane wanda yakeda sirri namu samman. Gashin idonta zara-zarane, gashin girarta kuwa irin mai W ɗin nanne kamar na Kajol, bi ma'ana yana haɗe bisa karan hancinta, Tanada fararen haƙora masu kyau suna jere reras dasu tanada dimple ɗinta mai ɗan karen kyau. Idanunta kuma ko yaushe kamar maijin bacci suke. Wonka tayi kana tayi al'wala dan ko bata salla bata zama babu al'wala. Tana fitowa ta kimtsa jikinta kana ta zura tattausan doguwar riga. Tana kokarin fitowa falo Rafi'a na ƙoƙarin shigowa da sauri Rafi'a ta zaro ido tare da cewa. "Yaushe kika dawo?". Hararanta ta ɗanyi tare da cewa. "Ba dai kin gudo kin dawo kin barni ni ɗaya ba". Cikin tausayawa Rafi'a tace. "La wlh yanzu nake ƙoƙarin komawa, na dawone in ɗan dafa mana abinda zamuci in mun dawo, sabida naga rabonki da abinci tun jiya, shiyasa kina shiga Office ɗin Dr na dawo". Kai ta gyaɗa alamun gamsuwa kana tace. "Na dawo a guje fa, wannan Sheykh ɗin hannunsa zafi kamar allurar mashi yakewa mutun". Zaro ido na mamaki Rafi'a tayi tare da cewa. "Shida kanshi ya miki?". Kai ta gyaɗa tare da cewa. "Eh". Cikin taɓe baki tace. "Lallai yau kin tashi da ƙafar dama, gashi kuwa naga har kin worke". Wucewa sukayi zuwa tsakiyar falon, cikin sauƙe numfashin Aysha tace. "Ba doleba yadda yake tura ruwan alluranshi nan kamar mai tura mai a mota, kuma ina dawowa nasha mgni, sannan abin ya iso, kinsan dama wuyar kafin ya isone". Dariya Rafi'a tayi tare da cewa. "Kinji allurar manyan likitocin da duniya keji dasu dai". Uhum kawai tace sannan suka fara cin abinci, sunaci suna hira. Cikin hirar tasu ne Rafi'a tace. "Anjima da yammafa jirginmu zai tashi". Da sauri Aysha tace. "Haba dai Rafi'a dan Allah ki bar zuwa hutunnan mana ki bari mu zauna, wallahi in kin tafi nima dole in tafi kuma ke kin san matsalar da nake da ita a gida ko Mamey ma da mukayi waya dazu cemin tayi kar in koma hutu Rugarmu, in zauna a makaranta". Cikin sanyi Rafi'a tace, "Wallahi nayi kewar gidane Aysha, shekara guda kenan banje gidaba fa". Cikin sanyi Aysha tace. "Haka ne kam ba, matsala, ai hutun sati ukune, kina tafiya yau nima gobe zan shirya zan koma Rugarmu". a haka sukaci gaba da hira suna cin abinci. Ƙarfe huɗu dai-dai na yamma jirginsu Rafi'a ya tashi daga Ɓadamaya international airport, zuwa Farazan state. Ita kuwa Aysha taci gaba da shirinta ba tare da ta gaya mutanen gida cewa zata dawo ba. Kaya kaɗan ta ɗiba dan tanada kaya a gida, system ɗinta da wayarta da kuma kaya kala biyu kawai ta ɗauka, sai yan ƙananun abubuwan, ta da tayi nufin sai gobe zata koma. Amman ina tafiyar Rafi'a yasa taji bazata iya zaman kaɗaicinba, dan haka huɗu da rabi, ɗaya daga cikin motocin dake maida ɗalibanda in gidajensu na kusane ya ɗauke ta. Kai tsaye garin Shikan suka nufa. Tafiyar ba wata mai nisa bace daga cikin birnin Joɗa zuwa Shikan, cikin mitina kaɗan suka isa, Ƙarfe biyara da miti biyar suka isa. Cikin Shikan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185