Chapter 13
Chapter 13
kalli Jamil da Jalal da suke gaidashi, dan su sai yanzu suka haɗu dashi tunda gari ya waye, Tsaɓanin Sheykh da kullum tare suke dawowa masallaci sallan asuba daga nan kuma ɗakin hutunshi suke shiga kakarsu mace ta kawo musu abin taɓawa. Bayan sun gaggaisa ne da mutanen fada, suka fita suka tafi. Sashin kakarsu Gimbiya Aminatu suka nufa. Basu da hijabi da sashin kakar tasu shiyasa kai tsaye suka shiga a falo, suka sameta, Da alamun yanzu ta fitito Dan ga al'kyebba a jikinta ga kuma hadimanta a zagaye da ita. Cikin tarin so da ƙaunar Jazlaan ɗin nata take kallon su, Murmushi tayi tare da cewa. "Miskili kafi mahaukaci ban haushi, kai dai kaji abinda malam zaice kada kace zaka binciki aikin malam". Shiru Jamil da Jalal sukayi, shi kuwa Sheykh ido ya zuba mata. Ita kuwa rausayar da kai tayi tare da cewa. "Eh mana kaji abin da malam yace kada ka duba aikinshi, dazu na gama jin wani wa'azin ka da kayi kan falala da ni'imomin dake cikin aure, kana bayani duk maluntar mutun darajarsa bata cikaba in bashi da aure. Sai najima wa'azin kamar da kanka kakeyi. Meyasa ne Jabeer kayi niyar yin aure mana ka cikata nasabarka da kamalarka da martaba da darajar ka data masarautar Joɗa". Jalal ne ya miƙe tare da cewa. "Ke in anzo gaisheki sai ƙaƙale-ƙaƙalen zance tsiya kika iya ni na tafi dan inada aikin yi". Haratanshi tayi tare da cewa. "Tafi daga nan mai ƙugu kamar buzuzu hegiyar masifa". Hararanta yayi kana ya juya ya fita. Ita kuwa Gimbiya Aminatu. Jamil ta kalla wanda shima ya miƙe yabi bayan Jalal. Shi kuwa Sheykh numfashin ya fesar tare da cewa. "Maganinki ya kare koda saura?." Da sauri tace. "Yauwa magani ya ƙare a kawo min wani". To yace kana ya mike ya fita. Daga bakin harabar sashin kakar tasu, Fadawanshi ke biye dashi a baya har parking lot ɗinsu mai ɗan karen girma da kyau, duk zagaye suke da fulawowi masu kyau. Wasu tsala-tsalan motocine da a ƙalla sun kai su takwas sai sheƙi sukeyi. Da sauri Ado drevernshi ya buɗe mushi ƙofar wata mota mai ɗan karen kyau wacce bada ita ya fita jiyaba, dan ita sai ranakun jumma'a-jumma'a yake hawanta, wannan ta yau mai kalar ruwan tokace sai sheƙi takeyi, yana shiga sauran fadawanshi suka yi yunƙurin shiga motocin dake jere a wurin a gefen wurin wanda dasu akeyi mishi rakiya. Da sauri ya ɗaga musu hannu, cikin in in narsa da in yana saurin mgna yake fitowa yace. "Kkku ba bari ba'a bukatar rakiya". Da sauri suka ɗan rusuna tare da haɗa baki wurin cewa. "Aje lafiya a dawo lfy Allah ya kiyaye gabanka da bayanka Sheykh". Amin Amin yace a taƙaice kana ya shiga motar, sarkin ƙofa ya rufe mishi marfin sannan Ado yaja suka tafi. Suna fita kai tsaye Babbar jami'ar dake cikin babban birnin Ɓadamaya suka nufa. A can cikin makarantar kuwa, Kasan cewar duk ɗaliban jami'ar sun san babban Doctor zai shigo yasa gaba ɗaya harabar asibitin dake cikin jama'ar cika da taron tsala-tsalan ƴan mata ƴaƴan manya, duk mai matsalar lfy tana fatan ya dubata sabida ƙwarewarsa. A hankali wasu ƴan mata biyu suke taku a farfajiyar shiga asibitin, bisa alamu duka ɗayar bata da lfy dan ɗayar na rike da hannunta, kuma a hankali suke tafiya. Cikin tausayawa ɗayar ta kalli wacce ta riƙewa hannun a hankali tace. "Garkuwa ki daure kiyi sauri mu isa, wallahi zamu samu layi da yawa, kuma wannan Sheykh ɗin kasaitarsa nada tarin yawa, yanada doka da ƙa'idoji da tsari, yanada tsauri kan tsare kima da darajar addininshi, daga shigar jikinki in kinyi kuskure kaɗan na shigar kima wallahi bazai dubaki ba. Shiyasa ahlul kitabi dake cikin makarantar nan suke masifar shakkarsa, kinga gashi azahar ta kusa, kuma wallahi ko sarkin garin nanne yazo ya dubashi in dai lokacin salla yayi to tashi zaiyi ya fita ya barshi, gashi shiru-shiru da ido yake hukunta mutun". A hankali wacce aka kira da GARKUWA tasa hannu ta gyara niƙab ɗin dake fuskantar, wacce ta dace da wata kekyawar arabian gawn dake jikinta wanda dama shigartace haka kullum sabida gudun kada wani ya ganta ya tsaida ita dan tasan duk namiji daya nuna yana sonta har lahira ake kasheshi wanda kuma duk Rugarsu akeda yaƙinin Ba'ana ne dan mutunne mai masifar baƙin kishi, yasha sanar mata a kanta zai kashe kowa ba damuwarsa bane da fari duk wanda ya nuna yana sonta da bulalin shaɗi yake korarshi, to yanzu duk wanda yace yana sonta sai dai a wayi gari ya rasu. Cikin sanyin muryar dake nuna azabar da takeji, murya na rawa tace. "Rafi'a, bazan iyaba marata ciwo kamar zata ɓalle, ki sakeni kije ki amsar mana foldana kafin in ƙaraso". Jin haka yasa Rafi'a cewa. "Zaki iya tahowa ke ɗaya?". Kanta ta gyaɗa mata a hankali. Hakan yasa cikin sanyi ta saketa kana ta wuce cikin Hospital ɗin da sauri. Dai-dai lokacin kuma motar Dr Jabeer Habibullah Nuruddeen Bubayero ta kutso kanta cikin farfajiyar. Bayan Ado ya dai-dai ta parking ne a cikin rumfar adana motor da aka rubuta Dr Jabeer a samanta. Ado ne ya fito da sauri ya buɗewa, Sheykh marfin motar, a hankali ya zuro ƙafafunshi ya fito. Cikin nitsuwa ya fara taku yana ratsowa cikin farfajiyar Hospital ɗin. Kasan cewar ta gabas ya fito Aysha kuwa ta yamma ta fito sai ya zama suna fuskantar juna. Yayinda sai sun haɗu wuri ɗaya zasuyi kwana sun fuskanci kudu inda nanne mashigar cikin asibitin. A hankali suke takowa suna fuskantar juna. Sosai ya zuba mata ido sabida ya lura gaba ɗaya jikinta karkarwa yakeyi alamun tsananin ciwo takeji gashi a hankali take taku. Ita kuwa Aysha, tafiya takeyi da kyer sabida azaban ciwo da mararta keyi. Kanta a sunkuye take tafiya, hakan yasa bata san da mutunba a gabanta. Da sauri Sheykh ya tsaya sabida wani irin bugawa da ƙirjinsa ya fara. Ganin ta tunkaroshi gadan-gadan, kuma daga yanayin tafiyarta tamkar zata faɗi ƙasa. Ganin tayi wani irin sunkuyawa tasa hannunta duka biyu ta damƙe mararta da takeji tamkar caccakarsa akeyi da allura. Gefe ya ɗan tsaya yana kallon ikon Allah, ita kuwa GARKUWA rumtse idanunta tayi da karfi, wata fitinenniyar zuface ke tsastsafowa tako ina, a hankali ta fara buɗe idanunta jin kartan da mararta keyi ɗin yana ɗan lafawa, a hankali ta zubawa kyawawan sawunshi idanu, cikin sauri ta ɗago kanta, ganinta tsaye gab kusa da namijin da bata saniba ne yasata ja da baya da sauri tare da miƙe tsawonta cikin firgici murya na ɗan rawa tace. "I'm very sorry". Bai kulata ba, sai kauda kanshi da yayi gefe. Ita kuwa Garkuwa cikin sanyi tace. "Dan Allah kayi haƙuri". Kai ya ɗan gyaɗa mata alamar Uhumm. Ita kuwa cikin sanyi tace. "Uhumm kaima Doctor Sheykh ɗin kazo ganin ne?". Da mamaki ya ɗan kalleta da gefen idonshi, sai kuma ya ɗan juyo kanshi kaɗan jin muryarta a sanyaye taci gaba da cewa. "Muyi sauri mu shiga ance yanada shegiyar ƙasaita da isa, wai ko sarkine yake dubawa in dai lokacin salla yayi tashi yakeyi ya fita". Cikin tarin mmki ya ɗan waro kyawan idanunshi tare da cewa. "Umh". Ita kuwa Garkuwa, hannu
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185