Chapter 103
Chapter 103
rufuba. A hankali yake taku cikin nitsuwa, Lips ɗin shi na ɗan motsawa alamun tasbihi yakeyi. Tafiya mai ɗan tsawo yayi sai gashi ya kuma riski wata ƙofar. Hannunshi yasa ya murɗa key ɗin ya buɗe, ƙofar. Sai ga kuma wata ƙofa irin ta ƙarafuna kana dai iya hango woje. Buɗe wannan ƙofarma yayi. A hankali ya kutsa kai. Wani irin sassanyan ajiyan zuciya mai tsawo yaja ya sauƙe a hankali. Idonshi ya lumshe sabida wani irin sanyi mai masifar daɗi daya ratsa mishi jiki da zuciya. Wani irin ɗan madaidaicin Garden Park ne mai masifar kyau.da sanyi da tsaruwa. Daga nan bakin ƙofar daya fito ɗin. Tayis ne fari tas a malale iya ganinka, sai gefen damanshi da bishiyoyin ayaba masu masifar duhu da sanyi dake jere reras. Gefen hagunshi kuma bishiyoyi mangoro ne irin yan duƙus-duƙus ɗin nan ke jere, Reras. A hankali yake taku yana tafe yana tasbihi. Yana jin kukan tsuntsaye mai daɗin ji yana ratsashi. Tafiya kaɗan yayi sai gashi ya baiyana a wani irin wurin mai masifar kyau. Wasu yan zagayen gini dakalin bulok bibbiyu akayi a ƙalla sunfi hamsin. A ciki ko wanne zagayen akwai bishiyar dabino. Na gabanta inabi na gaban inabi tuppa, kana sai Yazawa, sai kuma na tsada, daga tsada sai na kanya, sai goruba da na giginya. Cikin ko wanne zageyen kuma ƙasanshi koriyar ciyawa ce mai sanyi. Can tsakiyar filin kuma wata iriyar ƙoramace mai masifar sanyi, Ruwanshi na kwance fari ƙal-ƙal bakin wurin kuma jeren bishiyoyi goibane wanda sukayiwa kwaramar inuwa. Gaban ƙoramar kuma wasu irin kujerun silver ne masu masifar kyau da sansi a jere a ƙalla sun kai goma zuwa ashirin. Can gefenshi kaɗan kuma wani shingene aka zagaye da waya. Shuke-shuken gargajiya akeyi a wurin. Nan kusa da ƙoramar kuma shingen farar waya akayi a cikin ta wanda akayi ƴan ɗakuna-ɗakuna a cikin. Tsuntsaye ne a ciki iya ganinka ko wanne da muhalli shin. Kama daga Tattabaru farare ƙal-ƙal. Sai kuma tsuntsu carki jajaye masu kyan launi ga kuma kanari da suke blue. Sai kuma zabbi da suke yawo a ƙasa tako ina. Can bakin ruwan kuma agwagin ruwa ne sunfi ɗari ƙwa-ƙwa. Sai kuma zabbin daji. dangin tsuntsaye dai babu irin wanda babu. Ido ya zubawa tsuntsaye tamkar mai son yin magana dasu. A hankali ya sunkuyar da kanshi jin tattausan gashin Ɗawisun Masarautar Joɗa da ya kai shekaru masu tarin yawa. A hankali ya rusuna tare dasa tafin hannunshi ya shafa dai-dai ƙunɗun Ɗawisun inda wurin yake mai kalar blue mai kyau sabida Sheykh blue ne kalar da yafi so. A hankali ta fara taku, ta juya mishi baya kana ta ɗaga bindinta sama samɓal har yana iya taɓo geminshi. Wani irin takun ƙasaita tayi kana ta buɗa fikafikinta ta bazasu, ta fara tafiya a hankali. Wannan itace suntsuwar da muddin mutun ba jinin Masarautar Joɗa bace, in ka shigo mata gaba gaɗi ba tare da an gabatar mata kai ba, zatayi ta yagune mutun tana caccakarshi. Amman muddin dai kai jinin Masarautar Joɗa ne, kana shiga zata zo gabanka. Tayi maka hakan. Sai dai kuma bayan yin hakan in mutun nada wata zazzafar nasaba a masarautar misali shine sarki maici to in tayi wannan baza fikafikinta takanyi ta zagaya sarki sau bakwai kafin ta tsaya a gabanshi sai sarkin ya umarceta data tafi kafin zata tafi. To babban abinda ya ƙara jazawa Jabeer matsala a rayuwarsa shine, Duk sanda yazo gaban tsuntsuwar Ɗawisun nan sai tayi mishi wannan abin da zagaya sau bakwai abinda a tarihin masarautar sarki kawai yakeyiwa abin. Matsalar abin a gaban Barrister Kamal da kuma Baba Bashiru da Abba sai Lamiɗo ne ta fara yimishi wannan abun. Tofa ta bakin Baba Basiru ne mgnar ta zaga kunnen mazauna masarautar Joɗa. Babban tashin hankalin masu son gadar wannan kujerar, shine yadda side ɗin Jabeer ke kusanci da Garden ɗin da take ciki. Tashin hankalinsu ya ƙara tsananta ne tun randa Suka ga Lamiɗo yasa an buɗawa Jabeer hanyar shiga wurin ta cikin falonshi ba sai ya zagaya yabi hanyar da kowa ke bi ba, Ya zama shida Lamiɗo sune masu hanya kowa daga falonshi zai shiga wurin. A hankali Jabeer yayi murmushi tare da kallon yadda tsuntsuwar ta gama zagayashi kana tazo ta tsaya gabanshi tare da baza fikafikinta. Cikin harcen Larabci yace mata. "Fatana dai ba bauta min kikeyi ba! Domin babu wani abin bautawa da gsky sai Allah, wanda shine ya halicce ni ya halicceki. Ni kuma ba kowa bane face halittarsa, sai dai na kasance cikin halittarsa mai girma da karrama fiye da komai, dan shi da kanshi yace. Walaƙad karramna bani Adam." Wani irin juya kai tsuntsuwar tayi kana ta meda fiffigefa ta rufe, kafin ta juya ta nufi wani kekyawan wurin da aka ware mata, inda take tare da yayanta da mijinta. Juyawa yayi can gefe ya hango wasu yan kyawawan tsuntsaye farare A bakin ruwan. Ga tattabarun sun zagaye wurin da sauran tsuntsayen. A hankali ya zauna a wata kujera mai kamar gado. Kishinƙiɗa yayi kana ya lumshe idonshi yana maijin yadda sassanyan iskar wurin ke ratsashi. Karatun al'ƙur'ani ya fara cikin sassanyan murya mai daɗin sauraro. Umaymah kuwa tunda ta fito, sai ta nufi sashin Hajia Mama, hira sukayi sosai cikin shaƙuwa irin ta yan uwa. Suna zaune a nan Abba ya shigo. Tana ganinshi tai murmushi, shima murmushin yayi tare da cewa. "Maman yara". Cikin sakin fuska tace. "Na'am Yaya". Murmushi mai cike da zafi da ƙuna wanda ya baiyana har kan fuskarshi yayi kana ya zauna gefenta. Gaisawa sukayi cikin danne ababen dake cin ransu. Hajia Mama kuwa, tuni sai hawaye take zubdawa. A hankali Umaymah ta miƙa mata handkin dake hannunta alamun ta share hawayenta. Bayan ta share hawayenta ne, Abba ya miƙa tare da cewa. "Kin gaisa da Mom Imran kuwa? Da Salma". Fuska a ɗan haɗe tace. "A a". Miƙewa yayi tare da cewa. "To muje ku gaisa." Binshi tayi a baya suka nufi inda yace ɗin. A falo suka samu Mom Imaran tana ganin. Sun shigo tare da Hajia Mama tayi wani irin haɗe fuska, cikin nuna ko in kula tacewa Umaymah. "Yaushe kikazo?". A daƙile tace. "Jiya". Kanta ta ɗan kauda tare da cewa. "Ya hanya". Alhamdulillah tace a taƙaice. Cikin kufula Hajia Mama tace. "Mu tafi". Miƙewa Umaymah tayi kana Abba ma ya miƙa sashin Amaryarshi Salma ya nufa da ita. Suna shiga tana jin muryarshi ta fito, da sauri ta nufe shi da nufin zata ruggumeshi da sauri yace. "Ga Umaymah tazo". A take taja birki ta tsaya cikin gyatsine tace. "Ya kike kinzo lfy, ki gaida mutan gida". Cikin wani irin kallo Umaymah tace. "Uhummmm kema ki gaida mutan gidanku". Tana faɗin haka ta juya ta tafi abinta. Hajia Mama na biye da ita. Ita kuwa Salma tana ganin fitansu ta ruggume mijinta. Koda suka koma Side ɗin Hajia Mama bata daɗe a nanba ta nufi sashin Gimbiya Aminatu. To bata fito nan ɗinba sai shabiyu saura. Koda ta dawo Haroon da Jakadiyarsu da Aunty Juwairiyya kawai ta samu a falon. Sai kuma Jalal da Hibba da suke dinning area suna zaune bisa kujerun Dinning table ɗin. Sun sa plet a tsakiyarsu da kofunan tea a hannunsu, alamun sai yanzu sukeyin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185