Chapter 167
Chapter 167
ta tsaya gis gaba ɗaya jikinta karkarwa yakeyi. Cikin tsananin tsoro da firgita. "Hibba ta juya a guje tana cewa. "Wayyo Ummi! Ummi!! Ummi!!! Kizo zakiga yadda Aunty Shatu keyi." Ummi dake falo ita da Aunty Juwairiyya, Kamar daga sama suke jiyo muryar Hibba tana rabka musu kira cikin firgici da razani. Haka yasa Ummi da Aunty Juwairiyya miƙewa da sauri suka nufi corridor'n da suke jiyo muryar Hibba na fitowa. Kiciɓis sukayi a bakin ƙofar falon. Cikin sauri Ummi ta ture Hibba ta wuce da gudu ta nufi cikin ɗakin. Sabida jiyo muryar Jamil na cewa. "Innalillahi wa innailaihi rajiun hasbunallahuwani'imal wakil. Ummi! Ummi!! Kizoooo". Kusan a tare Ummi da Aunty Juwairiyya suka shigo. "Dai-dai lokacin kuma rawan da jikin Shatu keyi ya tsananta. Wani irin kuka tasa tare da tafiya ƙasa luuu zata faɗi Kusan a tare Ummi da Aunty Juwairiyya suka tarota. Bisa jikin Ummi ta faɗi hakan yasa itama Ummi tayi ƙasa ta zauna. Babu abinda suke maimaitawa sai innalillahi wa innailaihi rajiun. A kiɗime cikin tsananin gigita Jamil yace. "Subahanallahi Ummi ta sumafa". Jiki na rawa Aunty Juwairiyya ta juya da gudu babban falon ta fito tare da ɗauko goran ruwan sanyi. Kana ta juyo a da sassarfa ta nufi can. Hibba kuwa a gigice take gayawa Jalal da Ya Jafar abinda ke faru. Da sauri ya Jafar ya tashi ya nufi can. Jalal kuwa ya zauna dan ya lura Hibba tayi masifar tsorita. A ɗakin nashi kuwa, Shiru ta lafe jikin Ummi kamar babu rai koda. Ummi ta yayyafa mata ruwan sanyi a fuskarta, a banza saida ta kuma watsa mata a karo na uku ne. Kafin taja wani dogon numfashi cikin sanyi da tsoro Ummi tace. "Alhamdulillah". Sai kuma ta sunkuyo kanta tana ɗan kiranta. "Shatu! Shatu!! Shatu!!!". Ba amsawa kuma bata buɗe ido ba, A hankali ya Jafar ya zauna gefensu, karatun da yakeyi yaci gaba dayi. Cikin sanyi ta buɗe idanunta. Sai kuma ta yunƙura a hankali ta tashi zaune. Da sauri Ummi ta zaro ido ganin yadda idanunta suka juye a murɗe. Ita kuwa Shatu miƙewa tsaye tayi, cikin rawan sanyi da karkarwa, ta fara zagaya ɗakin a hankali taje baki Bathroom nanma buɗe ƙofar tayi ta shiga. Jim kaɗan ta fito. Idanun suna yadda suke sai dai. Yanzu hawayene keta shatata babu ƙaƙƙautawa. A hankali tazo bakin gadon. Sai kuma kawai sukaga ta faɗa kan gadon a sune! Wannan shine tashin hankali da ba'a samishi rana. Da gudu suka kumayi kanta, cikin firgici da tsananin tsoro Ummi ta ƙara yayyafa mata ruwan. Amman shiru, haka suka tsaya cirko-cirko, shi kuwa Ya Jafar sai gashi yana karatu yana kuka kamar dai yadda yakeyi kafin a auro Shatu a masarautar Joɗa in Sheykh baya nan. Gaba ɗaya sun birkice sunma rasa me zasuyi. Aunty Juwairiyya kuwa itama kuka ta farayi. Jiyo kukanta da na Ya Jafar ne yasa, su Jalal da Hibba shigowa. Ganin tana can yashe kan gado a sumene yasa Hibba ma kuka. Cikin ƙarfin hali Jamil yace. "Aunty Juwairiyya Hibba kada kuyi kuka, kuja hankalin mutane nan. Gashi yau salla ba mamaki akwai mutane a cikin Garden." Cikin tashin hankali Ummi tace. "Bari inje in sanarwa Gimbiya Aminatu abinda ke faruwa, ta sanarwa Lamiɗo, sai in biya in sanarwa Hajia Mama." Da sauri Aunty Juwairiyya tace. "Eh yafi kam". Ta juya zata fita kenan sai sukaji tayi wani irin nakasheshen dogon numfashi mai sassanyan sauti. Da sauri Ummi ta juyo ta dawo jikin sanyi tace. "Shatu! Shatu!! Shatu!!!". Shiru babu amsa sai binsu da ido tayi ɗaya bayan ɗaya. Ganin hakane Jamil ya matso. Tofi ya farayi mata. Ummi kuwa ci gaba da kiran sunanta tayi. Cikin tsoro Hibba tace. "Ummi kinga idonta ya koma dai-dai." A tare sukace Alhamdulillah. Sai kuma Ummi ta kuma kiranta. "Shatu!". A hankali tace. "Na'am Ummi". Sai kuma ta kalli inda take, kana ta juya ta kallesu baki ɗayansu, cikin mutuwar jiki ta yunƙura ta tashi. Murya a sanyaye tace. "Jamil sharan kenan ka tsaya kanata kallona. Gaya min ya za'ayi sharar". Cikin sauƙe tagwayen numfarfashi suka kalli juna, Cikin mamaki Jamil yace. "No ki huta kawai my Aunty zan share". Bata da ƙarfi a jikinta ko ta dage tace sai tayi sharar. Bazata iyaba jikinta duk a mace. Hakane yasa tace to. Hannu ta miƙa Ummi tare da cewa. "Ummi ɗan jamin hannuna mana". To tace tare da kamo hannun. Ta tsaida ita, cikin tafiyar sanɗa ta juya ta nufi hanyar fita. Binta sukayi a baya gaba ɗayansu. Jamil kuwa dube-dube yayi a cikin ɗakin kana. Ya fara tattarewa da kimtsawa da sherawa, ya canza mishi beshit and blanket, da rigunan pillows. Kana ya goge ko ina fes Sannan ya shiga bathroom ya wonke ya goge mishi. Su kuwa suna biye da ita har falonta. Ganin ta wuce bedroom ɗinta ne yasa Hibba da Juwairiyya suka tsaya. Ita kuma Ummi tabi bayanta. Ganin tana shiga ta hau gado ta kwanta ne a take sai bacci yasa Ummi ta juyo ta fito. Can babban falon suka koma suka zauna. "Ikon Allah sai kallo wannan abu da ban tsoro da ban mamaki". Ummi ta faɗa cikin al'hini. Jiki a mace Aunty Juwairiyya tace. "Sosai kam wannan al'amari ya firgitani". Hibba dai sai zuru-zuru tayi da ido. Nan sukayi ta mamakin wannan abin. Jamil na fito shida Jalal suka tafi. Shi kuwa Ya Jafar bayan matarsa yabi suka tafi. Hibba kuwa da Ummi nan suka zauna. Ummi ce ta kalli Hibba tare da cewa. "Sai anjima zan kira Umaymah na sanar mata abinda ya faru". Kai kawai Hibba ta kaɗan mata. Ita kuwa Shatu baccin tayi mai nauyi sai kiran sallan azahar ne ya tasheta. Su Sheykh Jabeer kuwa suna can sunata keta hazo. Tafiya awa huɗu ne zai kawosu ƙasar mun. A hankali ta buɗe idonta, miƙa tayi tare da yin salati. Kana ta tashi zaune. Bathroom ta shiga, wonka tayi da ruwan ɗumi. Kana tayi al'wa tana fitowa. Ta zura Hijabi tayi salla. Bayan ta idarne, ta zauna gaban dreesing mirror. Simple makeup tayiwa fuskarta. Sannan ta sauya shiga, wani tattausan lace mai ɗan karen kyau da tsada tasaka duguwar rigace tayi cib-cib da jikinta. Kasan cewarta kalar pink guava da ɗigo-ɗigin mint green ne yasa tayi masifar dacewa da kalar jikinta. Gyara gashin kanta tayi ta tubƙeshi tare da kitsen jelar. Ta saketa bisa kafaɗunta. Ɗaurin asseta tayi ya zauna ɗas a kanta, tattausan gyale minti green color ta yafa a kafaɗunta. Kana ta fesa turarukan ta masu daddaɗan ƙamshi. Sosai jan lallen gargajiya dake kan ƴan fararen yatsun hannunta yayi masifar kyau. Ga kuma zanen da akayi a saman hannun hakama ƙafafun ta, suma sun sha zanen jan lalle tayi kyau sosai, Ta fito ras da ita. Baki ɗauke da sallama ta foto falon. Cikin murmushi Ummi ta amsa sallamar tana mai kallonta, Hakama Hibba da Ummi ta kokkontar mata da hankali taji tsoron ya ragu. Gefen Ummi ta zauna, tana kallon Hibba na ɗaukarta hoto tana cewa. "My Happiness Aunty kinyi kyau". Murmushi tayi tare da cewa. "Na kaiki ne?". Da sauri Hibba tace. "Kin fini ma". Murmushi ta kumayi tare da cewa. "Ngd matuƙa". Sai kuma ta kalli Ummi tare da cewa. "Ummi me zamuyi abincin dare". Cikin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185