Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 43

Chapter 43

Garkuwa Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

da cewa. "Yauwa Sitti, bana son ana sawa Jazrah tana samin abinci, bana so, sai a turrota tazo taita kare min kallo". Fuskarta ta haɗe kana tace. "To yayi kyau, kawai in baka sonta, ka fito fili ka faɗa mana". Kauda mgnar yayi tare da cewa. Ki shirya in sha Allah zuwa ran jumma'a ina son in kasance cikin ƙasata ta haihuwa a jiharmu a kuma masarautarmu". Haroon da yanzu ya shigone ya ɗan kalli ɗan uwan nashi, cikin mmki yace. "Sheykh kawai dan ana mgnar baka matar aure shine kake shirin guduwa zaka bar ƙasar ba?". Bai kalli Haroon ba kuma baice, komai ba, sai rufe system ɗinshi yayi kana ya miƙe a hankali, gaban drower'n gadon ya nufa, buɗewa yayi, wasu E Passport guda biyu ya ɗauko, Kana ya dawo gaban Haroon. Hannun shi ya kamo ya danƙa mishi su, kana yace. "Gasu, ina son zamu bar ƙasar nan ranar al'hamis." Da sauri Sitti tace. "Kaida waye zaku tafi". Ba tare daya kalletaba yace. "Da ke". Kai ta kuma juyawa tace. "A a kam ka koma kai ɗaya, ni ban gaji da ganin ahlinaba". aKanshi ya kaɗa tare da cewa. "Zafa ki koma, don bazan barki a kasar nanba, kiyi ta haɗa min tarko, dole tare zamu tafi, inada zama mai mahimmanci, dole inje inji da matsalar al'ummar da aka naɗani GARKUWANSU, tunda ke kika sa na amince da wannan naɗin, ina zamana lfya, wani mulki ko sarauta basa jadawalin rayuwata, keda waɗancan tsofoffin sarakunan kuka likamin wai GARKUWAN FULANI, To sun samu matsala kuma dole inje in bincika". Shiru kawai Sitti tayi ganin karfin hali ziraran miraran. Zuwa yanzu ta dena mmkin, cewa akan abu biyu Sheykh ke iya doguwar mgna, akan Alqur'ani, wanda shine zaka samu zai iya wuni a zaune yana tabsiri ba gajiya ba yunwa bare ƙishi ko bacci. Sai kuma akan wannan sarautar GARKUWAN FULANI da aka bashi shekarun biyar baya, wanda harga Allah baison wannan Sarautar ko kaɗan sai dai dole da akayi mishi, da fushin da Abbunsu ya nuna a kan haka. Shiyasa duk sanda zaiyi ƙorafi yakan iya jera mgna biyar zuwa bakwai, wanda sam shi tsarin rayuwarsu ba mai doguwar mgna bace. Kai takaɗa jin yana cewa. "Ku ɗan bani wuri". Basuyi mgna ba suka fita, a tare, domin sun san Sheykh Jabeer mutunne mai tarin tsananin al'kuyya da killace jikinsa, shi kanshi yana kunyar kanshi a rayuwarshi ta duniya shi bai taɓa yin tsirara a kan kanshi wai yaga surar jikinshi ba, Allah yasani yana masifar jin kunyan kanshi. Haka yasa koda wonka zaiyi, baya yin tsirara, yanada wasu tausasan gajerun towel wanda duk rintsi dasu yakeyin wonka a jikinshi. Suna fita falo, Haroon ya tsaya yana kallon Jazrah, dake konce bisa kujera ta kife kanta a cinyar Jannart tana kuka mai sanyin sauti. Kai Sitti ta juya ta nufi ɗakinta, Allah ya sani Jazrah na son Sheykh, shi kuwa bai nuna ya tsaneta ba, amman dai ya nuna zahirin bazaiyi aureba. Haroon da Jannart ne suka zauna suna bata baki. Saida ta nitsune suka fita tare. Shi kuwa Sheykh suna fita, ya maida ƙofar ɗakin ya rufe. Kana ya dawo bakin gado. A hankali ya zare tattausan al'kyabbar jikinshi, fararen kayan dake jikinsa suka baiyana. A hankali ya zare rigar ya ajiyeta gefe. Zariyan wonɗon ya kunce, tare da zama, ya saɓule tare da matsawa gefe. Ya rage dagashi sai fararen boxes da vest. Juyawa yayi yana taku mai cike da nitsuwa, ya shiga bathroom ɗin. Yana shiga ya maida ƙofar ya rufe, kana ya rage hasken ciki. Sannan ya cire ƙananan suturun dake jikinshi tare da ɗaura towel ɗin, a ƙuginshi zuwa kan cinyoyinshi masu yelwar gargasa mai taushi da tsulɓi da sheƙi tana,konce lib-lib a farar fatar jikinshi. A haka ya fara, wonkan, bayan yayi Brosh a hankali yake bin jikinshi da sabulun mai ɗan karen ƙamshi, yanayi ya cuccuɗa jikinshin. a hankali ya iso kan ƙugunshin, cikin sabo da iya ɗabi'ar tasa, ya cusa hannunshi ta cikin ɗaurin towel ɗin, ya rinƙa cuccuɗa jikinshin da murza mishi daddaɗan sabulun ya murje ko wani lungu da saƙo na sasan jikinshi ba tare da idanunshi ma, sunga tsiraicinsaba. A ƙalla yayi sawon daƙiƙu ashirin a bathroom ɗin kafin, ya fito, yana ɗaure da wani babban towel mai ɗan karen kyau da taushi bayan ya matse wancan ya shanya. Yana saƙo ƙafarshi cikin bedroom ɗin ya...! Solo-salo-salon GARKUWA na dabanne! By *GARKUWAR FULANI* 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 🐄🕊️🌈🦚🐍🤴🏻💘 *GARKUWA* PAGE 13 NA *AYSHA ALIYU GARKUWA* 📝🍇🐄🌈🦚🤴🏻💘 FREE PAGE Littafin GARKUWA na kuɗine, Special Group 1k Normal 300, in kina buƙatar karanta lbrin GARKUWA turo katin mtn na ɗari uku kacal ta wannan layin 09097853276. Gareku mutanen Special Group turo dubu ɗaya ta asusuna 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, sai ki turo shaidar biyanki ta wannan number 09097853276. *Dan Allah da Manzonsa da darajar iyayenki, in kin san zaki sayi littafinane dan ki fitar dashi, na roƙeki da Allah da Manzonsa da darajar iyayenki kada ki saya bana son kuɗinki, ki riƙe kudinki ki barni in riƙe littafina. Dan Allah nace badon niba.* Yaji anata bubbuga mishi ƙofar ɗakin, bai kulaba, yazo a zauna bisa kujerar dreesing mirror, a hankali yake tsane ruwan jikinshi, bayan ya gama ɗan tsane ruwanne ya busar da tattausan sumar kanshi, ta hanyar na'urar busar da gashi. Mai ya ɗan shafa, kana ya gyara gashin da kyau, sannan ya miƙe yaje gaban. Drower'n, a nitse ya buɗe, wasu datsatstsun kaya riga da wondo na yadin Lamud, yadin Sky blue ne mai masifar kyau. Sai kuma ya zaro wata farar al'kyabbar fara ƙal. Da farin hirami. Rufe wannan gefen yayi, kana ya buɗe ɗaya gefen. Ƙananan kayan ne a ciki kamarsu Jallabiya da boxes vest dasu zagayen baƙin abin da yake ɗaurawa kam hiraminshi. Suma duk mafi akasari su fararene. A bakin gadon ya ajiyesu. Kana ya fara kimtsawa. Bayan ya gama shirinsa ya fito ras cikin kalar sky blue and white sai Black half cover da kuma baƙin zagayen saman hiramin. Ya fito ras tamkar dai yadda zuriyar mahaifiyarshi da suke tsatson limamen Harami suke fita. Ko yaya ka ganshi dole kace shi balarabene, sabida komai nashi irin nasune. Kyau, fari, gashi, ilimin addini, nitsuwa, imani, da kuma irin shigarsu, da shima ya rainu da hakan tunda a cikinsu ya girma. Wani turaren Oud Kareem ya feshe jikinshi dashi. Lumshe ido yayi sabida shida kanshi ya shaida ƙamshin wannan turaren nashi iyakane. A hankali ya nufi ƙofar fita yana tafe yana tasbihi. "Astagafirullaha wa'atubu ilaik. Astagafirullaha zunuba jami'an. Subahanallahi Wal'hamdulillah wa la'ilahaillahu Allahu Akbar." Da wuya ka iya jin abinda yake faɗin, sai dai ina ka lura da motsawan jajayen laɓɓansa, masu kama da jajayen kunnen fire masu taushi zaka fahimci tasbihi yakeyi. Ba kowa a wurin sabida haka ya nufi falo a nitse, A falon ya samu Sitti bisa dukkan alamu, shirin tafiya harami tayi. Tana ganinshi ta miƙe tare da cewa. "Muje ko". Kai ya gyaɗa mata, kana ya ɗan kalleta bayan ya ɗan tsagaita tasbihin bakinshi yace. "Zan shiga wurin Sheykh Abdulkareem". Cikin kula tace. "Muje sai mun dawo mana". Kanshi ya jujjuya mata kana yace. "Zan sanar dashi batun komawarmu". Gyara matafinta tayi tare da cewa. "Na sani ai, muje sai

Table of Contents

Chapters

185 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});