Chapter 55
Chapter 55
aurenta, to ya aikata hakan, (ma'ana ya kalleta) Jabir yace sai na nemi wata mata, daga cikin ƙabilar Banu Salma na kasance ina bibiyanta har sai da naga abin da zai birgeni a aurenta. Ɗan zagaitawa yayi kana yayi gyaran murya tare da cigaba da cewa. "To matasanmu na yanzu suna, fakewa da waɗannan hujjojin, suna fakewa da guzuma su harbi karsana, suna fakewa da hadisai suyi haramtaccen kallo, wata sun fake da rama suci ɗanyen gari. Hattara gareku iyayen yara maza da mata, Gargaɗi gareku matasa, bari in tuna sar daku wuraren daya halasta ka kalla a jikin matar da kake son ka aura. Dangane da inda ya kamata ka kalla, a jikin macen da zaka aura. Malamai sun kasu kan wannan hukuncin, saboda ba su, sami hadisin da ya yi bayani keɓantaccen wuri wanda aka keɓe ko aka ce nanne kawai za'a kalla ba, wannan shi ne musabbabin da suka karkasu kamar haka: 1 Mafiya yawan malamai sun tafi, cewa in mutun yana neman auren mace, yana iya duban fuskarta da tafukan hannunta. A Duba Fiƙhu wadi Juzu'i na 2. Shafi na 20 sannan kuma a cikin Fiƙhu Sunnah Juzu'i na 2 shafi na 24 wasu malamai sun ƙara yin bayani da cewa idan mutum ya dubi fuska mace, zai gane kyawunta, in kuma yadubi Fuskarta zai iya fahimtar cewa, mai ni'imtaccen jiki ne wato mai tattausan fata jiki, ko kuma mata marar ni'iman jiki. Sheikh imamul Al-Auza'i yana cewa. "Mai neman aure yana iya kallon wuraren nama dake jikin mace da zai aura. Duba cikin Fiƙhu Sunnah Juzu'i na 2 shafi na 24. Sheikh imamul Dauda kuwa yana cewa: Mai neman aure yana iya kallon dukkan jikin matar da zai aura, shima an samu daga Fiƙhu Sunnah Juzu'i na 2 shafi na 24. Ɗan tsagaitawa yayi tare da ɗago kekyawan tsintsiyar hannunshi ya kalli agogon Daimond dake ɗaure samfarin Gucci, Ganin lokacin salla ya ƙara tone yasashi yin gyaran murya tare da ci gaba da mgna gaggauce, yace. " A wata ruwayar kuma da aka samo daga Abudurrazaƙ Umar Sa'idu ɗan Mansur yace, (Amirul mu'minin) ya nemi auren ƴar Sayyidina Aliyu (R.A) wanda ake kira da Ummul-Kulsum, sai, Aliyu ya ambata masa ƙanƙantarta, sai yace. Zan turo ita idan ka ganta tayi maka matarka kenan, sai ya aiketa wuri shi. Lokacin da taje sai ya yaye suturar da ya rufe ƙwaurinta. Sai tace. (Ba don kai Amirul mu'minin bane da na tsole ko buge idonka, (wato da na mareka) idan muku dubi, wannan in har maganar ya inƙanta to ana iya yin hakan. Anan kenan in har ka kalleta batayi maka ba, to ka kama bakinka kayi shiru. Kada ka faɗi wata magana wanda zata iya cutar da ita. In kana ganin kai bata baka sha'awa ba, to tana iya bawa wani sha'awa ya aureta, domin ko wanne icce da ma tsincinsa, kuma abincin wani guban wani. Allah yasa mu dace, lokacin salla yayi, bari muyi salla sai in Allah ya kaimu sati mai zuwa sai muyi bayani kan halaccin mace ta kalli mijin da zata aura. Daga nan yayi addu'an kana, ya juya ya fuskanci gabas, tare da tada iƙama bayan yayi addu'an. Bayan an idar da sallane, suka fito, a jere. Ta ƙofarsun dai suka shiga, inda duk ahlin masarautar suke bin nan bayi da hadimai da sauran fadawa kusa, duk ta babbar ƙofar suke bi. Kusan a jere a jere suke tafi. Kasan cewar zasuyi tafiyar zuwa Rugar Bani ne yasa Mai martaba Lamiɗo ke sauri. Hakama Sheykh Jabeer, wanda Jalal, Jamil, Jafar, Haroon, Imran, Hashim ke tare dashi, A hankali ya tsaya jin muryar bappanshi ƙanin Abbanshi Baba Nasiru kenan na ce mishi. "Kai! Jabeer tsaya". Tsayawa yayi cak ba tare daya juyo ba, Suma sauran duk tsayuwa sukayi, Kusan a tare Baba Nasiru da Baba Bashiru. Suka isosu. Cikin haɗe fuska Baba Nasiri yace. "Jabeer, in dai aure kake so ai gwara ka fito fili ka gaya mana, mu bazai gagara ba mu aurar maka koda yar baiwace, tunda shi ubanka zuciyarshi ta mace, baya iya tsinanawa kansa komai." Da sauri ya rumtse idonshi, Jalal kuwa wani irin kallo ya watsa bappanun nasu, Shi kuwa Jabeer shiru yayi bai tanka musuba, Baba Basiru ne ya ne ya bugi kafaɗarshi tare da cewa. "Kodai kafi ganewa yawon zinace- zinacen daka saba ɗin ne? Kafin burin a barka ba mata, kana zaune ka tsufe a gida ka fake da rigar malumta kana iskanci a cikin tsarkakekkiyar masarauta ko". Ido ya zuba mishi babu ko kebtawa, ganin haka Baba Basirun ya ɗauke hannunshi dake kan kafaɗarshi. Dai-dai lokacin kuma Barrister Kamal da Dr Aliyu suka iso wurin. Suna isa Ya Jafar yayi saurin kamo hannun Ƙanin shi Sheykh Jabeer, ya fara ja da sauri alamun su tafi su bar wurin gaba ɗaya, jikinshi rawa yakeyi. Ganin hakane Haroon ya kalleshi cikin larabci yacewa Jabeer. "Ɗan uwana mu tafi". Barrister Kamal ne ya kalli Jabeer cikin sanyi yace. "Jabeer jeka, ku tafi kada ka biye musu, tunda sun girma basu san sun girma ba." Jin hakane yasa Jabeer ya juya ya fara tafiya. Jalal kuwa wani harara ya watsa musu kana ya juya yabi bayan yayunshi. Jafar kuwa Jan hannun Jabeer yakeyi a kiɗime gaba ɗaya jikinshi karkarwa yakeyi tamkar mazari. Ganin haka yasa Jabeer ya jashi ya kaishi sashinsu, ya damƙa hannunshi wa Juwairiyya kana yace mata ta kula dashi, yanzu zai fita shida Lamiɗo. Jiki a mace Juwairiyya ta mishi fatan a dawo 'lfy. Ƙarfe biyu da rabi dai-dai suna cikin motoci, wanda a ƙalla sun kai su goma. Motar forko Waziri ne wanda yake ɗane ga Yayar Lamiɗo. Sai Galadima, da Wambai, Ɗaya motar kuma Ɗan iyane da Sallama, da sarkin Dawaki, da sarkin fada, Sai motar da Lamiɗo ke ciki, shida Garkuwa wato Jabeer sai Haroon sai kuma Hashim da Laminu, ƙanin Hashim wanda duk yaran Gimbiya Saudatu ne matar babban yayansu Habibullah wato Abbansu Jabeer, wanda da shine Galadima. Ɗaya rasune aka bawa Ya Jafar sarautar wanda kwananshi goma da sarautar, komai na rayuwarsu ya sauya. Sai motar dake binsu wanda Jalal, Jamil, Imran Sulaiman ɗan Barrister Kamal, suke ciki. Sai sauran motocin fadawa kamaru, Ɗan kazagi, mai yiwa sarki fadanci da kuna dogari mai riƙewa sarki laima, da sarki mota da dai sauransu. A jere a jere motocin ke tafiya. Gudu sukeyi mai ɗan yawa sabida ganin yamma ta ƙarato, gashi basu je bama bare su fara shirin dawowa. Gudu sukeyi, kana fadawansu, rirtiƙe da bulalin dogaye. Kai tsaye Rugar Bani suka nufa. Koda suka iso cikin garin Shikan, sunga alamun garin babu lfy, har yanzu dan sai matasan ƙabilar ɓachama da hausawa suketa yawo a garin ko wanne na bawa yankinsu kariya. Suna isa cikin Rugar Bani. Gaba ɗaya mutanen Rugar duk inda suka gilma sai a bisu da ido, Yara maza da mata sunata guduwa suna shiga cikin gidajensu. Kai tsaye tsakiyar garin suka nufa wanda nanne fadar Arɗo Bani taken kuma lokacin duk manya da yara maza tsoffi da dattawan garin duk suna harabar wurin sabida yau jumma'a duk suna dawowa kiwo da wuri. Kuma duk a tsakiyar garin suke taruwa sabida bawa garinsu kariya, domin har yanzu suna cike da taraddadin abinda akayi musu. Kuma ya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185