Chapter 4
Chapter 4
tansu baki ɗaya. Arɗo Babayo ne yayi ɗan gyaran murya tare da kauda kanshi daga kallonta sabida kwarjininta yafi ƙarfin ƙwayar idanunsu cikin sanyi murya yace. "Allahu wahidun ƙahhar, Mutunce ba al'jana bace, Allah shi ya barwa kansa sanin dalilin kasan ce warta a cikin tsuffofin tsuntsaye, amman kam tabbas al'amarine mai tarin girma da sarƙaƙiya, Tine taimaka mata, da zuciya ɗaya ina ji a jikina ba mai cutarwa bace. Kuma akwai tabbaci da kekyawan zaton musulmace". Ido ta zubawa mijin nata da yake bata ƙarfin guiwa. Appa ne ya kalleta tare da gyaɗa mata kai, alamun eh ta taimaketa, Ita kuwa Parvina cikin tausayawa da zubda hawaye tace. "Appa kalli hannunta ya kumbura gashi jikinta zafi Appa a taimaka mata". Hannu ya miƙo ya kama Parvina cikin tausayawa yace. "Zo nan Parvina za'a taimaka mata kinga bata da lfy tashi a jikinta, kinga ki dena danne mata hannun da cikinta". kai ta gyaɗa kana ta kalli matar cikin sanyi tace. "Sannu!". Bata basu amsa bata kulasu bata kuma hafimtar komai daga garesu, haka yasa su Arɗo Babayo juyawa suka fita, ita kuwa Inna matsowa gareta tayi cikin tarin ƙarfin guiwa irin na fulani. Fulaninma irinsu na daji ba irin wasunku na birniba. cikin sanyi tace. "Taso muje daga ciki". ido ta zubawa Inna cikin yanayin wahalar da takeji, hannu Inna tasa ta kamo hannunta mai lafiyar, ta miƙar da ita tsaye. Allah da ikonshi, sai gata a tsaye cas. Haka yasa Inna ta jata suka koma cikin gida, cikin ɗakinta ta kaita, a bakin katifar da suka kwana ta ajiyeta, da sauri ta koma woje wuta ta hura ta ɗaura ruwan zafi. Kana ta dawo ciki. Cikin mamaki take kallonta ganin taja ta jingina da jikin gini kana, ta rumtse idanunta ga hawaye nata kwaranya daga idanunta. Gefenta ta zauna ta zuba mata ido. Jin an zauna gefen tanne yasa ta buɗe kekyawan idanunta, cikin kula Inna tace. "Sannu baiwar Allah, kamar naƙuda kikeji ko?". Kai ta gyaɗa mata alamar eh naƙudar takeji, murmushi inna tayi tare da cewa. "Alhamdulillah naji sanyi na ƙara gamsuwa ke mutunce, kuma kina gane me nake faɗa a yanzu, to amman kiyi magana mana". Kanta ta jujjuya mata alamun. "Bazan iyaba". Jin muryarsu Arɗo Babayo ne yasa inna tayi maza ta fito, Ganin Arɗo Babayo da Appa da kuma Malam Liman da sarkin bakansu wanda yake rugar makotansu ne yasata saurin fitowa tare da cewa. "Sannun ku da zuwa Malam Liman, Baka barka da zuwa". Taburma ta shimfaɗa musu, jin muryar Malam Liman ne na cewa. "A a bar taburmarnan ina baƙuwar tamu?". "Tana cikin ɗaki, da alamun tana fama da yanayin naƙuda ne". Inna ta faɗa cikin alhini. Sarkin bakanne yayi ɗan gyaran murya kana yace. "Ina son ganinta". Arɗo Babayo ne yace. "To bisimilla, shigo daga ciki". Ɗakin suka nufa Inna na gaba Arɗo Babayo na biye da ita a baya, kana Appa da Malam Liman da Sarkin Baka suka rufa musu baya. Suna shiga suka sameta zaune ta haɗe jikinta wuri ɗaya, jin motsin shigowar mutanene yasa ta ɗago kanta, da sauri ta kauda idanunta. Shi kuwa SARKIN Bakan, kanshi ya rinƙa jinjina wa cikin al'hini yake cewa. "Mutun ce ba al'janba, baiwar Allah an tozarta rayuwarki." Sai kuma ya kalli Arɗo Babayo cikin sauri yace. "Maza a bani madarar shanu mai ɗumi wanda aka tatsa yanzu". To Arɗo Babayo yace tare da juyawa ya fita, a harabar gida yayi arba da Gainako da yake shigowa da kwaryar nono, da sauri ya iso, kana yasa ƙaramar kwarya ya kamfati madarar shanun daketa tururi sannan ya juya ya koma cikin ɗakin. Yana zuwa ya miƙawa sarkin Bakan, yana amsar ƙoryar, ya ajiyeta a gabanshi jakar fatar ruƙimi da yakesa magungunanshi a cikine ya sauƙe daga kafaɗarshi, kana a hankali ya fara harhaɗa magunguna a cikin madarar, saida yasa komai sannan ya kalli Inna yace. "A bani zuma da zam-zam". Da sauri tace. "To". Kana ta miƙo ta ɗauko mishi, koda ta kawo da sauri yasa zumar da zam-zam ɗin ya gaureyasu,'. Kana ya bawa Malam Liman da Arɗo Babayo sukayi mata tofin ayatul shifa, a ciki, kana ya amshi kwaryar. Inna ya miƙawa kwaryar yace. "Gashi bata tasha". Amsa tayi kana ta matso kusa da matar a hankali tasa mata bakin kwaryar a bakinta. Tare da cewa. "Bismillah ki Sha". A hankali ta buɗe bakinta, ta fara shan madarar shanun nan da magungunan, masu haɗe da zam-zam da zuma da kuma rahamar ayatul shifa. Saida ta sha mai yawa sannan ta kauda kanta. Ae fa a take saiga naƙuda ta tashi gadan-gadan. Ganin haka yasa su Arɗo kab suka fito woje ya rage daga ita sai Inna. Ganin haka yasa Malam Liman tura Ori da yanzu ya shigo yaje ya kira matarsa ta taimakawa inna su amshi haihuwar. Ba jimawa kuwa Iya laure tazo, kai tsaye cikin ɗakin ta wuce. Cikin ikon Allah a take a sauƙaƙe Allah ya sauƙeta lfya, ta haifi yarta mace ƴar ƙanƙanuwa. Bayan sun yanke cibiya sun gyara, komai na wurin. Kana Inna ta taimaka mata tayi wonka, ita kuwa iya laure wonka tayiwa jaririyar ta haɗeta cikin zanin Inna ta bawa Parvina daketa tsalle. Koda suka fito daga wonka, konciya tayi a kan katifar, kana iya laure ta kontar mata da ƴar a gabanta. Ajiyan zuciya ta sauƙe mai ƙarfi kana a hankali ta lumshe idonta, tana son ta tuno wani abu na rayuwarta ta baya amman ina ta kasa tunowa, Abu ɗaya takeji bata manceba sunan Allah wanda tunda ta dawo mutun taketa maimaita kiranshi a zuciyarta dan taji bakinta bazata iya magana ba, amman a ranta tanaji tana bitar karatun al'ƙur'ani mai girma da tarin addu'o'in kamar yadda takeyi tun tana a tsunstsuwar ma. Ganin tayi shiru ne kamar maiyin bacci yasa inna da iya laure suka fito woje. Sashin Arɗo Babayo suka nufa, suna shiga sukayiwa juna barkar haihuwarta lfy. Shiru sukayi baki ɗayansu bayan duk sun zauna kamar yadda Sarkin Baka ya umarcesu, gyaran murya yayi kana a hankali ya fara magana. "To da forko dai sai dai muce. Alhamdulillah, mun godewa da yasa sanadinmu wata baiwar Allah zata samu waraka daga mugun cuta na magauta maƙiya azzalumai marasa tsoron Allah". Kai suka jinjina alamun gamsuwa, shi kuwa tonkoshe ƙafa yayi kana yaci gaba da cewa. "Kamar yadda kuka gani a yanzu mutunce bani adam ce ba tsunstsuwa bace kamar yadda kuka gani da zata a baya, aikin sihirine kawai ya maidata haka. Amman Alhamdulillah tunda gashi yanzu Allah yayi ikonshi ya karya abun da akayi mata ya kuma sauketa lfy dama shi asiri tasirinshi kaɗanne ga wanda yayi imani da Allah kuma dole gsky zatayi halinta watan-watarana". Arɗo Babayo ne yace. "Allah mai iko, mutun a maidashi tsuntsuwar Boleru kai abinnan da al'ajabi". Kai ya gyaɗa mishi tare da cewa. "Ɗan Adam kenan mai wuyar gane hali babu mai sanin halin mutum sai Allah, domin shi ɗan adam dare". Sai ya kuma kalli Inna tare da cewa. "Yanzu tayi magana ne?". Da sauri Inna tace. "A a batayi mgna ba sai dai in anyi magana tanaji kuma tana ganewa". Kai ya rausayar tare da cewa. "Zatayi magana in sha Allah, yanzu aci gaba da kula da ita yadda ya dace
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185