Chapter 90
Chapter 90
kunne shi ya kira sunanta cikin rauni. Murya a kausashe tace. "Jabeer". Da mamaki ya amsa dan sama da shekaru goma sha biyu kenan da Jazlaan take kiranshi, cikin sanyi yace. "Na'am Umaymah". Cikin bada umarni tace. "Jabeer ka tashi maza yanzu ka shiga fagen gasar nan ayishi da kai, bana son musu umarnine ba shawara ba". Cikin sauri ya zaro siraran kyawawan idanunshi, Dai-dai lokacin kuma Lamiɗo ya miƙe tsaye cikin tashin hankali da kiɗima da firgici da baƙin cikin dakatar da gasar Shaɗi da akayi a masarautarsu ya sani da anayi da Jabeer bazai ƙalubanceshi ba, cikin sanyi yace. "Zanje za'ayi dani, zan tabbatar da darajar masarautatarmu bata rusheba." Da ido yabi Dottijon kakan nashi wanda a ƙalla ya kai shekaru 91 a duniya. Cikin kauda kai yace. "To Umaymah yadda kikace haka za'ayi amman bari in kira Sheykh Abdulkareem in sanar mishi in ya amince dai zanyi". Da sauri tace. "A a ban yafe ka kirashi ba, wato don kasan in ka kirashi zai kira Sitti da Mai alfarma Jalaluddin da Sarki Nuruddeen ya dakatar da duk abinda za'ayin, tunda na san cemishi zakayi ba addini bane, al'adace, to ban yardaba maza tashi". Ganin Ya Hashim na miƙa masa wayarshi ne yasashi cewa Umaymah. To cikin sanyi. Yana amsa wayar da Ya Hashim ya miƙa mishi yaki Muryar, mahaifinshi cikin sanyi da kuma alamun yana kukane yace. "Jabeer ashe har kayi girman da Lamiɗo zai umarceka da yin abu kaƙi yi mishi mubaya'a, Ashe har na haifi ɗan da zai ja da mahaifina." Cikin sanyi da rauni yake jujjuya kai murya na rawa yake cewa. "A'a Abba, kayi haƙuri kada kayi kuka a kaina." Bai kulashiba yaci gaba da cewa. "Jabeer Ashe zuciyarka har tayi tauri da kangarewar da kanaji kana gani za'a daki mahaifina a gaban idonka, bazaka zame mishi GARKUWA ba, Jabeer wannan shine tukuicin tsantsar son da mahaifina keyi muka, wanda har ya jazamin ƙiyayya a wurin yan uwana sunaga ya fifitaku kan sauran jikokinsa Especially ma kai Jabeer komu daya haifa baya nuna mana son da yake nuna maka, shine zaka bari a dakeshi mutun mai shekaru 91 da ɗaya a duniya kai me shekaru 30 bazaka iya zame mishi GARKUWA ba?". Cikin rauni da ƙunar zuciya, ya miƙe tsaye hannunshi yasa ya kamo na Lamiɗo cikin tarin ƙuna da zafin rai da takaici yace. "Na Amince, zanyi gasar na yarda, ka koma ka zauna". Wani irin farin ciki ne ya ziyarci, zuƙatansu gaba ɗaya, sai dai kowa da irin manufar farin cikinsa. Jin haka yasa fadawan janye labulen da sukayi musu. Shi kuwa Lamiɗo hannunshi yasa ya kamo hannun Jabeer, cikin tsantsar farin ciki da al'fahari da ƙasaita ya fara taku, suna ratsawa cikin taron. Kana fadawansu na biye dasu a baya. Ɗanzagi yana. "Takawarka lfy Sarki mai daraja Lamiɗo ɗan Lamiɗo jikan Joɗa. Gyara kimtsi". A haka har suka isa cikin asalin dandamalin da aka jiƙashi jilak da ruwa, sabida hana ƙura wanzuwa. Gaba ɗaya taron mutanen wurin maza da mata manya da yara, Jabeer suka zubawa ido, sabida duk wanda ya ganshi yaga sahihin Balarabe, mai kamala da nitsuwa, uwa uba kima da haiba, ƙwarjini shi ya cika dukkan idanun magautanshi dake wannan yanki, yayinda masoyanshi ke taraddadin abinda zai faru. A tsakiyar filin suka tsaya, hannunsu dake raƙe dana juna Lamiɗo ya ɗaga tare da fuskantarta gabas, kana ya juya yamma, ya kuma juyawa kudu da Arewa, sannan suka dawo tsakiyar filin, Cikin ƙasaita, yace. "Ga GARKUWAN FULANI, kuma daga Wannan nasarar da zaiyi a gasar nan, Zai tabbatar GARKUWAR Masarautar Joɗa, GARKUWA kuma mai ikon zama inda yaso a cikin fada". Dariya Bukar yayi kana ya ɗaga hannun Ba'ana da yaketa wani abu da ƙirjinshi kamar damisa, Cikin isa da yaƙini da al'fahari yace. "Mu kuma ga namu Garkuwan, da muke da tabbacin bai taɓa gasa ya faɗiba". Sake hannunshi Lamiɗo yayi kana ya juya ya koma ya zauna, cikin rumfar da akayi musu masauƙin. Al'ƙalin gasar ne yazo tsakiyar taro, kamar ko yaushe, hannun Ba'ana ya kamo, ya ɗaga sama, hakan yasa, gaba ɗaya makiɗa da mabusa suka ƙara sautin kiɗe-kiɗen su, wanda Jabeer ke jinsa har tsakiyar kansa, Allah ya sani, baya son hayani koda dai-dai da ƙwayar zarra ne, ga wani masifeffen fargaba da tsinkewar da zuciyarshi keyi, yanaji tamkar yasa hannunshi ya toshe kunnuwanshi. Ɗan wani gajeren tsaki yaja sabida Allah ma ya sani baya son kallo, to kuma yanajin yadda idanun mutane ke yawo a jikinshi. Shi kuwa al'ƙalin gasar, yana sake hannun Ba'ana yazo ya kamo hannun Jabeer, Da sauri ya juyo ya kalleshi sabida kamo hannunshi da yayi sai yaji tamkar hannun jariri ya kamo dam laushi da taushin fatar, hannun sanyi ƙalau, girgiza kanshi yayi cikin tausayawa, sabisa, ya za'ayi ace mai wannan taushin hannun fatarsa ta iya jurar azababbun bulali masu masifar zafi. Ɗaga hannun Jabeer yayi sama. Yana mai nunawa taron mutanen shi a matsayin dashi za'a gwabza. Shi kuwa Sheykh Jabeer, duk abinda akeyi idonshi na cikin ɗan siririn farin galashi mai garai-garai dake liƙe a fuskarshi, Hannunshi kuma riƙe da carɓinshi, kana bakinshi ambaton sunan Allah. Cikin tarin mamaki ya kalli, Al'ƙalin gasar tare dasa hannunshi ya riƙe bakin al'kyabbar jikinshi cikin haɗe fuska yace. "Me hakan!?". Cikin saurin rusunar da kai Al'ƙalin gasar yace. "Za'a cire kayan jikin naka ne!". Cikin tarin mamaki ya zazzaro ido waje, a baiyane yace. "Akan me kenan, suturar da Allah yayi min a matsayin mulmi, in killace kaina, shine zaku yayemin a cikin dubban dubatan mutane?". Cikin dakiya Al'ƙalin ya ɗan kalleshi domin kwarjinin Jabeer ya cika masa fuska cikin sanyi yace. "Allah rene, ƙa'idar gasar ce, ba'ayi da kaya a jikin mutun sai ɗan kamfai, kawai ake bari a jikin mutun". Cikin kufula da harzuƙa yace. "To bada niba, Ni nan Muhammad Jabeer wallahi banyi lalacewar da zan tsaya tsirara a gaban jama'a ba". Yana faɗin haka ya juya a fusashe, zai fita cikin taron. Ganin hakane yasa Galadima, yayi saurin tasowa, kana Ɗan buram na biye dashi a baya, tareshi sukayi tare da kamo hannunshi. Da sauri suka juyo suna. Kallon gungun wasu matasa wanda suka kece da dariyar ƙeta cikin hausarsu ta ƙabilu suke cewa. "To ku ɗan naku ko yadda ake gudanar da gasar ma bai sani bane? Ya zaiyi zaton da wannan shigar tasa za'a dakeshi, to ai ko bulali dubu za'ayi mishi ba jinsu zaiba, Kai Ɗan kazagi, ka gaya mishi nan ba cikin masallaci bane. Nan wurin shaɗi ne". Jiyo hakane ya sa ran dukkan musulman wurin ɓaci. Sabida sun fahimci kafuraine masuyin wannan zancen. Galadima kuwa da Ɗan buram sun ɗauka abin wasane, a zatonsu zasu shawo kan Jabeer a sauƙaƙe, amman ina ya tiƙe yace babu wani zinɗiƙin ƙaton da zai sashi ya yaye suturar dake jikinshi. Dariyar da su Arɗo da sauran mutane keyine ya hautsuna lissafin Lamiɗo. Cikin harzuƙa ya taso, har kamar zaiyi tuntuɓe ya nufi inda su. Waziri, Wambai, Ɗan buram, Ɗurɓi, Da Galadiman, cikin tashin hankalin alamun akwai wata babbar manufa da Galadima ke son cimmawa cikin lamarin ya riƙe hannun Jabeer tare da cewa. "Haba Jabeer kai wanne irin mutun ne mai kafiya da taurin kan tsiya, yaya muna binka kana zillawa, muna haɗaka
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185