Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 18

Chapter 18

Garkuwa Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

tabbas Ba'ana kekyawane. A duniya kab Shatu ce tasan sirrinshi ciki da woje, sai daifa bata san yana sataba, amman duk wani abu na asiri da yadda za'a karya asirin da kuma yadda yake juyewa duk ta sani. To hakanne yasa sam bata fatan ya zama miji a gareta bare uban ƴaƴanta, sai dai babu yadda ta iya. Domin ya mata babbar rana a rayuwarta ya mata taimakon da yasa aka ɗaukar mishi al'ƙawarin aurenta. Gashi kuma duk wanda yace yana sonta karshenshi mutuwa, kuma yana gaya mata cewa duk wanda yace zai rabashi da ita zai kasheshi Wannan yasa kullum addu'ar shirya take mishi da fatan Allah ya rabata dashi lfy innshi ba mai shiryuwa bane. Tafiya sukeyi cikin nitsuwa a hankali, murmushi yaketayi cikin so da ƙaunarta yace. "Mata ya akayi na ganki da ƙaramar jaka?". Kai ta ɗan gyaɗa mishi tana kallon kekyawar fuskarshi, cikin murmushi yace. "Kece kika ajiyeni a kasar Kautal a Rugar Bani, kina ƙare karatunki zamuyi aurenmu in ɗaukeki mubar ƙasar, kawai dolece tasa na hakura da batun aurenmu kiyi karatu, dan naga kina son karatun kuma nasan zaki karantar mana da yaranmu, kuma ina son ki zama babbar lawyer mai zaman kanta, sai ki zama lawyer na koda watan-wata rana, rana zata ɓacin min". Murmushi tayi tare da cewa. "Kamar yaune zan kare karatun, Ya Ba'ana". Kanshi ya rausayar tare da gyara riƙon igiyar jakar da yayi, kana yace. "Allah ya nuna min wannan lokacin, in sha Allah sadakin aurenki Garken shanu ɗari zan bada". Cikin mmki ta zaro ido tare da cewa. "Kai Ya Ba'ana garke ɗari bama shanu ɗariba, ya bana ina zaka samu wannan shanun kaida garken naku ko shanu hamsin bai cikaba". Murmushi yayi tare da cewa. "Allah zai kawosu kafin lokacin auren namu". A hankali tace. "Allah ya kawosu". Amin Amin yace tare da ɗan juyowa ya kalleta, murmushi yayi mata, kana ya miƙo mata jakar tata cikin so yace. "Mun iso bakin Gari ki shiga. Ni zan koma baya dama rakoki nazo nayi kar shaiɗanun bakin kogi su cutarmin dake". Kai ta ɗan jinjina tare da cewa. "Ya Ba'ana lokacin sallah ya kusa fa ai gwara ka shigo sai kayi salla ka koma". Bakinshi ya ɗan tabe tare da cewa. "No bar sallan nan sai bayan mako biyu ina ƙara dafa jikinane kuma in nayi al'walan duk aikin zai karye". Dafa kanta tayi da sauri tare da cewa. "Wa'iyazubillah Wayyo Allah na Ya Ba'ana ka gane mana wannan abin da kakeyi shirka ne,". Kanshi ya jujjuya tare da cewa. "Shiga cikin gari zanzo musha hira da daren". To kawai tace mishi ta juya ta nufi cikin garin. Tana shiga ta kama hanyar gidansu, tana gab da shiga gidane ta haɗu da ɗan makotansu Iro cikin girmamawa tace. "Ina wuni Ya iro". Fuska cike da fara'a yace, "A a lale marhabin da ƙanwarmu yar al'barka anyi hutukenan?". Kai ta gyaɗa mishi sannu da hanya ya mata sannan ta wuce ya wuce. A gindin bishiyar mangoro dake kofar gidansu gab da zaure ta hango Bappanta yana zaune bisa dakalin dake wurin yana al'wala, da sauri ta nufi in da yake fuska cike da jin daɗi. Shima Bappa da sauri ya miƙe yana murmushi yake cewa. "Maraba lale da ƴar al'barka." Da sauri ta iso inda yake tana murmushi mai nuna tsantsar jin daɗinta tace. "Oyoyo Bappa na, Alhamdulillah na sameka lfy, ya Ummey na da Innata?". Dariya yayi tare da matsota yace. "Duk muna lfy". da sauri suka juyo ta cikin gida jin muryar yayunta suna cewa. "Oh wato mu kam bakiyi kewarmu bama ko?". Da sauri tayi gabansu cikin jin daɗi tace. "Oyoyo ƴan uwana Ya Gaini, nayi kewarku mana, musamman Ya Giɗi sarkin son girma". Murmushi sukayi dukansu, Seyo ne ya kalleta tare da cewa. "Wallahi yanzuma mgnarki mukeyi da Ummey, har Junainah na cewa wai ai duk munfi sonki". Dariyar jin daɗi tayi tare da cewa. "Ayyah ƴar ƙanwaliya tawa mai kishidani". Murmushi sukayi baki ɗaya kana Lado ya kalleta tare da cewa. "Shiga gida mu zamu wuce masallaci ne". To tace kana ta nufi cikin gida tana cewa. "Yauwa yaya Giɗi dan Allah a kawomin rake". Kai ya gyaɗa mata kana suka wuce ita tayi cikin gida. Tana shiga da fara'ar jin daɗi da ɗan karfi ta buɗe murya tare da cewa. "Assalamu alaikum, gani na dawo, ina Inna ina Ummey, Junainah ina kike?". Ai kusan a tare suka fito gaba ɗayansu, wani irin tsalle Junainah ta buga tare da rugawa ta nufi kan yayar tata cikin ihu da ɗaga sauti take cewa. "Oyoyo Addana oyoyo". Da sauri Ummey ta harateta tare da cewa. "Ke Junainah magriba cefa, kike irin wannan ihu ke sam baki da nitsuwa". Ita dai batama jitaba. Da gudu ta faɗa jikin Aysha, itama Aysha wurgar da jakarta tayi ta ruggume yar uwarta. Inna da Ummey kam ido suka zuba musu, suna masu jin daɗi irin soyayya da shaƙuwar dake tsakanin yaran nasu. Dariya sukayi baki ɗayansu, cikin jin daɗi inna tace. "To yanzu dai lokacin salla yayi ku shigo kuyi salla tukun sai ayita murna dan yau dai kam nasan kwanan zaune za'ayi". Murmushi Shatu tayi tare da karasowa gabansu cikin ladabi ba biyayya tace. "Inna ina wuni". Fuska a sake tace. "Lfy lau Alhamdulillah ya karatu". "Alhamdulillah karatu dai mun samu ɗan hutu." "Masha ALLAH yayi kyau". cewar Ummey hannun Ummeyn ta kamo tare da cewa. "Ummey ina wuni". Murmushi tayi tare da shafa kekyawar fuskarta tace. "Lfy lau Shatu muje muyi salla ko?". Kanta ta ɗan sosa tare da cewa. "Ummey ni nayi sallana a mota". Dariya Ummey tayi domin ta gano cewa Shatu na fashin salla, Ita kuwa Junainah baki ta tura tare da cewa. "To ba gashi ba, ba yanzu muka gama musuba ya Giɗi ba nace mishi nafi Addana son salla, tunda ni kullum sai nayi ita kuma wata rana sai tace a a ita tayi a makka ko kuma tace wai ai tayi kuma babu wanda zai ganta tanayin sallan". Ummey ce ta. Buge bakinta tare da cewa. "To Aku uwar mgna maza wuce kiyi salla, babu wanda ke son jawabin ki". Tura baki tayi kana ta wuce cikin ɗakin nasu, tana cewa. "Ai dama nasan kunfi sonta". Ita kuwa Ummey harara ta watsawa Shatu tare da cewa. "Ke kuma kada dai ki rinƙa kiyaye bakin wannan magananniyar". Murmushi tayi ta bita kana ta ɗauki buta ta shiga bayan gida dan gyara jikinta, sannan ta dawo. Tana shiga ta samu Junainah ta idar da sallan, Gefenta ta zauna, tare da jawo jakarta, sweet ɗinta data seyo mata, ta kwaso ta fitar mata. Ai kuwa tuni fushi ya ƙare, tazo ta raɓa jikin yayartata. Ummey kuwa da Inna saida sukayi sallan isha, kafin suka, fito tsakar gida dan tuni hadarin nan ya watse sai iska mai sanyi daketa kaɗawa. Bappa da su Ya Ladoma saida aka idar da sallan isha kafin suka dawo gida. Gaba ɗayansu a tsakiyar gidan suka zauna bisa manyan taburmaii guda biyu mazan na kan ɗaya matan na kan ɗaya. Abinci sukeci mai rai da lfy, tuwon faran ɗanyar shinkafa, da miyar ɗanyar kuɓewa data sha man shanu da tantakwashi, sai kifin banda sabi kifi na araha a wurinsu. Sai

Table of Contents

Chapters

185 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});