Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 168

Chapter 168

Garkuwa Book 1 Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

jin tausayinta Ummi tace. "A a akwai abinci harda na gobe da safe ma, yanzu kam ki huta, sai dai in akwai abinda kikeso ki gaya min in yi miki". Kai ta jujjuya alamar a a kana tace. "To Ummi a kaiwa Hadimai wani abincin kada ya lalace a banza ko". Cikin gamsuwa Ummi tace to. A can Airport kuwa ƙarfe uku dai-dai jirgin Ahlin masarautar Joɗa ta sauƙa. Nan motoci suka kwatsosu. Suna isa masarautar ana kiran sallan la'asar hakane yasa matan cikine kawai suka shiga cikin gida su mazan. Masallaci suka wuce. Ana idar da salla kuwa fada suka wuce baki ɗayansu. A sashin Gimbiya Saudatu kuwa wani irin dariya mai cike da masifar jin daɗi tayi tare da cewa. "Dai-dai kenan yaro zai dawo ya taradda da mummunan lbrin matarsa ta zama zautacciyar mata...! By *GARKUWAR FULANI*"Mummunam labarin amarya ta haukace. Ai kaɗan ma kenan, kowa yaci tuwo dani miya yasha. Hegen yaro mai jajayen kunnuwan da shegen baki mutun nace masa cuta zai ce ajali, kana ce mishi cas zaice maka kulle, wannan bakin nashi mai zaro zance da inada hali dana rufeshi kirib". Hadimarta dake zaune gabanta wacce taji cikekken bayanin abinda ya faru da Shatu a sashin Hajia Mama da itama yar rahotontace ta kamo mata. Shiyasa itama ta kawo mata rahoto. Cikin jin daɗi ta kalli Laminu dake gefe yanata murmushin jin daɗi tace. "Shiga ɗaki zaka samu kuɗi a kan gadona, kazo ka bata tukuicin wannan daddaɗan labari mai armashi". To yace kana ya miƙa ya ɗauki kuɗin yazo ya bata, tayi godiya kana ta miƙe ta fita. Ita kuwa Gimbiya Saudatu Baba Basiru da Baba Nasiru ta kira ta shaida musu abinda ya faru. Nan sukayi ta murnar abun, da shirya yadda abin zai ɗunguzuma yaci gaba. A can su Sheykh kuwa saida aka idar da sallan isha'i kana kowa ya nufi Side ɗinsa kamar yadda sukeyi duk shekara in sunje umrah sun dawo. A Babban falon sashin Jabeer kuwa. Ummi ce zaune bisa kujera Hibba na gefenta. suna mgn da Umaymah a wayar Hibbab nan Ummi ke sanarwa Umaymah abinda ya faru ɗazu da hantsi na firgitarwa. Cikin tarin mamaki da al'ajabi da tsoro tace. "Ummin Jabeer to yanzu ina take? Kuma ya jikin nata? Meya jawo hakan ne?". Juyawa Ummi tayi ta kalli bayanta a hankali tace. "Tana ɗakinta tunda tayi sallan isha'i ta konta, yau ko abinci babu abinda taci, tunda gari ya waye, dan koda muka dawo idi munci dukanmu amman ita ko ruwa bata shaba, kuma har yanzu babu abinda taci". Cikin fargaba Umaymah tace. "Jazlaan ɗin ya shigo wurinku ne? Ya sanine ko bai saniba?". "A a bai shigoba, eh gsky babu wanda yasan da wannan zancen duk Masarautar Joɗa, saini, da Jamil, Jalal, Hibba, Juwairiyya, Jafar. Mune kaɗai muka san da zancen". Ajiyar zuciya mai ƙarfi Umaymah ta sauƙe cikin sanyi tace. "Kada ku damu zanyi mgna da Jazlaan, kada ku gaya mishi, in lokacin saninshi yayi zai iya sani". Ta tace tare cewa. "Masha Allah gashi ma sai yanzu ya shigo". Tana faɗin haka ta katse kiran. Ta miƙe da sauri hakama Hibba cikin jin daɗi suke cewa. "Oyoyo mutanen saudia garin Manzon Allah, Barka da zuwa lfy da dawowa lfy". Ɗan gajeren. Murmushi yayi tare da ƙarasowa cikin falon. Jalal, Jamil, Ya Jafar na biye dashi a baya. Bisa kujera ya zauna tare da kallon Ummi fuska ƙunshe da annuri yace. "Barka dai Ummi na sameku lfy!?". "Lfy lau Alhamdulillah Sheykh ya kuka baro Sheykh Abdulkareem da ahlinshin. Ina mai sunanka Sheykh Jabir Ali". Cikin jin daɗin kulawarta ga yan uwan mahaifiyarshi yace. "Alhamdulillah suna lfy, Sheykh Jabir Ali yace in gaidaku gaba ɗaya". Cikin jin daɗi tace. "Ina amsawa kuwa ngd matuƙa". Jamil dake riƙe da jakukkunan da Sheykh yace ya ɗauko a motarsa ne ya wuce dasu. Yaje ya ajiyesu a bedroom ɗin shi kana ya dawo falon. Hibba kuwa ruwa ta kawo mishi. Murmushi yayi tare da amsar goran zam-zam ɗin yace. "Baku shanye tsohon ba Ummi ni gashi na samo sabo". Hibba ce ta ɗan kalleshi tare da cewa. "Hamma Jabeer, su Sitti ma sun dawo ne?". Kai ya gyaɗa mata alamar eh. Kana ya miƙe tare da cewa. "Ummi bari inje in ɗan huta". Kai ta gyaɗa tare da cewa. "Ai dole kam saida hutu dan gajiya da rashin bacci kam ka kwasosu dole kayi ramuwar bacci". Ta ƙarishe mgnar tana kollonshi tuni ya shiga corridor'n shiga cikin falonshi. Dama kuma tuni ita da kanta ta kai mishi abinci a Dinning table ɗinshi. Nan sukaci gaba da hira. Hibba na cewa. "Umaymah na ta dawo na kusa komawa". Cikin taɓe fuska Jalal ya kalleta a fakaice. Jamil kuwa dariya yayi tare da cewa. "Za dai ki gudu yarinya faɗi gskyarki". Murmushi Ummi tayi tare da cewa. "Ba wani tsoro ai na gaya mata ta kontar da hankalinta." Jafar kuwa karatunshi yakeyi. A hankali saɓanin baya da in zai karatun da ɗan ƙarfi yakeyi. Sosai suka ɗan yi hira kana suka watse kowa ya tafi makoncinsa. Shi kuwa Sheykh yana shiga. Ya rinƙa sauƙe numfashin gajiya tare da rage kayan jikinshi. Wonka ya shiga yayi kana yasa wasu riga da wondo masu taushi yazo ya konta. Ba tare da yasha ko ruwaba, sabida tarin gajiya da bacci. Gaba ɗaya wunin yau a zaune yayi yishi ko a ɗan tsaye. Gashi rabonsa da bacci tun jiya da safe da ya ɗanyi kaɗan kafin ya tafi harami sallan walaha. Yana konciya kuwa yayi addu'o'in ya shafa jikinsa. Kana ya fuskanci allon majigi dake liƙe a bongon ɗakin wanda yake ɗauke da full ƙura'an. Karatu ya farayi daga ƙasa zuwa sama wato nasi. Ɗaga nan bacci yayi awon gaba dashi ko inna'alzzan bai jeba. Ummi da Hibba kuwa suna isa falon Shatu cikin kula Ummi tace. "Kije ku kwana kinji ko Hibba babu abinda zai sameki, Bazata miki komaiba, bata da lfy bai dace mu barta ita ɗaya ba". Cikin sanyi Hibba tace. "Gsky Ummi bazan iyaba wlh ina tsoro". Cikin hikima Ummi tace. "To muje ki hau gado ku kwanta ni kuma sai in kwanta a ƙasa kam carpet ɗin. Gyada tayi cikin gamsuwa da hakan. Haka sukayi Ummi ta kwanta a ƙasa ita kuma Hibba ta konta gefenta a ɗan tsorace. Ita kam Shatu batama san sunayi ba, domin bacci mai nauyi takeyi. Haka dai Ummi tai shiru saida ta tabbatar Hibba tayi bacci kana ta koma ɗakinta. Washe gari da safe bayan Ummi, Saratu, da Hibba sun gama karyawa ne. Shatu da tunda tai sallan asuba ta koma ta konta kan sallayar sai yanzu ta fito. Tayi wonkanta fes ta ƙenƙesa ado da kolliyar ta ba irin mai ramɓatsau ɗin nan ba. Komai dai-dai tayi abunta. Riga da siket ne na Mateyal mai taushin gaske, White Coffee mai kyau. sai ɗan ƙaramin gyale ta yafa a kanta, cikin nitsuwa ta fito. A falo ta zauna tare da juyowa ta kalli Ummi dake shirya abinci a Dinning table. "Ina kwana Ummi". Tace cikin muryarta Normal. Cikin kulawa Ummi ta juyo tare da cewa. "Lafiya lau Shatu. Kin taso kenan". Murmushi ta ɗan yi tare da cewa. "Ummi meyasa baki tadani ba, kika shiga kitchen da kanki". Kai ta jinjina

Table of Contents

Chapters

185 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});