Chapter 173
Chapter 173
"Wato ku dai har yanzu baku girma da batun doki ba". Shiru sukayi sai Affan ne yace. "Tab Yusuf kuma da in ya ga doki bai hauba jikinshi har rawa yakeyi". Murmushi Sheykh yayi kana yace. "To muje muyi salla. Tukun tunda sai anyi sallan la'asar za'a fara ko". To sukace tare da miƙa ganin ya miƙa dan tuni uku da kwata ta wuce. Affan ne ya kira Ummi tare da cewa suzo zasu tafi. A tare suka fito kitchen. Sabbin kuɗi rafa yan dubu-dubu Yusuf ya miƙawa Hibba ƙulli ɗaya dubu ɗari kenan yace. "Gashi miƙa wa Ummi ta raba muku." Affan ma ya basu. Hakama Aryan. Hibba sai tsalle take tana cewa. "Yessss my brother's Allah ya ƙara buɗi Amin Amin sukace kana suka juya zasu fita. Cikin tsare girma Shatu tace. "Mun gode, a gaida gida". Gida zaiji sukace kana suka fita suka tafi. Suma su Ummi wucewa sukayi yin al'wala. Ana idar da salla kuwa aka fara hawan daba, hawan sarki dama duk sauran shagulgula na gidajen masarautun gargaji yayin wurin taron bikin salla. MASARAUTAR Joɗa ta cika tayi maƙil da bani Adam. Haka dai akayi taron lfy aka tashi lfy sai kuma gobe in Allah ya kai rai. Washe garin ranar da sassafe. Sheykh ya tafi asibitinshi. Ko karyawa baiba. Sai kusan sha ɗaya ya dawo da alamun yunwa da gajiya tare dashi. A falon ya zauna suna gaisawa da Ummi dan basu gaisaba ya tafi daga masallacin can ya wuce. Ummi kuwa tasa Shatu ta kai mishi breakfast ɗin shi da yanzu kam in yacima ya zama lunch ne. Hibba kuwa na can ɗauki tana ƙenƙesa ado. Cikin isa da ƙasaita Gimbiya Saudatu ta shigo tsakiyar falon babu ko sallama. Haɗe fuska Sheykh yayi tare da cewa. "Wannan banzan ɗabi'a na arnatakun baya, dan ko arna yanzu suna cewa konkon, mutun kamar shanu ko mahaukaciya". Cikin isa ta iso tsakiyar falon. Dai-dai lokacin kuma Shatu ta fito falonshi. Cikin shigar doguwar riga mai ruɓi biyu. Kanta ta ɗago ta kalli Shatu kana ta kalleshi cikin yin dariyar mugunta tace. "Eh kam tabbas tunda ka auro mahaukaciya dole kasan hali da ɗabi'un mahaukata ai. Zuwa gaba kaɗan kaima zaka fara ihu da kuka da sume-sume irin na wannan al'janar fulanin daji daka auro ɗin". Cikin tarin mamaki Ummi ta kalli Shatu ta kuma kalli Hibba da yanzu ta fito, cike da al'hinin ta yaya taji wannan batun ya fasa Masarautar Joɗa yes in dai Gimbiya Saudatu taji to ai shike nan kowa ma zaiji. Shi kuwa Sheykh ba gane inda soki burutsunta ya nufaba yayi. Ita kuwa cikin watsa musu kallon ku sakarkaru ne tace. "Kuna mamakin ta ina naji, cewar ji shekaran jiya iwar haka dai wannan matar tashin tana yashe a sume da ido a wulkice tana ƙarkarwa farfaɗiya kamar mazari ne. To ai Ni duk wanda yaci tuwo dani miya yasha. Inada tawa a cikinku duk motsinku ina dashi a tafin hannuna. Nan gaba kaɗan zamu samu riƙeƙƙiyar mahaukaciya a masarautar Joɗa". Cikin tsuke fuskarsa yace. "Yanzu ma ai muna da su mahauka ta kam, ke ɗin me banbancin ki da zararrun". Shiru yayi ganin yadda Shatu keyin taku a hankali cikin isa ta nufi gaban Gimbiya Saudatu. Ummi da Hibba kuwa miƙewa tsaye sukayi. Shi kuwa Sheykh gyara zamanshi yayi tare da ɗaura ƙafarshi ɗaya bisa ɗaya. Ita kuwa Shatu a hankali ta isa gabanta. Ido ta zuba mata tare da yi mata kallon tara saura kwata. Cikin dakkeyar Muryar rashin tsoro tace. "Toh *Bushiya* mai mugun baya, Bushiya mai bayan ƙayoyi masu kama da allurai, ki buɗe idonki da kyau ki kalleni Ni AYSHA ALIYU GARKUWA ba sa'ar yinki bace uwar mahassadan duniya, in kina cin ƙasa to tabbas ki kiyayi ta curi, ki bar min mijina ya sarara ki far masa rayuwa, ɗan shi ba sa'an yinki bane ki bar min mijina ya huta baya son ihun nan da kikeyi mishi, zan kuma iyan komai dan ganin na kauda dukkan abinda baya so." Wani irin daɗi ne ya rufe zuciyar Ummi da Hibba Sheykh kuwa ƙafarshi kawai yake kaɗawa yana mai binta da wani irin kallo mai tarin ma'anoni kalmarta ta *Mijina* yake ji tana sa duk wani hudan gashin jikinsa na amsa amon kalmar yana ratsa jikinshi da zuciyarsa haka yasa bai san sanda wani yalwataccen murmushi ya subce mishiba, tabbas Shatu akwai ƙarfin hali. Ita kuwa Gimbiya Saudatu tsuru tai da ido. Itako Aysha cikin karsashi tace. "Na lura ke dabbace, sam bakya gane yarukan mgna na bani Adam, kinfi son sai an miki irin yarukanku na dabbobi. Kina tsaye da farin yawu a bakinki kina zubda jini. Yayinda wasu ke bayanki da jini a bakinsu suna fidda farin yawu. Sokuwar rama mai tsami. Ni nan da kike ganina da idona tar a buɗe na shigo Masarautar Joɗa, kada ki ganni haka Ni ɗan hakine da zaki iya renawa amman tabbas zan tsole idanun magauta ruwanshi ya tsiyaye. In kin san fullanci to. *MIN MI KURORI CITTA NFAMƊA NHEYAH* NI ```DAKKEN YAJIN BORKONE INYI KAƊAN IN KUMA ISHI MUTUN``` Ki tsumayeni tabbas zanyi daka inyi tankaɗe inyi rairaya a masarautar Joɗa!. Ke ko kallo baki isheni ba domin bata ke akeyi ba da manyan Magauta nakeyi. Ja mugun bakinki ki fice min a gidana!". Rab-Rab. Jalal da Jamil dake da Jafar shigowa ne, suka tafa mata da hannu bibbiyu. Hakama Hibba. Ummi kuwa ƙasa tayi da kanta. Shi kuwa Sheykh ƙanƙance idonsa yayi yana kallonsu yana kaɗa ƙafa ya watsa idanunshi cikin na Gimbiya Saudatu yana mata kallon itama ta isheki. Aunty Juwairiyya kuma da tun ɗazu tana bakin ƙofar shigowa da sauri ta juya ta koma Side ɗin ta. Ya Jafar kuwa sai murmushi yake tare da dunƙulawa Shatu hannunshi kamar haka👍🏻 Wani irin juyawa Gimbiya Saudatu tayi tare da jan al'kyabbar ta ta fita. Har taje bakin ƙofa Shatu tace. "Ki riƙe kalmar mahaukaciya tabbas zakiga mahaukata a masarautar Joɗa zasu baiyana bila'adadin." Daga nan ta juya ta nufi Dinning area ɗin babban falon. Ita kuwa Gimbiya Saudatu ta juya ta fita. Shi kuwa Sheykh Jabeer a hankali ya sauƙe ƙafafunshi kana ya miƙa ya nufi falonshi. Haka nan yaji murmushi na tsubce mishi. Tabbas ya gamsu da ƙarfin halin Shatu da rashin tsoronta, sai dai yana jiye mata tuggun mutanen da bata san halinsu ba. Yana shiga yaci abinci kana ya shiga yayi wonka. Kana ya ɗauki wayarsa. Jalal, Jamil, Hibba, Ya Jafar, Shatu kuwa zama sukayi a falon cikin mamaki Ummi tace. "To wacece yar leƙen asirin Gimbiya Saudatu a wannan sashin? Ya akayi tasan abinda ya faru da Shatu? Waya gaya mata? Bayan in banda muyamu. Ni Juwairiyya, Hibba, Jalal, Jamil, Jafar. Wanda shi baya mgna, ita kanta Shatu bata san meya faruba batasan ya akayi ba. To waya fitar da wannan zancen a cikinmu?." Cikin gsky da gsky duk suka ce wlh babu wanda suka taɗawa mgnar Hibba harda ƙollarta tace. "Wlh ita ko Umaymah ma bata gayawa ba". To lallai kam akwai buƙatar bincike a tsakanin mu." Ummi ta faɗa tana mai cike da al'hinin abin. Ita kuwa Shatu uhummm. Kawai ta iya cewa tayi shiru bata ce komaiba. Haka dai suka tashi taron. Sheykh kuwa, number Umaymah ya kira
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185