Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 159

Chapter 159

Garkuwa Book 1 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

a kan Sheykh, ta yarda ta gamsu cewa mutun me ibada da imani da ilimi abin sone a zuciyar kowane mutum na gari. Bayan sunyi al'wala ne suka fito cikin manyan jihabai ƙatti har ƙasa suka nufi woje. Ananne Shatu tai mamakin ganin yadda kusufa-kusufa matan masarautar ke fitowa, duk suka nufi hanyar zuwa masallacin ta ƙofar dasu Lamiɗo ke bi. Suna fitowa jikin masallacin sai ga wani ƙaton rumfa na ƙara an lailayeshi da wani irin yashi fari ƙal-ƙal kana ga hasken wuta a cikinsa. ko wacce da sallaya a hannunta tuni wasu kuma sunma shimfiɗa sallayunsu sunbi jam'i hakanan matan maƙota da sauran matan bayi da hadimai duk nan suke zuwa. A jeru gaba ɗaya ananne ga kafaɗar matar sarki gata baiwa. Babu matsayi ko milki bare isa ko ƙasaita. Haka dai suka bi jam'i sai ƙarfe uku aka idar akayi addu'o'in kana akashafa aka kai sujjadar ƙarshi ta witirin. Kana akayi taiya akayi sallama duk kowa ya nufi gidanshi. Daga nan kuma aka kama aikin sahur. Suna dawowa Hibba ta kuma kunna TV nan ta samu su tuni su sun idar. Wasu nata ɗawafi ne sai addu'o'in ake jerawa. wanda sai kaji tsikar jikinka na tashi sabida yadda yake ratsa zuciya da jini. Washe gari da bayan sallan isha'i da asham, yanzu Jalal da Jamil ne kaɗai ke zuwa dan Imran da Sulaiman ma dasu aka tafi. Haka yasa yanzu duk suna zama a Dinning table suyi buɗa baki a tare. Jalal ne ya ɗan kalli Ummi cikin cin Beans salad da Shatu tayi musu. Hibba ce keta santi tana cewa. "Alhamdulillah yanzu dai saura mana azumi tara ko takwas". Murmushi sukayi, ita kuwa da sauri tace. "Kai takwas nema in sha Allah". Jamil kam tuni yake dariya tare da cewa. "Tara ne". da sauri ta kalli Ummi tare da cewa. "Ummi wai haka ne?". Cikin dariya tace. "A a ban saniba Hibbat." Plate ɗin data zuba ferfesun jan nama ta jawo tare da fara ci tana lumshe ido tace. "Takwas ɗin nema in Allah ya yarda". Allah yasa haka Shatu tace. Sai yanzu Jalal ya ɗan kallesu tare da cewa. "Ashe dai duk kanwar jace". Murmushi Ummi tayi kana sukaci gaba da cin abinci. Yau dai ana zaton salla saura kwana biyar ko shida. Da hantsi suna zaune dan yau sun tashi da wuri. Aunty Juwairiyya ce tayi sallama tare da shigowa, Bayan Ummi ta amsa mata. Gefen Hibba ta zauna tare da cewa. "Alhamdulillah Ummi ɗinkunan mu sun dawo, yanzu KB ya kawosu ya shigo ko?". "Eh ya shigo mana". Juyawa tayi ta kalli Hibba tare da cewa. "Je kice ya shigo Hibba yana nan zaki kanshi cikin baƙar mota". To tace tare da miƙewa da sauri. Jim kaɗan suka shigo tana gaba da jaka a hannunta yana biye da ita a baya da ƙattin jakunkuna guda biyu da wani yaro shi shima da manyan jakukkunan biyu. A tsakiyar falon bisa carpet suka aniye jakunkunan kana, ɗaya yaron ya juya ya fita. Shi kuwa Kabir ya zauna a ƙasa bisa carpet ɗin tare da cewa. "Barka da hantsi Ummi". "Barka dai Kabiru, munyi Sa'a an cika mana al'ƙawarin ko". Murmushi yayi tare da cewa. "Sosai ma kuwa Ummi aini telane mai amana". Hibba ce ta ɗanyi murmushi tace. "To ka bari a yebeka mana". Cikin dariya ɗan matashin yace. "A a ai duniyar yanzu kawai ka yabi kanka, dan ba lallai bane wani ya yaba maka". Dariya sukayi duka. Kana ya fara firfito da kayayyakin. Ko wanne da sunan maishi a jikinshi. In ya fito dana Ummi sai ya miƙa mata, in ya fito dana Aunty Juwairiyya da yaranta sai ya miƙa mata. Hakama na Hibba yana fitarwa yana miƙa mata. Shatu da yanzu ta fitone, ya kalla tare da cewa. "Barka da safiya Sayyada Shatu". Murmushi tayi Allah ya sani in sun ce mata Sayyada dariya suke bata wato irin ita matar Al Sheykh ko. Cikin nitsuwa da danne dariyarta tace. "Barka dai". Sai kuma ta ƙara so ta kalli Ummi tare da cewa. "Ummi waye ne shi?". "Telan mune". Ta bata amsa a taƙaicd. Cike da mamaki tace. "To ina ya sanni?". Hibba ce ta amshi zancen da cewa. "A hoto ya sanki, da mukaje kai ɗinkunanki hotonki kawai aka nuna mishi, ya ɗinka kuma kinga komai yayi dai-dai ko". Kai ta jinjina tare da cewa. "Lallai kam yayi ƙoƙari". Cikin dariya yace. "Uhum ai na iya aikina sosai Sayyada". Yanzu kam dariya sukayi duka. Kana ya zaro kayanta a ƙalla kala takwas ya miƙa mata. Amsa tayi tare da cewa. "Sannu". Hibba kuwa irga kayan tayi tare da cewa. "Kb saura kala bibbiyu a namu nan gani basu". Kanshi ya ɗan sosa tare da cewa. "Wannan yarinya akwai son kalato laifin mutum to sai jibi zan kawosu ko kuma in bawa Su Jamil in sunje amsar kayansu". Cikin murmushin Aunty Juwairiyya tace. "Yauwa ka bawa su Jalal ɗin ma kawai". To yace, kana ya miƙowa Ummi ƙatuwar jakukkuna guda uku tare da cewa. "To Ummi ga na yaranki". Murmushi tayi tare da cewa. "Ka kyauta min Kabiru ngd matuƙa, Allah yayi al'barka". Amin Amin yace kana ya sallamesu ya fita. Ita kuwa Ummi Saratu ta kwaɗawa kira tana zuwa. Ta tace. Jeki kira duk sauran hadimai suzo duk wadannan Kabiru yazo ya gansu ranar." Da sauri tace. "To kana ta juya ta fita. Ita kuwa Ummi. Inda take zaune ta nunawa Shatu. Tare da cewa. "Zo nan ki zauna, zasuzo, ko wacce zata gaya miki sunanta, sai ki duba sunan jikin kayan sai kibata, su duk kala ur'uku akayi musu. Zaki basu da kuɗi dubu biyar-biyar. Kai ta gyaɗa kana da sauri ta koma ɗalinta. Sabida. Sai yanzu ta gano me zatayi da wannan kuɗin da ya bata kenan. Kuɗin ta kwaso kana tazo ta zauna. Nan suka rinƙa zuwa suna gaidata da gaya mata sunansu. Kana Hibba ta irga dubu biyar, ta ɗaura kan kala bibbiyu sun ta basu. Ummi kuwa jakan gabanta ta buɗe tana basu takalma. Aunty Juwairiyya kuwa jakar hijabai ta buɗe tana basu. Suna godiya suna tafiya. Haka sukayi tayi har kusan awa biyu kafin suka gama, duk kayan sun ƙare sai kuɗin ne ya rage. Ganin lokacin salla yayi ne, suka tafi. Bayan sun idar da salla ne, suka fito. Nan a falon Shatu suka zauna. Suna ɗan hira sabida yau aikinsu baida yawa, kuma Saratu nacan na rage musu. A hankali wayar Ummi ta fara suwa, alamun ana kiranta. Da sauri ta kalli Hibba tare da cewa. "Hibba ɗauko min wayata a ɗaki". Miƙewa tayi tare da cewa to. Jim kaɗan ta fito da wayar da sauri ta miƙa wa Ummi wayar a kunne tare da cewa. "Amshi Ummi kiyi mgna na amsa kiran Hamma Jabeer ne, kin sanshi baya kira biyu." Cikin sauri da tarin jin daɗi Ummi tace. "Assalamu alaikum". Shi kuwa Sheykh Jabeer a can saudia yana tsaye ne a gaban dreesing mirror yana gyara igiyoyin al'kyabbar jikinshi. Tare da saƙala wayar a kunnenshi ya matseta da kafaɗarshi. Alamun sauri yake yana shirin tafiya haramine. Cikin sanyi yace. "Wa alaikissalam. Barka da gida Ummi". Fuska a sake tace. "Barka dai Sheykh, ya ibada?". "Alhamdulillah Ummi, yasu Jalal". "Suna lfy, kuma basa wasa

Table of Contents

Chapters

185 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});