Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 36

Chapter 36

Garkuwa Book 1 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

fesa mishin yasashi bacci. Daga nan suka ɗaukeshi sukaje suka sashi cikin motar da suka saka sauran yayunshi. Da suke konce kamar gawarwaki. Tsaye suke jikin motar, yayinda biyu daga ciki dakeda uniform ɗin police officers, kuma suna cikin motar da itama ta police ɗinne. Ɗaya daga cikin mutun huɗu dake gaban motarne, yasa hannu ya rufe ƙofar, sannn ɗaya kuma ya kira waya, cikin yaren Ɓachamanci yace. "Mun sace mutun biyar, uku yaran gidan Malam Liman ne, biyu daga ciki yaran gidan Ahaji Horo ne". Ɗan jim yayi alamun karɓar umarni. Tsawon daƙiƙu biyar sannan ya ƙatse kiran kana ya juyo ya kalli, sauran tare da cewa. "Yace ku, ku tafi dasu a cikin motar, ku wuce dasu,inda kuka shirya, mu kuma yace mu ɗan tsaya nan, yanzu zaiyiwa shanun Rugar Malam Liman kiranye da dogon fito. To in shanun suka nufi inda yake ba mamaki wasu su biyo shanun daga cikin makiyayan, to yace idan sun biyosu mu kashesu!". Kusan a tare suka sara mishi tare da busa sigarin dake hannunsu. Nan mutanen cikin motar sukaja, suka tafi. Su kuma saura mutun huɗun, komawa mafakarsu sukayi. Can cikin tsunƙurun dajin kuwa. Ba'ana ne zaune cikin taron matasan ƙabilar ɓachama da a ƙalla sun kai goma, cikin kausasa murya da bada umarni yace. "Zanyi fito ɗaya zuwa uku, cikin daƙiƙu 10 shanayen Malam Liman da Alhaji Haro da wasu. Zasu baiyana, a nan. Suna zuwa ku jasu ku fuskanci gabas, ta ƙasar Jihar Gombe zaku ratsa, kana ku nufi ƙasar chadi daga can." Shiru ya ɗanyi tare da zuba musu idanu, wani irin azzalumi murmushi yayi cikin barbarci ya kalli biyu dake kusa dashi wanda ƴan ƙanwar Bukar ne su barebari ne, cikin izaya yace. "Kada ku kauda ido akan ko wacce gonar makiyayin da zaku wuce ta gabanshi, ku shiga gonakin manoma, kuyi kiwo a ciki. Idan manoman suna cikin gonakin in sun muku mgna ku kashesu, sannan ku gudu da dabbobin yankin wurin". Cikin barbarci ɗaya daga cikin su yace. "Ba'ana, tsayuwa kiwon bazai ja mana tsaikoba, har cekiyar ya riskemu ba tare da munyi nisa ba". Murmushi yayi mai cike da fajirci sumar kanshi ya shafa tare da cewa. "Ba'akana Ku kiwaci duk gonakin manoma, hakanne zai jawo faɗa tsakanin MAKIYAYA da manoman, daga haka saiku gudu, kaga mun jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya, domin su mutanen duniya sun ɗauka duk wanda suka gani da dabobbi yana kiwo, BAFULATANI NE, sam mutane sun kasa ganewa cewa ba sai Fulani kaɗai ke kiwoba, kaga mun tada faɗa mun kwashi dabobbinsu, mun kashesu mun gudu, kuma in sunje kai korafinsu ga hukuma a kamasu ko a korasu ko azagesu, ace suke haddasa faɗa tsakaninsu da manoma, sun zama ƴan ta'adda a idon duniya. Mun kwashe dukiyoyinsu". Dariya sukayi baki ɗayansu, kana suka sara mishi, juyawa yayi, ya fuskanci gabas kana ya durƙusa, ya zuba guiwowinsa duka biyu a ƙasa, yatsarsa manuniya ta hannun hagu ya kafa a ƙasa, kana yatsarsa ta hannun dama kuma, ya toshe kunnenshi na dama, da ƙarfi ya rufe idanunshi kana, ya tsuke bakinsa ya rinƙa zuro iskar wata zazzafar fito mai bala'in sauti. Su kuwa sauran duk rufe ido sukayi dan jin fiton sukeyi tamkar zai fasa musu dodon kunne. Shi kuwa Ya Lado yana cikin kiwonshi kawai yaga gaba ɗaya, shanun sun juya sun fuskanci gabas, kana sun ɗaɗɗaga kunnuwansu sama, daga baya kuwa sunata karkaɗa binɗinsu. Cikin mamaki yake ratso tsakiyarsu. Dan in makiyayi yaga dabbobi suna haka yasan akwai abun da suka gani, ko mutun ko iska, ko maciji ko dai wani abu na daban to sukanyi wannan alamar dan sanar da makiyayinsu. So ganin hakane yasa Lado ya ƙara kutso kai cikinsu. Su kuwa dabbobin gaba ɗaya fiton da Ba'ana yake hurawane ya cika musu kunne, ai fa a take suka nausa a guje suka fuskanci gabas, da wani irin masifeffen gudu. Shanu da dawakai na gaba tumaki da awaki na baya hatta belbelun dake cikinsu, suna kiwo binsu sukayi. Cikin ƙarfi Ya Lado yayi wani irin ihun wanda dashi suke kiran dabbobinsu, amman ina basu juyoba. Da gudu ya fara binsu kana yana ihun neman taimako a wurin sauran makiyayan su. Amman da yake gudun dabba dana mutun ba ɗaya ba, Sun mishi nisa mai tarin yawa, hakanan shi kuma yayiwa sauran makiyayan dake biyoshi a guje su kawomishi agaji ya musu nisa. A haka suka rinƙa gudu, waɗannan mutun huɗun dake laɓene suka fito suka, tareshi ba zato ba tsammani kawai yaji an burma mishi wuƙa juyowan da zaiyi kuma yaji an kuma burma mishi wuƙaƙe a tako ina na jikinsa. A nan take ya faɗi babu rai. Su kuwa nan sukabi shanun da gudu. Koda sauran makiyayan suka iso inda gawar Ya Lado take. Hankalinsu yayi masifar tashi. Tabbas sun san babu masuyi musu wannan aikin sai ɓachama. Ko hanƙo kurar dabbobin basayi. Hankalinsu yayi mummunan tashi ganin gawar Lado, ga kuma tashin hankali da firgici rashin ganin su Gaini da Giɗi da Seyo Manunu da Sale. Junaidu ne yayi sauri ya kira mahaifinsu Ahaji Horo a waya ya sanar mishi halin da ake ciki. Wannan mummunan labari yayi matukar firgita al'ummar Rugar Bani hankalin kowa ya tashi. Hankali Bappa kuwa in yayi dubu to ya tashi, kuka cur-cur yakeyi da idanunshi. Junainah kam kuka da ihu harda burbuwa takeyi tana cewa. "Wayyo Ya Lado, Bappa ku nemo min Ya Gaini na da ya Seyo". Sai ta kuma faɗa jikin Ummey daketa kuka tamkar ranta zai fita, cikin kukan take cewa. "Ummey kicewa Bappa suje su nemo min Ya Giɗi na, kada su bari a kasheshi kamar yadda aka kashe Ya Hashimu da Ya Isa, da kuma Yaya Lado". Babu mai iya bata amsa a cikin wannan gida. Duk da tarin maƙota da suka cika gidan. suna zagaye da Inna wacce, take sume tunda taji yaranta Rai uku babusu babu dalilinsu su ko gawarsu ba'a ganiba ga kuma mutuwar Lado wanda shine yasata, sumewa. Faɗin tashin hankali da mutanen Rugar Kikan ke ciki bazai taɓa misaltuwa ba. Saidai ƙunane wanda duk mai imani zai iya ƙiyastashi a ranshi. A cikin garin kuwa tuni Arɗo Yabani yasa anyi shela anyi taron gaggawa, kowa ya shirya za'a shiga daji neman su Gaini, ko Allah zaisa a samosu. Haka matasa kusufa-kusufa suka rinƙa kusa kai cikin daji suna ratsa tsaununka da kozozzabai. Bappa kuwa da Arɗo Yabani da Ahaji Haro, da Ahaji Umaru ne da sauran dattawan rugarsu dana kewaye, gawar Lado suka ɗauko suka dawo gida da ita da sauran shanayensu gaba ɗaya matasa kuma suka bazama nemansu Gaini. Su kuwa sauran matasa majiya karfi daji suka rinƙa ratsawa. Amman babu koda kurar dabbobin nan, bare alamun su Gaini illa iyaka dai takalmansu da suka tsinto. A Rugar Bani kuwa, hankali na matukar tashe, Bappa ya tasa gawar Lado a gaba wacce sunyi mata wonka sun kimtsata cikin sutura kamar yadda shariya ta tanadar. Kuka mai tsananin cin raine ya kwabcewa Bappa, yana ruggume da gawar. Inna ma da yanzu ta farfaɗo da kukan ta farfaɗo, kuka takeyi tamkar ranta zai bar gangan jikinta. Hakama sauran matan maƙota. Hiden da Binto ma kuka sukeyi sosai a gidajensu sabida ɓacewar samarin su. Dattawan ne sukayi ta bawa Bappa

Table of Contents

Chapters

185 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});