Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 135

Chapter 135

Garkuwa Book 1 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

zaran kin ɗan yi musu mgna da murya a sama to cewa sukeyi, wai kayi musu ihu". Ya ƙarishe mgnar yana kallon corridor fitowa falonshi. Murmushi Hibba tayi tare da cewa. "Ga baki ga tsoro". Aunty Juwairiyya ce ta nuna musu wurin zama tare da fara zuba musu abincin. Ita kuwa Shatu murmushi kawai ta ɗan yi, sai taji hawaye na neman cika mata ido. Zamansu hakan ya tuna mata yayunta, ko ina suke? Wani hali suke ciki? Ko ya jikin Ummeynta? Ya Junainah keyi da kewarsu. Ba ya Lado, Babu Ya Gaini, Babu Ya Seyo, babu Ya Giɗi, sannan nima an kawoni nan an cusani cikin wani irin bahagon gida mai wuyar ganewa". A hankali tasa tafin hannunta tana share hawayenta cikin hikima. Ɗan juyowa tayi ta kalli. Umaymah dake cemata. "Shatu, ga Jalal da Jamil tagwaye ne, sune ƙannen Sheykh Jabeer da suke binshi yanada wasu ƙannen Affan baya ƙasar. Sai Imran ɗan amaryar Hajia Mama mom. sai kuma yayunsu mata, kin san su ai ko? Rumaisa da Rumana". A hankali ta gyaɗa kai alamar eh. Ita kuwa Umaymah su Jalal ta kalla tare da cewa. "Ga Auntyn ku, matar Hammanku". Jamil ne ya ɗan yi dariya tare da cewa. "Allah ya ɗaiyiba". Murmushi sukayi tare da cewa. "Amin Amin." Nan dai sukaci sukasha kana suka dawo falon. Kamar jiya haka yauma suka wuni. Umaymah da Ummi na yawan yi mata dukkan bayanin komai na Side ɗinta. Washe gari ranar. Al'hamis, da yamma taja Hibba suka koma falonta. Cikin yin ƙasa da murya tace. "Yauwa Hibba sammin wayarki. Wallahi na nemi tawa har na gaji ban ganiba tun a Side ɗin Gimbiya Aminatu". Da sauri Hibba tace. "Dama kinada wayane? Kuma ya ɓata baki faɗawa Umaymah". Da sauri ta jawo hannun Hibba tare da cewa. "Ina zakije?." "Zanje in gayawa Umaymah mana". Ta bata amsa tana cire code ɗin wayarta-ta tare da miƙa matashi, da sauri tace. "A a ki bari ke dai bani aron taki bari in kira Bappa na". Ajiye mata wayar tayi bisa cinyarta kana ta wuce ta fita. Ita kuwa Shatu, da ido ta rakata, jin tana ta rabkawa Umaymah Kira tun kafin ta fita. Ajiyan zuciya ta sauƙe tare dasa hannun ta ɗauki wayar. Jujjuya wayar tayi tare da miƙewa ta nufi bedroom ɗinta. Number Bappa ta saka, kana kirashi. tare da kara wayar a kunne mugu ɗaya ana biyu, aka amsa kiran. Wani irin murmushi tayi jin muryar Junainah tana cewa. "Bappa! Bappa ga wayarka ana kiranka". Da sauri tace. "Ƙanwaliya". Cikin wani irin mamaki da jin daɗin Junainah tace. "Laaaaah Adda Shatu, kece? Ina kike? Adda Rafi'a tazo jiya wai tana neman wayarki baya shiga, Bappa yace mata ai anyi miki aure, taita kuka tace to ya batun karatunki, Bappa ma ya nemi number ki baya shiga. Ina kika ajiye wayar ne to Adda Shatu". Cikin sanyi tace. "Wayar ta ɓata ne Junainah". Cikin tura baki tace. "To mijinki ya saya miki mana". Ido ta lumshe tare da cewa. "Ina Ummey na? Ya jikinta?". Cikin sauri tace. "Ummey tana na Kitchen, yanzu jikinta da sauƙi tana mgna kaɗan-kaɗan, ko ɗazuma itace tace. "Bappa ya kira mata ke!." Cikin tsananin jin daɗi tace. "Alhamdulillah, kai mata wayar". Da sauri ya juya ta nufi kitchen tana cewa. "Ummey! Ummey ga Adda Shatuna". Da sauri Ummey ta fito, ta amshi wayar. Cikin murya mai cike da sanyi tace. "Aysha na!". "Wasu zafafan hawayene, suka zubo mata, Cikin rawan murya tace. "Na'am Ummey na! Ya jikinki?". Ajiyan zuciya ta sauƙe tare da cewa. "Jiki da sauƙi, Shatu yaushe zaki zo?". Bappa da yanzu ya iso daga rakiyar da yayiwa Rafi'a ne, yayi murmushi tare da cewa. "Bani wayar nan". A hankali cikin girmamawa ta miƙa mishi wayar. Shi kuwa amsa yayi tare da karawa a kunne. jin muryar bappa yanayi mata sallama ne yasata jin sabbin hawaye masu masifar ɗumi, sabida tausayinshi. Duk da tsufanshi mugayen ƙabilar ɓachama basu barshiba, sun kashe mishi babban ɗan shi. Kana sun tafi da uku, sun barshi cikin zulumin suna raye ne ko sun mutu? A ina suke? Me akayi musu? Me sukeyi? Sannan itama data rage anyi mata wani irin bahagon auren da yafi kama da na mulkin mallaka. Muryarsace ta katse mata mgnar zuci da takeyi da cewa. "Shatu kina Lfy ko?". Murya na rawa tace. "Lfy lau Bappa, amman bana jin daɗin gidan, ina kewarku, ya jikin Ummey na? Ya lbrinsu su Ya Gaini an samu wani lbrin ko har yanzu shiru? Ya Ba'ana bai muku komai bako? Ya tafi ne ko yana nan?". Murmushi yayi tare da cewa. "To Shatu wacce tamɓaya ɗaya zan amsa miki'. Tana kuka tace. "Duka". Cikin hikima da jinƙai irin na iyaye yace. "To sai kinyi shiru kin dena kuka". Da sauri tasa hannu ta share hawayenta tare da cewa. "Na bari". Taku biyu yayi zuwa uku kana yace mata. "Ba'ana bai mana komaiba! Ya gudu ya bar ƙasar ma baki ɗaya! Jikin Ummey ki da sauƙi sosai! Su ya Giɗi munata addu'a in Sha Allah, in Allah ya yarda zasu baiyana garemu da izinin ubangiji. Kafuran nan kuma mun rigada mun karya ƙarfi su yanzu bazasu sake samun damar cutar da muba, in Sha Allah munfi ƙarfi su." Sai kuma ya ɗan tsagaita jin, tana murmushi mai ɗan sauti alamun jin daɗi, a hankali yaci gaba da cewa. "Rafi'a tazo, nayi mata bayanin komai, kuma in ta dawo zata zo, in an barta zata shigo". Da sauri tace. "Zan gayawa Ummi ta sanarwa sarkin ƙofa in tazo a barta ta shigo". Cikin danne ainihin tarin ƙunar watsewar gidanshi yace. "Yauwa to haka zakiyi. Sannan in sunƙi yarda kada ki damu. Umarnine gareki, kibi dukkan umarnin mijinki, kiyi mishi biyayya a cikin dukkan lamuranshi nasan bazai saki mugun abuba, kada ki saɓawa umarninshi. Kada kiyi komai saida amincewarsa. Ki kasance mai kula da lamuran rayuwarsa kada ki bar wani abun cutarwa tare dashi. Yanzu shine gatanki. Shine madadin Giɗi, Ganin, Seyo, Lado, ƙannenshi mata ki kallesu tamkar Junainah, mahaifiyarshi ki kalleta kamar Ummeynki, yan uwan mahaifiyarshi ki kallesu kamar yadda kike kallon innarku, yanzu sune ƴan uwanki. Domin naki basa kusa Ki zama GARKUWAR sa". Shiru yayi jin kuka na son kubce mishi. Ita kuwa tuni hawaye na kwaranya daga cikin manyan idanunta. Cikin sanyi yace. "Gobe zamu tafi, lardinmu, zamu koma can na wani lokaci". Wani irin tsananin razana da tsoro ta zaro ido tare da cewa. "Bappa zaku tafi Kardi kuma!? Ni ku barni a nan ba kowa nawa!?". Cikin sanyi yace. "Zamu dawo Shatu. Donke zamu dawo. Dole muje, in sanarwa iyayen innarku abinda ya faru da ita da yaranta. In kuma gayawa yan uwana halin da nake ciki a kan ɓatan yayunki, bayan salla zamu dawo. Can zamuyi azumi. Bakiga yanzu a nan ko tinkiya ba'a bar manaba". Cikin gamsuwa da zancen Bappa ta ɗan danne shessheƙan kuka tare da cewa. "Allah ya kaiku lfy ya dawo daku lfy. Amman Bappa ku barmin Junainah mana, a kawo min ita mana in samu iƴar uwa kusa dani". Cikin tausasamata zuciya yace. "Kada ki damu, su nan bazasu barki da maraiciba. Sai mun dawo zan kawo miki Junainah da kaina". Kit kiran ya ƙatse sabida kuɗin sun ƙare.

Table of Contents

Chapters

185 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});