Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 129

Chapter 129

Garkuwa Book 1 Complete Hausa Novel 1,211 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

hikima da sanyi tace. "Ka shirya gobe, ka gabatar da matarka ga ƴan uwanka da iyayenka". Hannunshi biyu yasa ya dafe kanshi. Tare da rufe idonshi, sabida sarawar da yaji kanshi nayi. sai kuma ya ɗan kalli Umaymah jin tana shessheƙan kuka. Cikin sanyi yace. "To!". Murmushi tayi tare da shafa kanshi kana ta juya ta fita da sauri. Kai tsaye sashin Gimbiya Aminatu ta wuce, ta sanar mata yadda sukayi da ɗan nata. Shi kuwa Sheykh Jabeer, a hankali ya miƙe al'kyabbar jikinshi ya zare, kana ya nufi bathroom da jallabiyar. Yana shiga ya zare jallabiyar da snglet ɗin. Kana ya shiga wurin wonkan. Ruwan sanyi ya sakarwa kanshi. sabida sarawar da kanshi keyi, tun ihun dasu Baba Basiru sukayi mishi a kanshi. Ga kuma wani sabon zance na zagaye idanun mayu da kulullukan masu konciyar ɗaukan rai na masarautarsu. A ƙalla yayi mituna biyar ruwan sanyin na zubo mishi a tsakiyar kai, kafin ya fara sauƙe ajiyan zuciya alamun kan ya fara lafawa. Al'wala yayi kana ya fito. A nan drower'n glass dake bathroom ɗin nashi ya kimtsa kanshi cikin wasu datsastsen yadi mai masifar kyau Super Nour, Noble blue mai ɗan karen kyau, tattausan yadine mara nauyi, kana yanada ɗan shara-shara kaɗan, riga da wonɗo ne dai-dai jikinshi rigar half jomfa ne wanda aka watsa mishi aiki da da baƙin surfani. in ka tsura mishi ido sosai zaka iya hango shatin snglet and white boxes jikinshi. Wani Oud mai daɗin gaske ya fesa. Kana ya fito. Baƙar fula ya kafa a kanshi wanda ya bawa tattausan gashin kanshi damar baiyana ta gefe da gefen kanshi da kuma ƙeyanshi. Fararen kyawawan Ƙafafunshi, ya zura cikin. Wasu tattausan takalma baƙi. Sai kuma yasa hannu ya ɗauki carbinshi. Agogon dake liƙe saman mirror ya kalla, Lokacin sallan la'asar yayi, dan haka dole babu baccin tsakanin azahar da la'asar ɗin da ya dawo yi. A masallaci ya samu su Haroon da Jamil. Bayan anyi sallan ne kowa ya kama sabgogin gabanshi. Shi Jabeer komawa gida yayi. Ya saka garen kayan jikinshin kana. Ya fito, Ummi ya samu tsaye a tsakiyar falon, cikin kula tace. "Zaka fitane?". Kai ya gyaɗa mata alamar eh. ba tare da damuwar rashin bata amsarba tace. "Da yan rakiya ko kai ɗaya?". Yana gyara zaman hular kanshi yace. "Ni kaɗai. Zanje gidan Malama Abubakar ne!". Murmushi tayi tare da cewa. "Ka gaida minshi". "In sha Allah zaiji. Umaymah fa?". Gane abinda yake nufine yasata cewa. "Tana can sashin Gimbiya Aminatu, wurin ɗiyarta Amarya Aysha". Kanshi ya ɗan sunkuyar ba tare da yace mata komai ba, ya fita. Malam Abubakar shine, malamin da ya fara ɗiga mishi harafin Ba''un a allon shi, wato Be a fillance, Basinmi'arra a hausance ko?. A wurin shi yayi sauƙan forko, sai dai zuwa yanzu, shi Jabeer shike ƙara wa Malam Abubakar sani, akan Nahawu da Tajwid sabida shi da karatun zaure yayi. Umaymah kuwa, ita da kanta ta sanarwa Lamiɗo cewa, gobe Sheykh zai gabatar da amaryarshi. Haka yasa, ta fara shirya Aysha, shiri na musamman. Cikin Hadiman Juwairiyya ɗaya daga cikinsu. Mai suna saratu, itace Umaymah tasa ta yarfawa Aysha zanen lalle mai ɗan karen kyau. Kana Ummi da kanta ta wonke mata kai sabida ita keyiwa Juwairiyya ma. Sosai ta fito ras. Ita kuwa Shatu duk abinda sukeyi Mata. Tunanin Hibba al'hinin da tun randa tazo bata kuma ganinta ba. tana son ta tambayesu ta rasa ta ina zata fara, dole dai haka ta haƙura tai shiru. Washe gari ranar talata. Da hantsi, ko ina na sashin Gimbiya Aminatu sai ƙashi yakeyi, sabida shiri da kimtsa amarya. Umaymah da kanta take kimtsata, wani irin dakekken wagambarine mai matukar kyau Royal blue, tasaka doguwar rigace. Tayi cib-cib da jikinta. wani irin ɗauri ɗan kwali Aunty Juwairiyya ta murza mata a kanta, irin mai stpes ɗin nan. Kana sai wata farar al'kyabbar masarauta fara ƙal mai kolliyar zaren aiki da ulunta Royal blue. da surkin Golding color mai sheƙi. Wasu fararen takalma masu ratsin Sky blue ne a kekyawan kafarta da yasha jan lalle, takalman basu cika tsini da tuduba, sai dai kuma ba dab da ƙasa bane. Tayi kyau iya kyau, sai ƙamshi da sheƙi take zubawa. Umaymah ce ta kama hannunta har zuwa falon Lamiɗo, wanda bai rigaya ya fita fadaba. Gefen Gimbiya Aminatu ta ajiyeta, kana tace. "Bari inje inzo da Angon." Murmushi Gimbiya Aminatu tayi tare da cewa. "To kuyi sauri dai". To tace kana ta fita. A can sashin Sheykh Jabeer, kuwa. Da alamun wonka ya fito, a nitse yake kimtsawa, cikin wani fitinenne yadi mai taushin gaske. yadin Royal blue ne mai masifar kyau. rigar half jomfa yar tsukekkiya, tsaki ya ɗan ja lokacin daya gama dai-dai-ta zaman rigar a jikinshi sabida tayi kib-kib a jikinshi har kamar ta ɗan matseshi. Wondon kuma irin mai iya kuibin sawune, irin sakun wondunan ahlul sunna. a hankali ya iso gaban drower'n da hulunanshi da hirami da baƙin abun saman hiramin ke jere a ciki. Har yasa hannunshi bisa wani farin hula, sai kuma ya sunkuya ya ɗan kalli. Kanshi. Fuskarshi ya ɗan tsuke, sai kuma ya ɗan juyo jin muryar Haroon yana cewa. "Wow masha Allah, gsky kayi kyau, Please ka fita haka mana, ka ganka ɗan saurayi mai jini a jika, amman in kasa al'kyabbar nan, sai kwarjininka yayi yawa yaseen. Ni kaina sai inji ina shakkarka,". Kai ya ɗan shafa kana yasa hannunshi ya zaro hiraminshi fari da baƙin zagayen. ɗaya marfin drower'n ya buɗe tare da zaro wata dakekkiyar al'kyabbar fara mai ratsin blue na zaren aiki gaba da bayanshi. Gaban gado ya dawo yana warware al'kyabbar tare da cewa Haroon. "In na fita a haka ai ji zanyi kamar babu tufafi a jikina, sabida sunyi min kaɗan." Ya ƙarishe mgnar yana zura al'kyabbar a jikinshi. Masha Allah, Haroon yace. Kana ya matsoshi yana tayashi gyara zaman al'kyabbar yana cewa. "Duk shigar da kayi tana maka kyau, in na ganka ba al'kyabbar sai inga kamar kafi kyau. In kuma kasa al'kyabbar sai inga kafi kyau". Baice dashi komaiba yaci gaba da gyara sakun hiraminshi, saida ya gama dai-dai-ta hiramin sai ya juya ya nufi, wannan drower'n da hulunanshi ke jere a steps biyu na sama. Biyu na ƙasan kuma jerin takalmanshi ne. Fararen takalma masu taushi ya saka ƙirar Gucci, Zara-zaran yatsunshi sarari sabida ba sau ciki bane ba kuma half cover bane. turare ya fesa, tare da sa hannunshin ya shafa sajenshi. Kana ya kalli Haroon daketa ɗaukar shi hoto. Cikin tura baki Haroon yace. "Na bari, nasan yanzu zakayi ƙorafi, yanzu ina zakaje?". Yana fita yace. "Valli Hospital, akwai yaron da zan duba aikin da akayi mishi". Bayanshi ya biyo tare da cewa. "To sai ka dawo". Ni zamuje wurin Budurwar Jamil taga babban yayanshi. Wani kallo ya mushi tare da cewa. "Allah ya shiryeka babban kobo". Dariya Haroon yayi tare da cewa. "Eh naji na yarda, zanje yaro ya samu matsala da ita tanata wahal dashi ba dole inje in dai-dai-ta musu matsalar ba". Juyowa yayi jin abinda Haroon yace cikin sakin gajeren murmushi yace. "Uhumm yaushe ka zama luwali, bani da lbri, to kai taka matsalarma yaushe ka warware ta, kun iya cikamu da zancen ku ƴan soyayya ne, kuma bakuma

Table of Contents

Chapters

185 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});