Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 11

Chapter 11

Garkuwa Book 1 Complete Hausa Novel 1,207 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

amman ya rigada duniya tanayi mishi kallon mashayi, tantiri kana taƙadirin yaro. Haka nan nasan Jamil ma ba mazinaci bane Umaymah amman a idanun mutanen duniya shi tamkar ɗan akuya suke ganinshi, Kamar yadda Ya Jafar yake ba majanuni bane amman mutanen duniya kallon majanun suke mishi". Kanshi ya sunkuyar cikin sakekkiyar murya yace. "Duk an liƙa musu munanan tabo, a cikin rayuwarsu, Umaymah, ni ma ɗin bazan tsiraba tabbas nasan nima akwai wani tabon da ake kallona dashi, nasan nima bazan tsiraba". Da sauri Umaymah ta sunkuyar da kanta ƙasa wasu zafafan hawaye masu azabar zafi da ƙuna a zuciya suka fara kwaranyowa a idanunta, wani zazzafan shessheƙan kuka ya kwabce mata. Jin shessheƙan kukan natane yasa Sheykh Jabeer ya ɗan ɗago kanshi cikin jarumta da ƙarfin hali yayi wani murmushi mai ciwo a rai. A hankali yace. "Kuka kuma Umaymah, inada yaƙinin ƙarfin zuciyarkine da yasani sanar dake matsalar ƴaƴan ƴar uwarki, tunda ita bazata iya yin komai a kaiba". Cikin shessheƙan kukan tace. "Ba komai Jazlaan in sha Allah babu komai face al'khairi a cikin rayuwarku, insha Allah babu wani tabon da mutane ke ganinka dashi. Yanzu yaushe zaka wuce Leddi julɓe?". Cikin miskilar murya mafi karamci yace. "Yau da dare zan wuce, gobe da asuba zamu wuce Saudiyya Sittin ta matsa tana so taje taga ahlinta". Kai ta ɗan gyaɗa kana tace. "Ibrahim ma yace ya kusa dawowa". Kanshi ya ɗan rausayar kana yace. "Eh munyi mgna dashi ɗazu". Kanshi ya ɗan juyo ya kalli sauran woyoyinsh dake bisa Stull ɗin dake gefenshi, Kiran shugan ɗaliban J.S.U Ɓadamaya ne ke shiga, bai kula kiranba yaci gaba da magana da Umaymahnshi, har saida yaga ta samu nitsuwa kafin ya barta. Tashi yayi a hankali yake taku cikin kamala da nitsuwa irinta manyan limamai a hankali yake manna farar tattausar fatar ƙafarshi da in ya taka sai kaga kamar jini zai tsallo. Yana shiga cikin ɗakin nashi, al'kyabbarsa ya cire tare da buɗe wani sashi na durowarsa ya sanƙala a masanƙalinta. Da tattausan farar jallabiyar dake ƙasanta ya shiga bedroom da ita, Wannan lokacin wonkansa ne, babu abin da zai katse mishi uzurin domin ya kasance mutun mai mutunta lokacin rayuwarsa ko wani lokacin da abinda yakeyi. Wonka yayi cikin tamfatsen bathroom ɗin nashi. Yana fitowa, ya wuce gaban dreesing mirror, kimtsawa yayi a gaggauce dan lokacin tafiya aikinshi ya karato. Koda ya gama kimtsawa cikin wasu tattausan manyan kaya riga da wondone da kuma babbar gariyarsa, kayan sun kasance farare ƙal-ƙal ne, sai zazzafan aikin kufta da akayi mishi mai blue color, kana sai hular zanna bukar daya murza bisa kanshi da yake wadace da tattausan suma baƙiƙƙirin mai sulɓi da sheƙi, hular itama farace sai ratsin blue, hakama takalman sawunshi da suka kasance irin na sarakuna ne, Agogon Daimond dake hannunshi shima yanada yanayin ɗigon blue mai garai-garai, Sai kuma ya sunkuyo ya ɗauƙi biyu daga cikin woyoyinshi yasasu a al'jihun babbar rigar tasa, jakar system ɗinshi ya ɗauka da hannunsa na dama, kana hannunshi na hagu kuma sajenshi yake shafawa a hankali har zuwa kan madai-madaicin tsabtaceccen gemunshi mai ɗan karen kyau da burgewa. A haka ya fito daga cikin ɗakin nashi. Yana fitowa cikin tamfatsen falon nashi da ya kasance yanada iyaka da bayi da hadimai duk iya karsu can bakin ƙofar babban falo bai yarda da wai bayi su shigo suyi mishi hidima har cikiba, Jamil shike kula da tsabtan sashin sirrin ɗan uwan nashi. Ido ya lumshe jin wani irin sassanyan ƙwamshi da sanyi mai ratsa zuciya daya ziyarci jiki da zuciyarshi. A hankali yake taku, har zuwa dinnin area, a hankali ya ɗan juyo, jin an jamishi kujerar. Jamil kenan. Zama yayi bisa kujerar, kana, ya miƙawa Jamil jakar system ɗin nashi. Amsa yayi ya rataya a kafaɗarshi, sannan ya matso gab kusa da ɗan uwan nashi, baƙin Tea ya haɗa mishi da zuma sai bredy wanda shima da zuma a jikinshi , wanda yasan iya abinda zai ci ya sha kenan duk da tarin. Abinci da hadiman Aunty Juwairiyya, suke kawowa dominshi ga kuma na Hadiman Hajia Mama, wanda duk Umminshi Jakadiyace ke kawosu, domin ita tana shiga har cikin falonshi ɗakin konciyarshi ne dai bata shiga, amman falo ukun nan duk tana shigarsu da kitchin da sauran ɗakunan sashin. Suna zama babu jimawa, wayar Jamil ta fara tsuwa, da sauri ya ɗauka tare da karawa a kunne, sai kuma yayi zuru-zuru da idanu ganin yadda Hammanshi ya tsareshi da fitinannun idanunshi masu sa hanjin cikinsu kaɗawa, cikin yin ƙasa da murya yace. "My love Sheykh yana kusa". Ya ƙarishe mgnar da murmushi a fuskarshi, shi kuwa Sheykh kauda idonshi yayi yaci gaba da zuƙan tea ɗin a hankali a hankali. Shi kuwa Jamil cin abinci yai haninƙan kana. Shi kuwa Sheykh ido kawai yake zubawa ƙanin nashi bai tashiba har saida yaga ɗan uwan nashi ya gama cin abincin. Sannan suka jero suka fito falo, A can bakin ƙofar shigowa babban falon suka samu sarkin ƙofa da kuma hadimai na jere a wurin suna hangosu duk suka rusuna har ƙasa har suna haɗa baki wurin cewa. "Takawarka lfy ɗan Babban Yaya jikan mai martaba sarkin Nuruddeen jika ga mai Alfarma Sarkin Musulmai Jalaluddin. Malam ɗan Malam Habibullah jinin Limamen Saudia malamai magada annabawa, jika ga ƙabilar da tafi ko wacce ƙabilar duniya d...". Hannun shi biyu ya ɗaga musu alamar amsawa gaisuwar da sukayi mishi, da kuma dakatar dasu da kirarin da sukeyin. Kana yaci gaba da taku Jamil na biye dashi a baya, Sarkin ƙofane yayi saurin rusunawa tare da cewa. "Hajia Mama ta turo jakadiya a sanar maka cewa tana buƙatar ganinka". Kanshi ya gyaɗa kana yaci gaba da tafiya, Gefen dama ya nufa, inda wani tamfatsetsen part mai tarin girma yake, a hankali hadiman dake tsaron wannan ƙofar suka fara rusunawa tare da bashi hanya da gaidashi. Tafe suke har cikin part ɗin, wani babban falo suka fara ratsawa kana suka wuce zuwa cikin wani corridor sai gasu a wani fitinenne falo mai wadatar tsabta da ƙamshi. Wasu ƴan yarane guda biyu duka mata, Suna ganinsu suka ruga a guje jikin Sheykh Jabeer suka faɗa tare da cewa. "Sabahul khair Uncle MJ". Sunkuyowa yayi ya ɗan shafa kansu tare da cewa. "Sabahul noor ya Habittey". murmushi sukayi kana suka sakeshi suka isa gaban Jamil sunkuyowa yayi ya ɗauki ƙaramar bayan sun gaidashi ne babbar ta juya da gudu tana cewa. "Ummi ga Uncle MJ". tsayawa tayi tare da kamo hannun wata kekyawar mace matashiya yar duma-duma, tayi shiga irin ta larabawa, kamo hanunta tayi suka fito falon. Murmushi ta ɗanyi tare da cewa. "Barka da safiya GARKUWAN FULANI, GARKUWAN ahlin Sitti". Fuska ya ɗan sake still bawai yayi murmushi bane, a hankali yace. "Barka da safiya". "Barka dai Sheykh Dr Garkuwa". Babbar rigarshi ya ɗan gyara tare da cewa. "Ya jikin Ya Jafar?". Kai ta ɗan ranƙwafar tare da yin rau-rau da idanunta murya na rawa tace. "Jiya kwana yayi baiyi bacciba, Sheykh, hankalina yana tashi, sabida duk randa baiyi bacciba, to kwana yake karatu yanayi yana kuka, kukan da yakeyi ɗin ne yake sashi zazzaɓi da ciwon kai, gashi ba cikin zuciyarsa yake karatunba ya wuni karatu a baiyane ya kwana karatu a baiyane babu

Table of Contents

Chapters

185 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});