Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 109

Chapter 109

Garkuwa Book 1 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

na ɗari uku kacal ta wannan number 09097853276. In kuma special Group kikeso kiyi min TRANSFER ɗin dubu ɗaya rak ta asusun na 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa. Sai ki turo shaidar biyanki ta wannan number dai 09097853276. Masu turo katin mtn numbers ɗin zaki turo ba hotonba. By *GARKUWAR FULANI* Ta ɗan buga table ɗin, tare da cewa. "Malam ka tashi kaje ka taimakawa yan uwanka musulmai! in kuma baka da lfy ne ka nemi bokaye irinka su duba lfyarka". Zuwa yanzu gaba ɗaya jikinshi tsuma yakeyi ta ciki. Kanshi ne yakeji yana jujjuya mishi sabida yadda ta konkotsa glass table ɗin da kanshi ke kife a kai. Ga kuma sautin muryarta da yake jinshi har tsakiyar kanshi. Da sauri ya ɗago kanshi tare da ware matsakaita kyawawan idanunshi na zaiba. Cikin sauri Haroon ya matsoshi ganin idanunshi sun cika tab da ƙwalla sai sheƙi sukeyi alamun suna iya zubda ƙollan a ko wanne lokacin. Cikin harɗewar murya ta larabci yacewa Haroon. "Please ka fitar da ita a nan, ta matsa kaina zata fasa min dodon kunne". Ita kuwa Shatu cikin tarin mamaki da al'ajabi ta zaro manyan idanunta tare da cewa. "Laaah!". Sai kuma ta fara ɗan ja da baya tare da cewa. "Afwan baka da lfy ne!?." Wani irin fitinenne murmushi Haroon yayi tare da cewa. "Eh baya jin daɗi ne, ɗan fita zamu kira wasu bokayen suzo su dubashi". Cikin sauri tace. "Subahanallahi bokaye kuma?". Kai ya gyaɗa mata tare da cewa. "Yesss ba haka kikace ba, ya nemi bokaye ƴan uwanshi su dubashi". Kanta ta ɗan dafe tare da cewa. "No kada ka munana min zato, ina nufin likita bokan turai ka gane ko?". Da sauri taja da baya ganin Jabeer ya miƙa tsaye da ƙarfi. Shi kuwa Sheykh Jabeer tsayuwanta kusa dashi barazana ce ga zuciyarshi tabbas zata iya faso ƙirjinshi ta fito. Ganin yadda ya haɗe fuska ya nuna mata hanyar fitane, yasa ta juya ta fita. Shi kuwa Jabeer komawa yayi ya zauna tare da sauƙe wasu tagwayen ajiyan zuciya a jere a jere. A hankali yake jin bugun zuciyarshin na ɗan dai-dai-ta kamar dai yadda yaji kafin ta shigo. Sai kuma ya fara jin zuciyarshi na tsinkewa ras-ras kamar dai tana tsoron kada wani abu yayi nesa da itane. "Ya ilahi ya mujibadda'awati ya hayyu ya ƙayyum". Sune kalaman da Jabeer yaketa maimatawa a saman lips ɗinshi. Haroon kuwa wani irin kallo yakeyi ma Jabeer mai cike da nazari. Jalal ma kallonshin yake cike da tarin mamaki duk da sun san baya son akeyin mgn da ƙarfi a kanshi, to amman idonshi bai taɓa ciko da hawaye ba, sai yau. Ita kuwa Shatu, ido ta zubawa Rafi'a da ta tsareta da ido, cikin yin ƙasa da murya tace. "Rafi'a dama, wannan shugaban tuzuran ƙasar nan, yana aiki anan asibitin gwamnatin jihar nema?". Kamo hannunta Rafi'a tayi tajata sukayi gaba. Haroon kuwa dariya yayi sabida, duk da rage muryarta da tayi sunji abinda tace, sabida wurin da suke ɗin yanada amsa kuwar amo. Cikin yin ƙasa da murya sosai Rafi'a tace. "Garkuwa ki nitsufa ki rufa mana asiri, kin ko san waye wannan?!". Shiru sukayi dukansu lokacin da suka juyo wata kekyawar mata tana bawa wasu ƴan mata Nurses a ƙalla sun kai goma lbri. Ido Rafi'a da Shatu suka zubama wannan matar cewa. "Shi wannan Dr Jabeer Habeebullah Nuruddeen Bubayero Joɗa, ba kamar sauran mutane bane, shi mutunne da Allah yayi masa wasu baiwa da nasabobi masu tarin yawa". Wata ƴar kekyawar cikinsu ne ta ɗan lumshe ido tare da cewa. "Allah ya sani Aunty ina sonshi, ina son wa'azin shi, muryarshi kawai in naji yana zuba larabci sai inji bani da sauran damuwa a duniya, sai dai shi kuma yana nan kamar dutse!". Da sauri Matar nan tace. "Ai bazai yiwuba, wlh bazai taɓa kulakiba, duk nacinki da korkosarki, shiyasa wasu ke raɗe-raɗin shi waliyi ne!". Numfashin ta sauƙe tare da ci gaba da cewa. "Duk matsayinki, kyanki, mulki, sarauta, gata, ilimi!. ko da meye kike taƙama dashi a duniya ya fiki abin". Kusan a tare suka haɗa baki wurin cewa. "Kawai dan shi jikan sarkine sai yafi mu komi?". Kanta ta jinjina tare da gyara zaman ta cikin sanyi tace. "Ba haka bane. Bari kuji kaɗan daga cikin nasabarsa. Kunga forko dai shi mutum ne wanda ubangijin yayi mishi baiwar ilimin addini dana zamani. Yana ɗaya daga cikin manyan malam da Afirka gaba ɗaya take ji dashi. Sabida a ƙiyasin malamai babu yaro matashi mai jini a jiki da tarin ilimin addini kamarshi. Tun yanada shekaru takwas a duniya ya haddaci al'ƙur'ani mai girma. Sannan ya fara karatun littafai shine matashin da yakeda haddar hadisai zunzurutunsu a kanshi sama da dubu ashirin. Kunji wannan darajeta da tasa ko manyan mutane suke girmama shi. Sannan shi jinin Masarautar Joɗa ne ta wurin mahaifinshi. Ta wurin mahaifiyarshi kuwa shi jinin sarki Jalaluddin ne, masarautar sarkin Musulmai. Kana ta wurin kakarshi data haifi mamanshi. Asalin balarabiyar saudiya ce, wacce zuriyarta ne limamen Harami. Kunga nasaba kan nasaba kenan. In kyau ne na halitta, babu irin kyan da bai ganiba, In kuwa kuɗine, ku leka ƙasan gidan saman nan zakuga ayarin motocin da sukayi mishi rakiya, to ko kakan nashi Lamiɗo motar da yake hawa bata kai ta Jabeer ba. Uwa uba shi mutun ne da ya ƙoshi da sunna, baya son bidi'a. Shi mutun ne wanda ya samu kekyawan zato a wurin mutanen duniya ake mishi shaidar salihi, mumini, mai tausayi." Da sauri suka ƙatseta da cewa. "To Aunty meya hanashi yin aure har yanzu?". Cikin maida numfashi tace. "Allahu alamu, sai dai ance kamar shi bana miji bane!". Cikin sauri wata tace. "Kai mgnar. Duniya dan Allah kiji zancen ƴan shashi faɗi. Bita da ƙulli har an samo sharrin da aka liƙa mishi bawan Allah." Rafi'a kuwa kai ta jinjinawa Shatu alamun kinji ko, ita kuwa Shatu zuru tayi kamar makahon daya tsinka garaya". Cikin sauri wacce tace tana sonshin tace. "Wlh ni dai ko shi bana miji bane zan iya zama dashi a hakan in da zai yarda muyi aure". A hankali Shatu ta gyara riƙon da tayiwa wayarta tana ɗaukar su video. A hankali matar nan ta nisa tare da cewa. "Uhum Nafeesat kenan ai kuwa da wuya ya aureki duk abinda zakiyi. Sabida kin ga Dr sugzana yar India ce ƙabilar buramin bautar wuta takeyi. Tace tana sonshin, tace in dai zai aureta zata musulunta, amman yaƙi". Da sauri ɗaya dake cinsu tace. "Sabida me yaƙi duk da tayinta na shiga addinin Allah?". Cikin sanyi matar tace. "Yayi bayani kuma manyan malamai sun gamsu da hujjarsa, inda yace, tace dole sai in zai aureta zata musulunta, kenan badon Allah zata musulunta ba sai dan sonshi. Ta kuma ce in sunyi aure duk yaransu rabasu zasuyi rabi suyi addininshi rabi suyi addininta bi ma'ana wasu suyi bautar wuta wa iyazubillah. Yace wannan dalilin yasa bazai aureta ba, kuma shi baya sonta, ya kuma gargaɗi mata su dena cewa suna sonshi. Dan shi yanzu al'majiri ne sai ya girma zaiyi aure". Dariya sukayi baki ɗayansu. Jin hakane yasa Rafi'a yana Shatu suka ci gaba da tafi. Su kuma waɗancan sukaci gaba da hirarsu. Tafiya kaɗan sukayi suka samu wasu

Table of Contents

Chapters

185 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});