Chapter 29
Chapter 29
tashi buɗe idonki ki gaya min meya sameki meke miki ciwo". Ina babu magana saima kara rumtse idanunta da tayi tare ƙara ƙaƙƙame jikin Ya Gainin nata. Ya Lado ne da Seyo suka sunkuyo kanta addu'o'in suka rinka tofa mata, duk addu'ar da tazo bakinsu tofa mata sukeyi, Giɗi kuwa ruwa yasa a tafin hannunshi yana shafa mata a fuskarta. Cikin al'hini sauran makiyayan duk suka iso kansu, ganin yadda suke birkice ne ɗaya daga cikin ƴaƴan Alhaji Haro da kuma Alhaji Umaru sukace. "Gaini mu tafi gida da ita, tunda dama lokacin tashinmu yayi, an kusa fara tafiya masallacin juma'a." Cikin damuwa Giɗi yace, "To ai bazata iya tafiya ba". Seyo ne ya miƙe cikin sauri yace. "Bari inje in kawo doki sai mu ɗaurata a kai". Da sauri Manu ɗan Alhaji Haro yace. "Yauwa yi maza, kunga ku kuma Gidi kuje duk ku haɗo mana kan dabbobi ku fuskantar dasu hanyan gida". Ai kuwa haka akayi sauran yaran duk suka kaɗa shanun. Koda Seyo ya kawo dokin, shida kanshi ya hau baya sannan aka ɗaura mishi ita a gabanshi, a haka suka nufi gida. Koda suka isa gida, da kanta ta taka har zuwa cikin gida, suna biye da ita a baya. Kai tsaye ɗakin Ummey ta shige, bisa gado ta konta ta duƙunƙune tana rawan sanyi. Da sauri Ummey da Inna da Junainah suka biyota a baya. Cikin tsoro Inna tace. "Subahanallahi Shatu meya faru". Ummey kuwa gefenta ta zauna, tare da jawo borgo tana rufe mata jikinta. Giɗi ne da yanzu ya shigo, shine ya basu lbrin iya abinda suka sani. Seyo kuma cewa yayi a mata hayaƙi. Haka kuwa akayi sukayi mata hayaƙin kana Ya Gaini ya zauna yayi mata rubutu nanma aka wonke aka bata. Jin jikinta yayi zafi jau ne, alamun zazzaɓi ne ya rufeta yasa, Ya Lado yaje ya ɗauko mata mgnin a ɗakin Bappa, nan Ummey ta bata tasha, a take bacci ya ɗauketa. Ummey kuwa da Inna woje suka fito sunata dariya dan su a zatonsu ko gajiyane yasata hakan tunda ita dai bata saba zuwa kiwoba tunda tanada yayu maza da yawa. Koda akayi sallam Juma'a aka idar, su Bappa da yaranshi kab basu dawoba saida akayi sallan la'asar kafin suka dawo gida. Ummey kuwa da Inna aikin abincin dare sukeyi wanda girkin ranar jumma'a na dabanne, zabbi biyar suke yankawa kullum jumma'a wata rana kuma tattabaru wani lokacin kuma jan nama Bappa ke saya to yauma hakanne. Inna ce zaune tanayi musu wonke-wonke yayinda Junainah kuwa keyin shara, dama wonke-wonke aikintane to duk randa takeji tsiya sai tayi ta ƙorafi, shiyasa yau tana farawa Inna ta fara aikin. Ummey kuwa tana cikin kitchin ɗinsu, wanda dama da Shatu lfyarta lau muddin tana gida ita keyi musu, girki domin Ummey ta horeta da iya girke-girken na ban mamaki. A hankali Shatu ta bude idanunta daga baccin da takeyi, Cin karfin jikinta ya ɗan dawo, a hankali ta tashi zaune, da sauri ta fito woje, sabida ganin ita ɗaya ne a ɗakin. Da sauri ta fito, Inna ce ta ganta cikin kula tace. "Shatu kin taso?". Kai ta gyaɗa mata alamar eh. Cikin kula tace. "To ya jikin naki?". A hankali tace. "Da sauƙi, Inna zanyi wonka". Mikewa tayi dan dama ta gama wonke-wonken. Botiki ta ɗauka kitchin ta shiga, ruwan zafi ta ɗebo nan take cewa Ummey. "Shatu ta farka". Murmushi Ummey tai tare da cewa. "Na jita ai wai zatayi wonka, ke kuma harda biye mata kamar ta shekara ba lfy, Shatu ba dai rakiba". Dariya suka ɗanyi, ita kuwa a tsakiya gidan ta zauna kan dakalin da ke gindin bishiyar ceɗiya dake wurin. Bayan inna ta kai mata ruwan ne ta kalli Junainah cikin sanyi tace "Junnu zoki rakani inyi wonka Mana." Ido Inna ta zaro tare da cewa. "Hahhh Shatu yau kuma ta rakaki wonkafa kikace". Kanta ta gyaɗa cikin raunin fuska tace. "Eh Inna tsoro nakeji shiyasa". Ummey dake kitchin ne ta fito rike da aikoshn data zuba zabbin data soya a ciki, tace. "Shatu ki rage tsorofa". Kai ta gyaɗa kana taja hannun Junainah tare da ɗaukan kondon kayan wonkanta, A bakin ƙofar mashiga bayan gidan tace. "Yauwa Ƙanwaliya jirani a nan". To Junainah tace, haka ta tsaya tana jiranta, Ita kuwa wonkanta tayi, a nitse kana, tana fitowa. Tayi al'wala, ɗakin Ummey ta shiga, sallan azahar da la'asar ɗin tayi, sannan ta zira wata tattausar doguwar riga. Turare ta ɗan fesa kana, ta fito, Gefen katangar kitchin ɗinsu ta samu Ummey tana haɗa wuta a murhun dake wurin. Inna kuwa zaune take a gefe, da turmi a gabanta, kana tana jajjaga tattasai da tumatur da kuma tarugu da al'basa. Taburman data fito dashine ta shimfiɗa gefensu. Inna ce ta kalli Junainah da itama yanzu ta fito wonka tace. "Yauwa Junainah zoki kawowa Addanki abinci." To tace kana tazo ta shiga ɗakin Inna. Ta fito da tire a hannunta da wasu ƴan kananun robobi guda huɗu a kai masu marfi, sai kuma kula a tsakiyarsu. A gaban Shatu ta ajiye kular. Kana ta wuce ta nufi ɗakin Ummey. Ita kuwa Aysha kular ta buɗe, dambun zogalenen a cikin wanda yaji, ganyen zogalen da kuma al'basa, sai tururi yakeyi. Ƙananan robobin kuwa, ɗaya dakekken yajin ƙaragone wanda yaji magi da borkino da kuma tafarnuwa. Kana ɗaya robar kuma, soyayyan man shanune a ciki. Ɗaya kuma yankekken al'basane da kuma tumatur, sai dafeffe kwai duk a yayyanka, Kana ɗayan kuma dambun namane mai laushi, a ciki, ɗan karamin aikoshin dake gaban Ummey taja, ta zuba dambun, kana ta zuba sauran kayan hadin. A hankali ta fara ci. Junainah da ta fito yanzune ta kalla tare da cewa. "Junainah bani ruwa". To tace kana ta juya ta nufi gindin randunarsu inda suke jere a ƙalla sun kai shida ko dan ba manya bane dukansu na taɓone masu ɗan karen sanyi, ga kuma inuwar bishiyoyin ayaba da sukayiwa randunar ƙawanya, Shiyasa ko yaushe ruwan zakajishi kamar na firiji, A kofin silver ta ɗebo mata kana tazo ta zauna gefenta, sunaci a tare. Ummey kuwa tukunyar ƙasa ta ɗaura a wuta tare da tsulala man shanu, a ciki. Kayan miyan da inna ta kirɓa ta amsa ta zuba a cikin manda yayi zafin ta fara soya miyar, zabbin da zatayi musu. Kana ɗaya murhun kuma ruwan tuwo ta aza a tukunyan ƙarfe. Inna kuwa data gama kirɓa kayan miyar, shinkafar tuwon ta ɗebo tazo tana wonkewa. Suna cikin haka su Bappa da yayunta maza suka dawo. Nan suka shimfiɗa katuwar taburma a tsakar gidan. kana Giɗi ya ajiyewa inna ledodin tsarabar jumma'a da Bappa kanyi duk ranar sati. Tirirruka Ummey ta miko mata ta baza, juye kayayyakin a cikin. Reke,Lemu, kwakwa, da Giginya, da kuma dafaffiyar gyaɗa, da ƙosai mai zafi da biredi da soyayyen doya da fulawa mai jawa. kayan cimarmu kenan fulani Zubawa maza nasu akayi, aka basu a tsakiyarsu suka ajiye sunaci da mahaifin nasu. Shatu kuwa da Junainah aka basu nasu. Ummi da Inna kuwa sun ajiye nasu dan aiki sukeyi. Ya Gaini ne ya ɗan danki ƙosai da bredy yasa a bakinshi, tauwana yayi kana idanunshi na kan Aysha saida ya haɗiye kana yace. "Shatu, ya jikin naki?". Murmushi ta ɗanyi sai kuma ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185