Chapter 93
Chapter 93
ya juya ya koma, can cikin ɗakin Jabeer ɗin. Zaune suke gaba ɗayansu, shi kuma yana konce ya duƙunƙune cikin wani jibgegen blanket mai masifar kyau da taushi. Sai karkarwa yakeyi tamkar mazari, Cikin sanyi Lamiɗo ya ɗan janye borgon tare da cewa. "Jabeer!". Duk da azaban zafin da yake ciki, bai hanashi buɗe idonshi ba, wani irin mugun kallo ya watsawa Lamiɗo, murmushi sukayi baki ɗayansu kana cikin lallami Galadima yasa hannunshi ya kamo nashi cikin sanyi yace. "Jabeer tashi ko? Tashi kasha mgni". A kufule yace. "Bazan shaba ku barni in mutu tunda hakan shine fatanku". Da sauri Abba ya kauda kai tare da yin wani faffaɗan murmushi kana, ya juyo ya kalleshi cikin bada umarni yace. "Muhammad tashi. Maza tashi kasha mgni". Kanshi ya ɗan gyaɗa kana a hankali ya fara yunƙirin tashi zaune. Ganin hakane Haroon yayi saurin taimaka mishi ya tashi zaune. Idonshi ya rumtse sabida ji yake kamar har cikin ƙasusuwan jikinshi ake tsikara da bakin allurai gashi duk inda hudar gashi yake a jikinsa sai ya ɗan tasa kamar wurin da cinaka ya ciza. Cikin tarin kula da wani mashahurin farin ciki, Lamiɗo da kanshi ya amshi haɗin maganin da sarkin Shaɗi yayi mishi a wani ma dai-dai cin kofi. Hannunshi yasa ya amshi kofin kana ya kaishi bakinshi, fuska ya kwaɓe sabida gafin mgnin da yaji a jikinshi. Cikin bada umarni Abba yace. "Ka shanye duka". Ido ya rumtse kana ya kafa kanshi ya shanye shi tas. Miƙa musu kofin yayi, kana ya amshi wani kofin da Abbansu ke miƙa mishi, Shima shanye shi yayi tas. Yana miƙa wa Lamiɗo kofin. Ya fara wani irin gyatsa mai ƙarfi, gyatsan a jere a jere. Cikin sanyi Haroon yace. "Sanno my broz". Ina babu halin amsawa dan gyatsan ya tsananta, wani irin zufane ya keto mishi daga tsakiyar kai har kan babbar yatsarshi. Wani irin murɗane ya fara ɗibanshi tamkar zai tsinke mishi ƴaƴan hanji. Cikin wani irin zabura ya fara wani irin yunƙiri. Sai gashi yanata kela wani irin baƙin amai akan tattausan blanket ɗin nan. Murmushi Sarkin Shaɗi yayi tare da kallon aman da kyau kana ya juya ya kalli Lamiɗo da Abba yace. "Da dafin kunamai yake tsuma bulalinshi, ga nan dafin yake amayarwa." Murmushi Galadima yayi tare da cewa. "Uhumm kaji mugun banza ko". Shi kuwa Abba ido ya zubawa Jabeer ganin yadda yaketa kela amai, fuskarshi nan tayi jazir, jijiyar kan goshinsa nan ta tashi ta miƙe samɓal. Haroon kuwa tallafeshi yayi yanata ce mishi sannu. Sai dai yayi kusan 30 minutes yana kwara amai kafin ya koma ya jingina da jikin Haroon yanata wasu irin zafafan numfarfashi tare da lumshe idonsa. Da sauri Lamiɗo yasa hannunshi ya tattare blanket ɗin ba tare da aman ya ɓata ko maiba. Ya dunƙuleshi ya miƙa wa sarkin Shaɗi. Da sauri Sarkin Shaɗi ya miƙa Abba wani butan duma. Sannan ya amshi borgon. Shi kuwa Lamiɗo Haroon ya kalla tare da cewa. "Cire mishi wannan rigar". Da sauri Haroon yace to kana ya fara kiciniyar cirewa mishi jallabiyar. Duk da yana galabaice saida ya ɗan ja tsaki tare da ture hannun Haroon cikin muryar dake baiyana a wahalce yake yace. "Bana so ku barmin rigata". Hannunshi Abba ya buge tare da cewa. "Bakinka bazai mutu bako". Shiru yayi yana gani Haroon ya cire mishi rigar cikin murmushin da ganin jarumta da ƙarfin hali irin na Jabeer Galadima yace. "Cire wannan ta cikinma". Ba musu ya bari Haroon ya cire mishi rigar, Wani irin zaro ido Haroon yayi gani duk jikinshi yayi shatin zanen irin manyan kunama nan". Lamiɗo da Galadima da Sarkin Shaɗi kuwa murmushi sukayi tare da haɗa baki wurin cewa. "Uhum dafin ya gama fita, cikin jininshi." Abba kuwa hannun ya haɗa ya miƙa wa Lamiɗo dake mishi alamun zai zuba mishi abu a hannun. Wani haɗin mgnin ya zuba mishi cikin tafin hannunshi. Murzawa yayi kana, ya shafa a duk jikin Jabeer. Wani irin sassanyan ajiyan zuciya ya sauƙe tare da lumshe idonshi. sabida wani irin sanyin da yaji yana ratsashi har cikin ƙasusuwan jikinshi. Tuni wani bacci mai fitinenne daɗi ya kwasheshi. Nan suka gama yi mishi komai. Kana suka fita, Dr Aliyu kuwa da Ya Hashim suka shigo bisa umarni Lamiɗo. Drip and injections Dr Aliyu ya ɗaura mishi tare dasa ruwan alluran a cikin ƙarin ruwan da akeyi mishi. Ganin sun gama yi mishi komai ne, suka fita suka tafi. Suka bar Haroon kaɗai. Dan in ruwan ya ƙare ya cire mishi. A falo kuwa Ya Hashim nayi musu bayanin ya samu bacci jikin da sauƙin duk sai suka tashi suka nufi masallaci. Jakadiyarsu da Aunty Juwairiyya aka bari a wurin. Sum jin shiru ba motsin Haroon yasa suka tafi sashin Juwairiyya dan bawa hadimanta umarnin shiga kitchen. Bayan awa ɗaya kuwa ruwan ya ƙare ya cire mishi. Ganin yana bacci ne yasa ya shiga wonka. A can cikin gidan kuwa. Sashin Gimbiya Saudatu zaune take a bisa bakin gadonta ita da Laminu ɗan ta na biyu video da yayi a Rugar Bani na zabgar Jabeer yake nuna mata, cike da tsantsar jin daɗi, sai dariyar mugunta sukeyi. Babban ɗan ta Ya Hashim ne, zaune can gefensu, ya zuba musu ido, yana nazartansu, to sukuma me sukeji a zuƙatansu, akan Jabeer da sauran ƴan uwansa shin duk wannan ƙiyeyyar ta mecece". Muryar Baba Nasiru suka jiyo a falon yana sallama. Da sauri Gimbiya Saudatu ta miƙa tsaye tare da kamo hannun Laminu tace. "Zo taho muje gacan ƙaramin Babanku". Da sauri suka nufi hanyar fita, wani irin kallo yayiwa Ya Hashim tare da jan tsaki cikin faɗa tace. "Banza mara zuciya, wanda bai san masoyansa da maƙiyansa, ai dai duk abinda nakeyi a kankane". Tana faɗin hakan suka fice. Jiki a mace yabi bayansu, Allah ya sani baya son cutar da Jabeer da sukeyi. A falon ya samesu zaune harda Baba Bashiru sunata sheƙa dariyar mugunta. Gefe can ya zauna ya zuba musu ido. Bayan sun ɗan tsagaita dariyar ne, Baba Nasira ya nisa tare da cewa. "Allah kenan maji roƙon bawa, gashi ya amsa min addu'o'in da nai a safiyar yau ɗin nan, Yadda na wuni da baƙin ciki, shi kuma zai kwana da azaba". Cikin sauri Gimbiya Saudatu tace. "Ai Ni nafi kowa farin cikin wannan dukan Kawo wuƙa da akayi wa wannan hegen yaro mai jajayen kunnu, yaro sai hegen baki da rashin tsoro duk barazanar da akeyi mishi baya kashe bakinsa. Musamman ni kam ina mgna kafinma in sauƙe numfashin ya bani amsa ga shegen azanci. Ɗan is abun buga cincim yau dai babu wannan bakin ai". Cikin dariyar ƙeta Laminu yace. "Ai wlh Umma ni so nayi a kashe hege a can, mu binneshi a waccar ƙaramar Rugar mu dawo salum salum abinmu". Cikin murtuke fuska Baba Basiru ya kallesu tare da cewa. "Ai Ni yau ko mutuwa yayi ban huce baƙin cikin dana shaƙa ba lokacin da naga ya fito ɗakin sirri da Lamiɗo har yanzu in na tuna zuciyata bugawa takeyi, to wai ma meye hakan ke nufi. Da farin ɗan uwanmu da aka bawa Galadima ya rasu dare ɗaya, ana biyu aka bawa wancan hegen yaro mai nisan kwana Jafar ɗin sarautar. Wannan abu shi yafi komai tada
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185