Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 70

Chapter 70

Garkuwa Book 1 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ga hukuma ko masarauta sai ayi burus damu, koma a ƙara mana da cin zarafi ko ƙazafi. To gashi yanzu ankai matakin ana sace mana yara, ko gawarwakinsu ba'a bar mana, shiyasa mukayi tattakin isowa gareka adalin shugaba, ka duba lamarinmu." Wani irin zafi da ƙuna ne ya cika zuciyar, Maimartaba Lamido, zalumci yayi yawa. Gyara zaman babbar Al'kebbar sarautar dake jikinsa ya ɗan yi, yana maijin ƙuna da tafasa a zuciyarshi, fargaba da tsoron, haƙin bayin Allah'n da aketa kashewa ya cika mishi zuciya, sabida sanin shine sarki kuma shugaba, ga duk wani mutun dake yankin. Wani nannauyan numfashi yaja mai ƙarfi. Juyawa yayi ya fuskanci maga takardar fadar tashi, cikin bada umarni yace. "A rubuta takarda a aikawa Haman-Ɓachama cewar ina bukatar ganinshi, da gaggawa. Kana ya tabbatar kafin ya isoni yankin da yake mulka babu sauran zalumci, ko ƙabilanci!". Cikin cika umarnin da maga takardar ya ɗan rusuna, tare da cewa. "An gama ya Mai alfarma Sarki Adalin Sarki." Waziri, Galadima, Wambai, Sarkin fada, kana da sarkin dogarai, duk, shiru sukayi sabida a zahiri ake iya hanƙo tsantsar tashin hankali da ɓacin rai a fuskar adalin shugaban nasu. Su kuwa su Bappa sosai sukaji sanyi, a zuƙatansu, sabida nuna kulawarshi garesu, cikin iya sarrafa harshe da tausasan laffuza mai martaba sarkin Nuruddeen Bubayero Joɗa yace. "Kuyi haƙuri, ku gafarceni, bani da labarin dukkan abinda ke faruwa daku, sai yanzu, naji daɗi da kuka nemeni, da matsalarku, In sha Allah ni kuwa zan ɗauki mataki, da izinin ubangiji koda belbelun dake cikin shanunku baza'a sake kashesuba, bare dabobbin ku, bare a kai ga rayukanku. Zan kirayi GARKUWAN FULANI, yanzu, zan sashi maza ya taho ya dawo ƙasar sa, Domin shiga lamuranku nauyin a kanshi yake." Sai kuma ya ɗan numfasa kana ya kalli wani bafadensa dake tsaye bayanshi yanayi mishi fifita da maficin da akayishi da gashin kekkyawan ɗawisu. Cikin bada umarni ya umarceshi daya koma gefe, Da sauri ya rusana ya koma gefen. Shi kuwa Sarki Nuruddeen, wani ɗan kekyawan matashi dake gefen damanshi ya kalla tare da cewa. "Imrana, kiramin Sheykh Jabeer." Kai ya ɗan rusunar kana yasa hannu ya amshi wayar da Kakan nashi ke miƙa mishi. Amsa yayi, kana ya kira Sheykh Jabeer, wanda shi kuma a dai-dai lokacin yana gaban Sheykh Aliyu, Abdulkareem, Jabeer, Sitti, Jazrah, Haroon. Da dai sauran ahlin nasu. Wanda kiran ne yasa ya samu ya fece daga tarkon da ake naɗa mishi. Jin wayar tayi ringing har ta katse ba'a ɗaga bane, yasa Imran ɗan rusunar da kanshi tare da cewa. "Wata ƙil baya kusa da wayar." Kai ya jinjina mishi tare da cewa. "A a zai kira, bayan amsa kirana yanzu zai kira". Kai ya gyaɗa alamar gamsuwa. Suko su Bappa duk suna zaune cikin kamala. Shi kuwa Sheykh kamar yadda ya saba, hakane baya amsa kiran kakan nashi, sai dai ya bari in tayi ta katse sai ya kira, shiyasa, yanzuma ya bari saida ta katsen sannan ya kira. Gyara zamansa yayi tare da kara wayar a kunnensa na dama. Imran kuwa yana ganin kiranshi yayi maza ya amsa, cikin tarin girmamawa yace. "Barka da hantsi, Hamma Jabeer". A can gefen Sheykh Jabeer ɗin kuwa, ido ya lumshe cikin yanayinshi da sun rigaya sun saba yayi shiru. Da sauri Imran ya kuma ɗan rusunar da kanshi yace. "Afwan Sheykh Assalamu alaikum ". Murya can ƙasa yace. "Wa alaikassalam". Cikin ɗan tura baki Imran ya kuma maimaita mgnarsa ta forko. "Barka da safiya, Hamma Jabeer ya, Sitti?". A taƙaice yace. "Alhamdulillah". Da sauri Imrana yace. "Masha Allah, ga Lamiɗo". "Na'am". Yace a takaice. Shi kuwa Imran miƙawa kakansu wayar yayi. A hankali Sheykh ya ɗan buɗa laɓɓansa cikin zazzaƙan sautin muryarsa yace. "Assalamu alaikum". Murmushi mai cike da so da ƙaunar jikan, nasa yayi tare da amsa sallamar tasa. Gaisawa sukayi, bayan sun gaisa ya tambayi labarin su Sitti da ƙanennenta da kuma mahaifinta, sai kuma ya kora mishi jawabin abinda ke faruwa a jihar tasu. Kana, ya ɗoro da cewa. "Ka dawo, kayiwa lamarin tubkar hanci". Cikin sanyi yace. "In sha Allah. Ina nan tafe, nanda kwanaki uku. Ina jajanta musu, abinda ya faru, kuma in sha Allah. hakan bazai kuma faruwa ba. Da haka sukayi sallama. A can garin Numan kuwa cikin Rugar Kikan. Gaba ɗaya garin shiru yayi, dan wannan abunda ya faru yayi masifar shiga jikinsu. Da dama maza matasanmu sun tafi kiwo, kamar yadda suka saba, rayuwar yau da kullum. Saura sai irin dattawan da aka bari, da mata da yara maza da mata. Cikin garin Bonon kuwa, gaba ɗaya, matasan garin dama ƙauyuka gefensu na ƙabulun Ɓachamawa, duk sun hallara wuri ɗaya, suna cike gaban dodon tsafinsu, wato Bonon ɗin, giyar burkutu mai ɗan karen tsami da wari, suketa sha, tamkar zasu fasa cikkunansu. Yayinda gefe guda kuma, maƙerar dake gefe wasu matasa su ne maƙera keta wasa ababen faɗansu, kamarsu wuƙaƙe, Adda, sitaka, barandami, mashi, kibau, da dai sauran mugayen makamai, sai sheƙi sukeyi. Suna cike a wurin, Ba'ana ya iso, cikin wata shigar rigar saƙi. Hanya suka rinƙa buɗa mishi, hardai ya isa ga sarkinsu, dake zaune gefen dodo sun. Zama yayi kusa da sarkin nasu ya sasu a gaba, Cikin harshen ɓacamancin yace. "Ku hanzarta, ku shiga, duk matasansu majiya ƙarfi, sun tafi kiwo. Dottijan su kuma sun tafi, kai gulmarku, ga Sarkin su wannan karon basu tsaya ga sarkinku na nanba, ina da yaƙinin kuma za'a sauraresu a can. Yanzu matansu da ƴaƴansu, ƙanana mata da mazane suka rage a garin. Sai wasu dattawansu dake, dakon dawowar magulmatan can. Kuyi maza, kushiha kafin su dawo, ku share garin kab. Ku kashesu gaba ɗaya babba da yaro mace dana miji." Da sauri wani daga cikin su yace. "Harda gidansu Shatu?". Cikin izaya yace. "Harda su, domin Mata, bata nan, ku kashe kowa nata, ta hakane zata dogara dani kaɗai tunda bata da kowa nata a duniya, dole Ni zan zama mijinta ubanta yayunta ƙannenta uwarta, in zama Garkuwarta in zame mata duniyarta ta hakane zata yarda nine ɗaya gatanta kuma duniyarta, ba tare da ta zargeniba, a hankali wata rana in sata tayi ridda, musha giya, muyi tsafi tare da ita, bazatayi min musuba, mu haifi ɗanmu na forko mu bawa dodonmu yasha jininshi yasa mana al'barka a aurenmu". Wani irin ihu da sowa na tsantsar jin daɗin bayaninshi sukayi baki ɗayansu. Hakama dodonsun, saida ihunshi ya firgitasu baki ɗayansu. Dariya mai amo mara daɗin ji. Sarkin nasu yayi, kana ya busa ƙahon dodonsun, alamun ya basu izinin tafiya. Nan fa duk suka rinƙa shiga, cikin maƙerarnan suna ɗaukan makamai, suna nufar garin Rugar Kikan (Rugar Bani) kenan a guje... Cikin garin Shikan kuwa, Bani rana ta fara tasawa, mata masu zuwa tallan nono cikin garin Numan, suka fara ɗaukar ƙorarensu, suna fita garin. Yara maza da mata kuwa, wasu na wasa wasu na ɗebo ruwa, wasu na ɗebo kayan lamɓu. Yayinda wasu kuma suka dawo break dan tara tayi. Cikinsu kuwa harda Junainah. Tafe take da saurinta da ɗan tsalle-tsallenta tana rataye da yar jakarta, da sauri ta tsaya ganin Junaidu a gabanta rike da kwanɗon zabari wanda yake cike da ƴaƴan itatuwa. Murmushi ta ɗanyi tare da sunkuyar da kanta cikin surutunta tace. "Har naji tsoro!". ta

Table of Contents

Chapters

185 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});