Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 146

Chapter 146

Garkuwa Book 1 Complete Hausa Novel 1,208 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ya fuskanci tray'n data ajiye mishi, plate ɗin fruits ya ɗan buɗe kana, ya ɗauki Fork ɗaya, janye ƙafafuwan shi, yayi ya sauƙo dasu ƙasa kana ya gyara zamanshi ya fuskanci Dinning table ɗin da kyau. Fork ɗin yasa ya fasa cikin dabino da yake irin na kwali nanne mai laushi ne, ture ɗan yayi gefe kana ya soki dabinon a hankali ya kai bakinshi, bayan yayi addu'o'in buɗa baki. Ido ya lumshe jin lokacin da sanyi da zaƙi da ɗanɗanon dabinon ya game mishi baki. Ita kuwa Shatu kuka tasa tare da riƙe ƙugunta, da kanta cikin muryar kuka take cewa. "Wayyo Allah na. Wayyo Ummey na, bayana ya karye ƙuguna ya ɓalgace, kaina ya fashe ƙeyana ya tarwatse". Ta ƙasa Glass ɗin table ɗin ya ɗan kalleta, kana ya maida kanshi yaci gaba da cin dabino, yana maijin wani irin masifeffen dariya na taso mishi jin raki da Shatu ke zubawa. Saida yaci ƙwaya bakwai, kana a hankali ya fara tsira Fork ɗin kan ƴaƴan inabi masu masifar sanyi da daɗi, ci yakeyi yana jin ƙishin daya addabi moƙoshinsa na wucewa. saida ya tsinke nonon inabin kab ya cinye, kana ya fara soka kankana da akayiwa ƙaƙanan yanka kana aka barbaɗa garin madara a samansu, shima shanye rabinshi yayi. Wani sassanyan gyatsa yayi tare da ture tray'n gefe. Ita kuwa Shatu sosai taji zafin faɗuwan ga azumi ga gajiyan aiki ga faɗuwa ga haushin yadda duk ihun da tayi babu wanda ya kulata, bare a kawo mata agaji, abun ya haɗe mata sai hawaye share-shere ta tabbatar da a gidansu ne tayi wannan ihun da gaba ɗaya iyayenta da yayunta da ƙanwarta duk suna kanta, da tuni an ɗagata a wurin ma. Bege da kewa da kukan rashin yan uwanta da watseman ahlinsu ne ya tunzura hawayenta. Ta kasa tashi sabida jikinta duk rawan yunwa da gajiya yakeyi ba ƙarfi sam. A hankali ya miƙe tsaye bayan ya sha ruwan zam-zam mai ɗan sanyi kan ƴaƴan itatuwan da yaci. System ɗinshi ya ajiye kan Dinning table ɗin, tare da wayarshi. Gefenta ya ɗan ratsa ya fara taka steps ɗin tare da kallonta a fakaice. Yana gab da sauƙane ya ɗan motsa lips ɗinshi tare da cewa. "Kaɗan kenan in dai baki dena samin ido a jikina ba, Faɗuwa harda kareireyewa zakiyi in baki kiyayi yimin kallon ƙurillaba, na lura ku mutanen wancan dajin bakuda abinda kukafi so sama da kallon killataccen wuri na jikin mutun. Muddin baki dena satan kallon jikina ba, sai waɗannan mayatattun idanun naki sun tsiyaye kin huta ki zama makauniya babu ɗan jagora. Kiyi dai a hankali ko kya samu ki mutu da idonki,". Ya ƙarishe mgnar yana tafi kamar bashi yayi mgnar ba. Ita kuwa Shatu hannun tasa ta sharce hawayenta tare da rakashi da hararan kai mugune. A falon ya samu su Ummi sunata dariya. Cikin sauri ya kalli su Jamil yace. "Kai wannan dariyar na menene, ku taso mu tafi masallaci". Cikin dariya Jamil yace. "Allah ko Hamma Jabeer ina zaton Hibba bata taɓa azumi ba sai bana. Ga yadda ta dawo wuni ɗaya, wai a haka kuma har ta fara lissafin wai yauwa yau mun kai ɗaya mun rage". Ɗan gajeren murmushi yayi tare da cewa. "Muhibbata tashi kije kiyi salla sai ki ɗan konta ki huta kafin a kira isha'i ko". Cikin sanyi tace. "To Hamma MJ". Jalal kuwa cikin yin ƙasa da murya yace. "Gobe ma zakiyi ne ko zaki huta". Cikin kwaɓe fuska tace. "Zanyi Umaymah tace, bana ko ɗaya in nasha sai na biya". Murmushi ya ɗan yi tare da cewa. "Ashe dai kin girma". Da sauri ta sunkuyar da kanta, shi kuwa yabi bayansu Jamil. Duk sukayi gaba, Sheykh kuwa na bayansu. har yaje tsakiyar falon sai kuma ya ɗan tsaya jin Ummi na ce mishi. "Shetu fa". Cikin saurin tafiya masallacin yace. "Tana can ta faɗi wai ko ta karye ne naji tana cewa ban dai san mataba". Yana kaiwa nan ya fita, ita kuwa Ummi da sauri ta miƙe cikin zaro ido tace. "Karaya kuma? Innalillahi yaushe". Tayi maganar tana nufar falonshi, A bakin ƙofar shigowa sukayi kiciɓis da ita, da sauri ta tareta tare da tallabota, jin yadda jikinta ke rawane ta jawota suka fito falon cikin tausayawa tace. "Sannu Shatu". Cikin tausaya Hibba taketa jera mata sannu. Ajiyeta bisa kujera Ummi tayi tare da cewa. "Baki sha ruwan ba ma ko?". Kanta ta gyaɗa mata alamar eh. Hakane yasa Ummi tacewa Hibba ta ɗebo mata, abin shan ruwan a take kuwa ta kawo mata. Bayan tasha ruwanne duk suka nufi cikin ɗaki dan yin salla. Daga yin sallan magriba su Jamil suka dawo sukaci abinci kafin aka kira sallan isha'i, kana suka koma akayi sallan isha'i da asham sannan suka nufi harkokin su. Shi kuwa Sheykh Jabeer daga Masallacin gidan Radio Ɓadamaya ya wuce, wurin yin shirin Fatawa. Sai tara dai-dai ya dawo, gida. A kitchen ya jiyosu. Bisa alamu duk girkin abincin sahur sukeyi. Shi kuwa bayan ya shiga, wonka yayi-yayi shirin bacci kana ya fito falonshi. Soyayyan Arish da kwan ya ɗanci tare da tarfa ferfesun ya ɗan ci. masa biyu. Jin cikinsa yayi tib ne, ya miƙe ya dawo falon. zama yayi bisa kujera yana kiran Umaymah, tana ɗagawa tace. "Jazlaan ina autata, ya azumin yau dai?". Gajeren murmushi yayi tare da cewa. "Umaymah autarki akwai raki, yau ita har ta fara lissafin an kai ɗaya saura 29/28". Dariya ta ɗanyi tare da cewa. "Kaɗan ma daga aikin Hibba". Sai kuma tace. "Ina ɗiyata kuma, ya azumin?." Kanshi ya ɗan jingina da kujera kana yace. "Alhamdulillah". Jin muryar Haroon na cewa. "Wai ɗazu ina ka shigane inata kiran wayar ka baka ɗagawa". Gyara zamanshi yayi tare da kurban coffee ɗinshi kana yace. "Na bar wayar a gida, da ɗaya na tafi na Fatawa". "To ya Amarya?". "Ban sani ba". Cikin dariya Haroon yace. "Allah baka haƙuri". Amsar wayar Umaymah tayi sukaci gaba da mgnar kan tafiyarsu Umrah. Daga bisani sukayi sallama, ya miƙa ya nufi ɗakin baccinsa. A kitchen kuwa, bayan sun gama komai na sahur ne. Ummi ta cewa Shatu taje ta ɗauko Foodflaks ɗin dake falonshi. To tace kana ta juya ta tafi. Koda ta shiga ɗan kalle-kalle tayi ganin baya nan, yasa ta harari falon ma gaba ɗayatare da cewa. "Mugu". Sannan ta ɗauki kwanukan ta fito. Duk sauran abincin Saratu suka haɗawa ta kai musu ita da sauran hadiman. Wanke-wanke tayi kana ta tattare komai sannan ta wuce part ɗin su. Su kuma ganin har goma tayi ne, yasa sukayiwa juna saida safe duk suka shiga. Yauma kamar daren jiya haka sukayi. Washe garima haka suke tafiyar da rayuwarsu. Cikin tsari da kuma samun damar hutu da ibada dan ribatar watan Ramadan ɗin. A hankali aka fara nisawa cikin watan Ramadan, kwanaki suna ɗan mirginawa da kaɗan-kaɗan. Yau wunin azumi na biyar kenan. Da hantsi bayan sunyi walaha sunyi karatun al'ƙur'ani. Sanin yanzu Ummi na jin tabsir ɗin da yakeyi a masallacin Masarautar Joɗa ne yasa, Shatu tana gaisheta ta fito. Hibba kuwa Side ɗin Aunty Juwairiyya ta nufa. Ita kuwa Shatu falonta ta fito. Bisa kujera ta zauna, tare da kiran number Junaidu wanda Rafi'a ce, ta batashi data tare da bata haƙurin

Table of Contents

Chapters

185 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});