Chapter 40
Chapter 40
kele, cikin irin matsayin da ƴan auta kedashi a wurin iyayensu yace. "Mama, shifa zato zunubine koda ya kasance gsky. Ki dena jifar Mommy da batun wai ita ta tambaɗamu, ya za'ayi keda kanki ki rinƙa suffantamu da marasa nagarta mu dai gsky ba a tamɓaɗe mukeba, Menene a cikin mulki da sarauta, Mama akwai wani mulkine matabbaci a duniya banda mulkin mahaliccin mu, in ma Imran ya gaji sarauta menene a ciki ɗan uwanmu nefa". Cikin sanyi ta girgiza kanta a hankali tace. "Ɗan uba dai ba ɗan uwaba". A tare suka zuba mata ido baki ɗayansu. Aunty Juwairiyya kuwa, ruggume yarta kawai tayi, tana jin ranta na suya. A cikin fada kuwa, tun tuni Maimartaba ya fito, yana shigowa suka gaisa dasu Bappa ya amshesu a mutunce, cikin kulawa, da mutuntaka, bayan sun gaisa ɗinne suka koro mishi jawabin abinda ke tafe dasu. Shiru mutanen fadar sukayi baki ɗayansu, sai muryar Ardo Bani, da yake ƙare zancensa da cewa. "Babban tashin hankalinmu, kullum ɗauki ɗaɗɗayan da akeyima yaranmu da tsoffinmu. Kana a sace dabobbin mu, in mun kai kukanmu ga hukuma ko masarauta sai ayi burus damu, koma a ƙara mana da cin zarafi ko ƙazafi. To gashi yanzu ankai matakin ana sace mana yara, ko gawarwakinsu ba'a bar mana, shiyasa mukayi tattakin isowa gareka adalin shugaba, ka duba lamarinmu." Wani irin zafi da ƙuna ne ya cika zuciyar, Maimartaba Lamido, zalumci yayi yawa. Gyara zaman babbar Al'kebbar sarautar dake jikinsa ya ɗan yi, yana maijin ƙuna da tafasa a zuciyarshi, fargaba da tsoron, haƙin bayin Allah'n da aketa kashewa ya cika mishi zuciya, sabida sanin shine sarki kuma shugaba, ga duk wani mutun dake yankin. Wani nannauyan numfashi yaja mai ƙarfi. Juyawa yayi ya fuskanci maga takardar fadar tashi, cikin bada umarni yace. "A rubuta takarda a aikawa Haman-Ɓachama cewar ina bukatar ganinshi, da gaggawa. Kana ya tabbatar kafin ya isoni yankin da yake mulka babu sauran zalumci, ko ƙabilanci!". Cikin cika umarnin da maga takardar ya ɗan rusuna, tare da cewa. "An gama ya Mai alfarma Sarki Adalin Sarki." Waziri, Galadima, Wambai, Sarkin fada, kana da sarkin dogarai, duk, shiru sukayi sabida a zahiri ake iya hanƙo tsantsar tashin hankali da ɓacin rai a fuskar adalin shugaban nasu. Su kuwa su Bappa sosai sukaji sanyi, a zuƙatansu, sabida nuna kulawarshi garesu, cikin iya sarrafa harshe da tausasan laffuza mai martaba sarkin Nuruddeen Bubayero Joɗa yace. "Kuyi haƙuri, ku gafarceni, bani da labarin dukkan abinda ke faruwa daku, sai yanzu, naji daɗi da kuka nemeni, da matsalarku, In sha Allah ni kuwa zan ɗauki mataki, da izinin ubangiji koda belbelun dake cikin shanunku baza'a sake kashesuba, bare dabobbin ku, bare a kai ga rayukanku. Zan kirayi GARKUWAN FULANI, yanzu, zan sashi maza ya taho ya dawo ƙasar sa, Domin shiga lamuranku nauyin a kanshi yake." Sai kuma ya ɗan numfasa kana ya kalli wani bafadensa dake tsaye bayanshi yanayi mishi fifita da maficin da akayishi da gashin kekkyawan ɗawisu. Cikin bada umarni ya umarceshi daya koma gefe, Da sauri ya rusana ya koma gefen. Shi kuwa Sarki Nuruddeen, wani ɗan kekyawan matashi dake gefen damanshi ya kalla tare da cewa. "Imrana, kiramin Sheykh Jabeer." Kai ya ɗan rusunar kana yasa hannu ya amshi wayar da Kakan nashi ke miƙa mishi. Amsa yayi, kana ya kira Sheykh Jabeer, wanda shi kuma a dai-dai lokacin yana gaban Sheykh Aliyu, Abdulkareem, Jabeer, Sitti, Jazrah, Haroon. Da dai sauran ahlin nasu. Wanda kiran ne yasa ya samu ya fece daga tarkon da ake naɗa mishi. Jin wayar tayi ringing har ta katse ba'a ɗaga bane, yasa Imran ɗan rusunar da kanshi tare da cewa. "Wata ƙil baya kusa da wayar." Kai ya jinjina mishi tare da cewa. "A a zai kira, bayan amsa kirana yanzu zai kira". Kai ya gyaɗa alamar gamsuwa. Suko su Bappa duk suna zaune cikin kamala. Shi kuwa Sheykh kamar yadda ya saba, hakane baya amsa kiran kakan nashi, sai dai ya bari in tayi ta katse sai ya kira, shiyasa, yanzuma ya bari saida ta katsen sannan ya kira. Gyara zamansa yayi tare da kara wayar a kunnensa na dama. Imran kuwa yana ganin kiranshi yayi maza ya amsa, cikin tarin girmamawa yace. "Barka da hantsi, Hamma Jabeer". A can gefen Sheykh Jabeer ɗin kuwa, ido ya lumshe cikin yanayinshi da sun rigaya sun saba yayi shiru. Da sauri Imran ya kuma ɗan rusunar da kanshi yace. "Afwan Sheykh Assalamu alaikum ". Murya can ƙasa yace. "Wa alaikassalam". Cikin ɗan tura baki Imran ya kuma maimaita mgnarsa ta forko. "Barka da safiya, Hamma Jabeer ya, Sitti?". A taƙaice yace. "Alhamdulillah". Da sauri Imrana yace. "Masha Allah, ga Lamiɗo". "Na'am". Yace a takaice. Shi kuwa Imran miƙawa kakansu wayar yayi. A hankali Sheykh ya ɗan buɗa laɓɓansa cikin zazzaƙan sautin muryarsa yace. "Assalamu alaikum". Murmushi mai cike da so da ƙaunar jikan, nasa yayi tare da amsa sallamar tasa. Gaisawa sukayi, bayan sun gaisa ya tambayi labarin su Sitti da ƙanennenta da kuma mahaifinta, sai kuma ya kora mishi jawabin abinda ke faruwa a jihar tasu. Kana, ya ɗoro da cewa. "Ka dawo, kayiwa lamarin tubkar hanci". Cikin sanyi yace. "In sha Allah. Ina nan tafe, nanda kwanaki uku. Ina jajanta musu, abinda ya faru, kuma in sha Allah. hakan bazai kuma faruwa ba. Da haka sukayi sallama. A can garin Numan kuwa cikin Rugar Kikan. Gaba ɗaya garin shiru yayi, dan wannan abunda ya faru yayi masifar shiga jikinsu. Da dama maza matasanmu sun tafi kiwo, kamar yadda suka saba, rayuwar yau da kullum. Saura sai irin dattawan da aka bari, da mata da yara maza da mata. Cikin garin Bonon kuwa, gaba ɗaya, matasan garin dama ƙauyuka gefensu na ƙabulun Ɓachamawa, duk sun hallara wuri ɗaya, suna cike gaban dodon tsafinsu, wato Bonon ɗin, giyar burkutu mai ɗan karen tsami da wari, suketa sha, tamkar zasu fasa cikkunansu. Yayinda gefe guda kuma, maƙerar dake gefe wasu matasa su ne maƙera keta wasa ababen faɗansu, kamarsu wuƙaƙe, Adda, sitaka, barandami, mashi, kibau, da dai sauran mugayen makamai, sai sheƙi sukeyi. Suna cike a wurin, Ba'ana ya iso, cikin wata shigar rigar saƙi. Hanya suka rinƙa buɗa mishi, hardai ya isa ga sarkinsu, dake zaune gefen dodo sun. Zama yayi kusa da sarkin nasu ya sasu a gaba, Cikin harshen ɓacamancin yace. "Ku hanzarta, ku shiga, duk matasansu majiya ƙarfi, sun tafi kiwo. Dottijan su kuma sun tafi, kai gulmarku, ga Sarkin su wannan karon basu tsaya ga sarkinku na nanba, ina da yaƙinin kuma za'a sauraresu a can. Yanzu matansu da ƴaƴansu, ƙanana mata da mazane suka rage a garin. Sai wasu dattawansu dake, dakon dawowar magulmatan can. Kuyi maza, kushiha kafin su dawo, ku share garin kab. Ku kashesu gaba ɗaya babba da yaro mace dana miji." Da sauri wani daga cikin su yace. "Harda gidansu Shatu?". Cikin izaya yace. "Harda su, domin Mata, bata nan, ku kashe kowa nata, ta hakane zata dogara dani kaɗai tunda bata da kowa nata a duniya, dole Ni zan zama mijinta ubanta yayunta ƙannenta uwarta, in zama Garkuwarta in zame mata duniyarta ta hakane zata yarda nine ɗaya gatanta kuma duniyarta, ba tare da ta zargeniba, a hankali wata rana in sata tayi ridda, musha giya, muyi tsafi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185