Chapter 85
Chapter 85
tayi fresh. Wani mugun kishi ne ya turnuke Kabir, cikin bacci rai ya nufi inda Yusuf yake, tare da karbar Hydar a hannun sa sannan yace," waya baka izinin taba yaro na, kada ka kara dora wannan karamin hannun naka akan ɗana. Mai da kallon sa yayi kan Amriya yace," Amriya da gaske ne kinyi wani Auren. Cikin radhin fshimta ta kalli su Dad, girgiza mata kai suka yi data ce eh. Murmushi Amriya tayi tace kwarai kuma, baka ga alama ba. Aure muka yi, tunda yanzu ka dawo saika saka mana albarka. Dad yace toh yanzu dai kaji, Amriya yanzu bah mallakin ka bace. Dan aka ka cire rai akan ta, Grandma tace yauwa kawa ta lubabatu tanada wata yarinya Saratu a kauye, naga zaku dace sosai, kuma gata bazawara, kaga dama ance zaurawa sunfi iya kula da miji, koh ya ka gani?. Bazai yuba, Wallahi bazan yarda bah, saikun kaini wajan limamin da ya daura auren nan, wallahi wannan bah adalci bane. Indai har da gaske anyi auren nan, toh wallahi saidai na dauwama a gauro, dan babu abinda zanyi da yar ƙauye kazamai. Kallon Amriya yayi yace, "Amriya dan Allah kiji tausayi na, ki fada min gaskiya". Kallon_kallo suka shiga yi a tsakanin su, hatare suka kwashe da dariya, sannan suka hada baki wajan fadin April fool. Kallon su Kabir yayi ya girgiza kai, sannan yace dama wasa kuke da hankali na koh. Janyo Salma Yusuf yayi yace,"toh nidai kaga matata uwar dakina, yanzu aka ma juna biyu gare ta. Hatake kunya ta kama Kabir, yaji kamar ya nutse kasa saboda kunya. Murmushi Amriya tayi, sannan ta nufi inda yake tare da rungume shi hawaye ya fara bin kan kunci ta. ganin aka yasa su Dad dasu Grandma suka bar musu parlour, yayin da shima Doct Habib yayi tafiyar sa... da sauri Kabir ya share mata hawayen ta sannan yace, "kuull kar na sake ganin kin zubda hawaye kinji. Girgiza masa kai Amriya tayi tace, nayi matukar kewar ka sosai Kabir, jin sunan nasa yayi wani iri a bakin ta, kallon ta yayi yace, menene wani Kabir, kice min Kalb kamar yadda kika saba a da. Murmushi gaba daya suka yi, kallon su Adeef Kabir yayi yace, me kuma kuke yi a gida?, baku koma makaranta bah?, Dariya Adeef da Ammar suka yi sannan suka ce, tsohon zance kenan, tun yaushe muka gama har mun samu ma aiki. What!, kuna nufin kun gama makaranta?, da yardar Ubangiji ma kuwa cewar Abdul. Gaskiya nee, toh su waɗanan fah, Kabir ya fada yana kallon su Mansy, oh wai su maryam kake nufi, ai matayen mu kenen. What!, wait a minute, kuna nufin ku ukun nan aure kukayi kuma a cikin shekara daya, Sosa keya Abdul yayi tace kwarai kuwa Aure muka yi, muma yanzu mun shiga saga ciki, sai ma kaga ranar auren mu, shagali iya shagali, anyi rawa na futa fitina, saima kaga photunan da mu kayi na buga wa a jarida. gaskiya babban Yahya kayi missing abubuwa da dama wallahi. Kabir yace toh taya kuka hadu dasu, Maryam din, danni dai nasan yan duniya ne, ana yahya ya kake cewa mata yanmu yan duniya , mun hadu dasu ne fah a nan Nigeria, kuma gashi sun chanza halayen su , sun koma ga Allah, dan Allah adens tono abinda ya ruga ya wuce. Shikenen Kabir ya fada, Adeef yace nidai Maryam itace matata, Ammar yace ni kuma zulaihat ce matata, Abdul ya janyo Kalisat yace toh Ni ma ga my wife nan. Murmushi Kabir yayi yace,"masha Allah, Allah ya kara hada kan zukatan mu, gaba-daya suka amsa da Ameen. Nadira ce tace Yahya kaga ƴarmu, karbar yarinyar Kabir yayi yace, "Masha Allah, ya sunan ta? , Nadira ta bashi Amsa da fadin sunan ta Safiya, wow nice name, gashi kuwa tayi kama da ke sosai har dogon bakin Baban ta. Turo baki Sadiq yayi yace,"kaji dashi". Miko Ɗan ta ita ma Fatima tayi tace,"ga shima ɗan gogon namu, ta fada tana kallon Khalid, harara Khalid ya galla mata, sannan yace zaki yi bayani ne idan muka shiga ɗaki. Dariya Kabir yayi tare da karbar yaron, sannan ya kalli Khalid yace, toh meza kayi wa kanwar yawa idan kunne ɗakin, kardai kana dukan mun kanwa. Khalid yace, " ita tasan abinda nake nufi". Maida kallon sa Kabir yayi yace, ta shi ma mene ne sunan sa?, Fatima ta bashi amsa da cewa sunan sa Zubairu amma hana ce masa Zubair. dariya Kabir kwashe da shi. tare da fadin wanene ya saka masa wannan sunan dan Allah, Fatima tace ba shine bah, nace a saka masa Abdullahi, sai yace min wai tun kafun yayi aure yace indai dansa na fari namiji ne wai Zubairu zai saka masa. Khalid yace,"toh nayi laifi ne, sunan kaka na wato mahaifin Baba na, shiyasa nace duk ɗanda na haifa indai na miji ne, saina saka masa zubairu. Gaskiya ne,gashi kuwa kuna kama harda katon kai naka. Khalid yace oho dai duk katon kaina bankai ka ba, naga ma kafi ni. Mika wa Fatima Zubair Kabir yayi, sannan ya mike tsaye yace, Ni zan je na dawo, inaso naje baki ɗimin mahafiyata. A'a ka bari mu fara cin abinci tukun nan saika je cewar Nadira, aka kuwa aka yi saida suka ci abinci, sannan suka yi sallah tare da yiwa Allah godiya daya kara nuna musu rana mai cike da farin ciki . Bayan sun idar, Kabir ya nufi part din Momsy shiga ɗakin Momsy yayi, ya tarar da ita akan kujera a zaune, zama kusa da ita yayi, tare da dora kansa akan kafadar ta yace," Momsy na, nayi kewar ki sosai, hade rai Momsy tayi tace, "ni banga alama bah","yanzu Amriya ta dawo gare ka ka manta dani koh, ta fada tana murmushi", Murmushi Kabir yayi yace,"kunsan menene Momsy, a duk sanda na ganki bana jin cewa ina tuna wa da ita, amma idan na ganta ke ce ke fadowa a raina". Murmushi Momsy tayi, tare da shafa kansa tace,"Allah yayi wa rayuwar ka Albarka ɗana. Maza kaje yanzu matar ka na bukatar ka, tsawon shekara daya leɓen, baka tare da ita, yanzu ya kamata ka fara nuna mata soyayya, kaji koh. Insha Allahu Momsy zan je, amma kuma kibari na zauna, sabo da kema nayi kewar ki sosai, hira sosai suka sha, abun gwanin burge wa, yayin da suna yi suna dariya. Ganin garin ya fara duhu yasa Kabir faɗin bara naje, nasan Hydar na chan domin kuwa shima yayi missing daddy sa. Mike wa yayi sannan yayi wa Momsy saida safe, daga bisani ya fuce daga ɗakin, zuwa yayi ya tarar gaba daya kowa ya koma part dinsa.Murmushi ya saki, daga bisani ya shiga cikin dakin su. Tarar da Amriya yayi da kan standing mirror a zaune, ta saka kayan barci, yayin da ta daure gashin ta wanda ya' yalalo ga tsantsi ga laushi. Zuwa yayi kusa da ita, sannan ya rungume ta, ta baya, tare da karbar Ribon din hannun ta sannan ya daure mata gashin ta dashi. Ɗaukar ta yayi chakk, sannan ya dire ta akan gado. Kallon sa Amriya tayi tace,"kyakyawan Mijina ya dawo gareni . Murmushi Kabir yayi yace,"my beloved wife Sabeen kenen. Ya mutse fuska
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89