Chapter 52
Chapter 52
siyo ruwa, wanda zaku sha, Khalid yace kibarshi nizanje, Amriya tace Aa kana min bakinciki zanje Aiken mami naa, bakasan nasamu lada koh , murmushi gabadayansu sukayi ,Tana kaiwanan tafuce daga dakin. Murmushi Kabir yayi karo na farko da amriya ta burge shi. Kallon kabir mami tayi tace kabir gsk kayi dacen mata, kariketa hannu bibbiyu, karike matarka kuzauna Lfy, yadda hakkinta bazai aukanka bah itama hakkinka bazai aukan ta bah kaji, wlh sa'ar mata, irin Mace kamar amriya, mai tausayi da amana dakuma taimako daidaiku nee, kaji koh, kabir yace insha Allah mami Ngd, kifara cin abincin kafun takawo ruwan. Barana je nadawo yana kaiwanan yafuce, futan shi keda wuya suka ci karo da abbansu Khalid, gaisheshi kabir yayi, abba su Khalid Ya amsa . Tareda fadin suna ciki kuwa, kabir yabashi amsa da cewar Eh suna ciki, OK tom shikenen Ngd. Kabir yace ya hkr, abba yace wlh Lfy Ngd. Shiga dakin yayi da sallama a Bakinsa, inda su DAD suka amsa gaggaisawa sukayi, inda su DAD suka fuce suka basu guri. Inda ake sayarda ruwa amriya tanufa inda mutanen wajan sai binta suke da kallo. Sallama amriya tayi, inda mutanen wajan suka amsa, Sannan tace abani ruwa na roba, mikamata mai ruwan yayi ta karba, Tana shirin budewa tasha taji Ihuun mutane suna fadin aka mota ,aka mota. Juyawarda zatayi taji anfado mata ajiki, daka tawa amriya tayi ta dago da matar. Daga jikinta bayan amriya matar ta tsaya sannan matar tafara mgn cikin dashashiyar muryanta tace, kada kibari su kama ni Dan Allah nidin bah mahaukaciya bace. Daya daga cikin likitocin yace, ke yarinya ki matsa daga wajan matar nan mahaukaciya cee, tanada cutar mantau .tsintar ta akayi acikin ruwa . Yanzu sacatery za'a kaita shine take guduwa. Kallon idanuwan matar amriya tayi tace Wacece kee, hada idanuwa sukayi da matar Hatake hankalinta yatashi, tarike hannuwan amriya sannan tace kece, kece, tabbass kece. Kokarin cire hannunta amriya tayi tace ni Kuma menayi, matar tace ke zaki kawo karshenta, ke zaki gamadasu, dole ki gama dasu babu inda zalinci ya Dore, dole hasan cewar jaruma ta baiyyana, kada kibarsu, kada kirabudasu, ki yakesu har sai inda karfinki yakare yata. Kada kataba gazawa, yakamata ace asan cewar kin baiyyana, mai kawo karshen zalinci ta zo. Kitashi tsaye, kitada makamai ki yake su, Taruke kafadar amriya tace kada kirabudasu na rokeki, ki kawo karshensu, tabbas zun debo ruwan dafa kansu, ki kashesu karki Kyale kowa. Tana kaiwanan matar tafadi summamiya , daukar matar sukayi suka feceda itah daga asibity. sosai hankalin amriya yatashi ,jikinta yafara karkarwa. Karasowa kabir yayi ganin mutane sun taru aka yasa yaja hannun amriya suka bar wajan. Bangaren su mami kuwa, Shiga ciki abba yayi yace sannu maryam ya jiki, sama sama, mami ta amsa. Ajiyan zuciya abban su Khalid yayi yace, nasan nayimiki babban laifi, na tauye miki hakkinki a matsayinki na matata. Bansan dawane ido zan kalleki bah, tabbas na aikata kuskure kuma nagano kuskurena, Dan Allah na rokeki kiyafemin ki gafartamin, Na miki alkawarin cewa akan bazata sake maimaita kansa bah, Dan jimm mami tayi tace naji nayafe maka, Dan Allah kafuta zan kwanta. Aba maryam kenen haryanzu fushi kike dani, ki taimaka ki yafemin, wlh bada San raina nake aikata, abunda nake yamiki bah, koh kishiyarki mah tuntuni na Dade da sakinta, kawai namiki karyar cewar ta tafi wajan iyayenta Hutu nee. Mami tace toh ni ina ruwana da ita Ai bah akaina take zaune bah. Kowa zamansa yakeyi. Murmushi dad yayi yace, matata kenen, shikenen zan tsuguna Kuma na hada hannayena na rokeki Dan kisan da gsk nake . Kokarin tsugunawa yake, mami tayi Saurin mikewa tace Aa, ka rufamin asiri, sokake Allah yayi fushi dani, na yafe maka, toh idan mah ban yafe maka bah mezanyi, abunda yafaru yaruga daya faru, wlh na yafe maka duniya da lahira kuma. Nice mah yakamata ace na nemi gafarar ka sbd magganganu dana fada maka Mara dadi, Dan Allah ka yafemin. Abba yace aini babu abunda kukamin Kuma baki min laifin komai bah, akasari mah dalilin magganganu da kika fadamin yasa na gano kuskure naa, Dan aka na yafe miki. Murmushi mami tayi tace Alhmd ina mai godiya a gareka, abba yace nine yakamata na gode miki. Jijigata Kabir yashigayi Ganin tafara futa a hayyacinta,yasa yanufi gida da itah batareda yanar dasu DAD bah, direct daki yakaita, Tareda zaunan da ita yace ke meyasa meki, meyafaru, Rike hannunsa tayi wanda zoben tah ke sanye tayi, tareda saita Daidai saitin zuciyarta ta dora, zoben akai, wani irin nutsuwa ne yafara ziyartatta, dauke hannunsa zaiyi ,yaji takara kankame hannun tace, kada kacire hannunta katsaya, tsyawa yayi yana Kallon ikon Allah, rintse idanuwanta tayi sukacigaba da Tsayuwa wajan harta samu nutsuwa. Dagowa tayi tareda sakin hannunshi tace kayi hkr na Rike maka zobe batareda izininka bah, ka yafemin, Kallonta Kabir yayi yace, meyasa wancan matar naga tarike ki, meyasa kike yawan faduwa idan kinga abu ko Kuma idan an watsa miki RUWA. Meyake faruwa dake kifadamin gsk, yau inason kifuto ki gayamin asalin Wacece kee, meyasa Duk wannan, fadamin Wacece kee. Dago idanuwanta tayi wanda hawaye sukara zarya akan fuskanta, tace ni be kowa bace bace mutum irinka. Yes I know, amma inason insan dalilin dayasa kike faduwa just like that, koh ki tsuma, kokuma akasarin aka, waye yayi sanadiyan faruwan akan. Share hawayen dake bin kuncinta tayi tace, KAINE SILA . ........... 馃挮馃挮馃挮馃挮馃挮馃挮馃寠馃寠馃鈥嶁檧锔忦煣溾€嶁檧锔忦煣溾€嶁檧锔忦煣溾€嶁檧锔忦煣溾€嶁檧锔忦煣溾€嶁檧锔忦煣溾€嶁檧锔? COMMENT & SHARE PLS 馃檹馃檹馃檹. ALKALAMIN 馃枈锔忦煐婏笍馃枈锔? BABY ISHA 馃挒馃挒馃挒(AISHA M.B) 2/28/24, 22:12 - AISHA M.B (Baby isha): Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JYYV16dbYaX1dykLX7EE91 ALJANAR RUWA CE 馃鈥嶁檧锔忦煂婐煂? PAGE 4锔忊儯0锔忊儯鈻讹笍4锔忊儯1锔忊儯 WRITTEN & DIRECTED 鉁嶏笍 BY BABY ISHA 馃挒馃挒馃挒 https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*鉁嶏笍 (J.W.A) Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan 茩asaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sau茩i.鉁忥笍 ------------------------ Jin furucinta yayi kamar saukar aradu. Juyowa yayi ya da Kallon mamaki ya kalleta, ya ce "Kamar ya kenen? Ban fahimta ba." 'Dan jim Amriya tayi ta ce "Kwarai kuwa, kaine silan komai da yake faruwa da ni." Kabir ya ce "Ni Kuma taya na zama sila? fad'amin ina jinki." ya karashe maganar fuskanshi a had'e. Kallonshi tayi ta ce "Eh kaine, kuma har yau har gobe zan cigaba dafad'in kaine." Kabir ya ce "Nifa ba abunda na tambaye ki kenen bah, tambaya ta itace tayaya ni nazama sila?" Ya fad'a tare da sunkuyar da kansa gefe. "Amriya ta ce, ta yarda na ceci rayuwarka daga teku, wanda shine ta saka haryanzu ka kasance a Raye.." A firgice ya juyo ya kalleta, da sauri ya mike idan ran kabir yakai dubu to ya 'baci ,ya ce "Harke kinkai kimin karya, wato kin samu labarin cewar wata ta ceci rayuwata, Kuma na kamu da sonta, wato saboda kinsan rauni na shine kike son kibi ta salon yaudara ki yaudareni, that can never be possible." 'Dago idanuwanta amriya tayi wanda suka kada sukayi jajir, ta ce "Dan Allah ka yarda dani , wlh ni ce na taimakeka, zobena ne a hannunka wanda ya su'buce ya fad'a hannunka, dan Allah ka bani zoben na koma duniyata, inba haka bah mutuwa zanyi na rokeka." "Ya isa, wannan magganganu naki sun isheni haka, bana son na karajin komai
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89