Chapter 63
Chapter 63
toh shikenen, inajiran Duk wacce zaki kirawo, ina jira, Da sauri su, Aunty amarya da doct khadija, suka nufi hanyar waje. Tarar da su Sadiq sukayi a yashe cikin jini. Sosai su ke kuka, sun rasa yadda zasu sa rayuwarsu. Cinci barsu sukayi suka nufi part din Su nadira dasu, inda kowacce ta Fara kula da mijin ta. Kwantar da su Dad akayi, yayin da Aunty amarya ta Bawa Dad magani, yasha, bayan hour 3, jikin kowannen su ya lafa, yayinda su sadiq sun farka, kuma doct khadija tayi musu treatment, kowa aikinsu ya tashi, amma banda Kabir da haryanzu baiko Motsa bah. Hankalin su Khalid ne ya kara tashi, Dad yace Meyasa Haryanzu Kabir bai tashi bah, Dan Allah ku ceci rayuwansa, banason wani abu yasami d'ana, doct khadija tace, nayi iya bakin kokarina wajan ganin ya farka, amma babu alamun zai farka, ina tunanin fa ya fada a doguwar suma. Gaban kowannen su ne ya tashi, grandma tace khadija doguwar suma fah kika ce, yanzu menene mafuta. Dafe kanta Aunty amarya tayi, tana mai nazarin mafuta a garesu. Da sauri Aunty amarya da Dag'o, sa'anan tace, akwai mafuta, juyowa gabadayansu sukayi, suka hada baki wajan fadin, menene mafuta? Aunty amarya ta basu amsa da fadin, "Amriya", kwarai kuwa Amriya itace mafuta, zata iya, da taimakon ta, da taimakon Allah, zata iya cetan shi. Doct khadija tace da kyar Amriya ta yarda, tazo, saboda ta fadamin cewar bazata kara tako kafarta cikin wannan gidan bah, kuma yanzu bah karamin tsana tayi wa Kabir bah, da kyar mu iya shawo kanta tayi. Tazo, Khalid yace insha Allah zamu yi iya bakin kokarin mu, wajan ganin ta zo. balla kofa sukaji anyi. """"""""""""''''''''''''''''''''''"""""""""""""""""" Rasss gaban Amriya ya fadi ! , zuciyar ta, yafara Dukan uku uku, dafa ta doct Amina tayi tace, y'ata Amriya meyafaru? Amriya tace, Ammi", jikina yana bani cewar, ahalin dana baro suna cikin halin tsaka mai wuya, tundazu gabana yake ta faduwa, yusuf yace toh kije ki gani mana, ko kuma muje, Sai a lokacin Amriya ta tuna da irin cin mutuncin da suka mata. Amsa ta bawa yusuf da fadin, bazanje bah, na fasa, na ruga dana daukar wa kaina alkawarin bazan sake sanya kafafuwa na a wannan ahalin bah, dan aka, su nemar wa kansu mafuta, batareda taimakona bah. COMMENT & SHARE PLS. ALKALAMIN AISHA M.B Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JYYV16dbYaX1dykLX7EE91 https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*?? (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ?asaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sau?i_.?? ALJANAR RUWA CE ??♀?? PAGE 4??7????4??8?? WRITTEN & DIRECTED?? BY AISHA M.B (BABY ISHA) ??? ---------------------------------------- cikin rashin fahimtar maganar Amriya Doct Amina tace, taimako Kuma! Wane taimako kike musu? Ganin aka yasa Amriya Saurin chanza magana da fadin, Aa Ammi kawai dai nafada ne cewar bazan Kara taimakon su bah, amma wasa nake babu wani abu. Rike hannunwan ta Ammi tayi tace Amriya kenen, yanzu kenen baki yarda dani bah, kinai tsoro ne? na ruga dana fada miki cewa ki dauke mu tamkar ahalin ki, ki daukeni tamkar mahaifiyar ki, ki fadamin gaskiya, Dan jimmm Amriya tayi, sa'anan tace ina tsoron bayyana muku wacece ni ne saboda, dalilin akan ne yasa wancan ahalin suka koreni, Kuma ina tsoron kada kuskure daya faru ya Kara maimai ta kansa. Kallon ta bban yusuf yayi, yana mai fadin, Aa y'ata babu abunda zai faru, ki shafa wa zuciyar ki ruwan sanyi, bazamu taba butul talki bah kinji, Gyaran murya Amriya tayi sa'anan tace, a gaskiya nidin bah mutum bace kamar yadda kukayi tsanmmani, nidin ALJANAR RUWA CE, Amma Dan Allah kuyi hakuri ban fada muku asalin wacece ni bah kafun na Fara zama daku a matsayin bakuwa, ni yanzu mah zan tafi, Kallon Ammi Amriya tayi tace, gaskiya Duk wacce ta sameki a matsayin uwa, toh tabbas bah karamar yar sa'a bace, rayuwata bah karamin kyau zaiyi bah, Ni yanzu zan tashi na tafi zanje na cigaba da lallaba rayuwata. Jin kalaman ta, yasa Jikin kowanne sune yayi sanyi, shafar fuskar ta Ammi tayi tace, Aa Amriya kada kidamu muna tare dake Duk rintsi Duk wuya, baza mu taba rabuwa dake bah, Sanin cewar ke bah mutum bace akan bazai sanya mu gujeki bah, koh kadan baki yi kalan wa enda suke cutarwa bah, Kuma nidin zan kulada ke tamkar yadda mahaifiya zata kuka da yarta . Ki sani mu dake gabadaya ahalin ne yanzu, kada ki kara bambamta kanki damu kinji, nima na rasa y'ata mafi soyuwa a gareni kamar dai yadda kema kika rasa mahaifiyar ki, dan aka yanzu kinzama y'ata tabbas kedin yar sa'a ce, na tabbata da mahaifiyar ki tana nan zata yi farin cikin ganin wannan d'iya tata wacce take tattare da sa'a da Kuma alkhairy, na tabbata a koda yaushe zata kasance tana Alfa'ari dake. Murmushi Amriya tayi sa'anan tace nagode sosai Ammi, hakika kedin mahaifiya ce ta kwarai, bazan taba mantawa da irin alkhairy da kika aikata a gareni bah, rungume ta Ammi tayi Tana Mai fadin Allah yayi miki albarka y'ata. Tura baki gaba Yusuf yayi Tareda cewar, wato yanzu Ammi kinsamu Auta, ni kuma za'a manta dani koh, murmushi Ammi tayi tace Yusuf kenen sarkin k'ishi toh kaima tawo na sama albarka, Tashi yayi ya nufi inda su Amriya ke Zaune, yana isa ya zauna a kusada Ammi yace, toh nima asaka min albarka, Tom shikenen yusuf Allah yayi maka albarka, Allah ya baka Mace ta gari wacce zata haifa min jikoki, Yusuf yace, Aba Ammi jikoki kuma tun yanzu, Abba yace, toh yusuf idan bakayi aure ka haifan mana jikoki bah, me kake so kayi, wai yaushe zaka futo da mata nee, Yusuf yace kada kadamu Abba nan bada dadewa bah insha Allah, Amriya tace Kardai ka dauko mana mumuna irin wannan budurwar taka dana gani. Kallon sa sukayi baki daya, Ammi tace Dama kanada wacce kakeso baka taba Sanar mana bah, Sosa k'eya yusuf yayi Tareda fadin, Hmmm Ammi fah karya Amirya takeyi, babu wata budurwar danake da. Amriya tace Bawani karyar da nayi, ai ranar nan na ganta, yusuf yace a ina kika ganta din? a awajan nan.. ganin Amriya na shirin tona masa asiri yasa yayi Saurin daukan pillow zai buge ta dashi, Amriya na ganin aka tayi Saurin mikewa tareda nufa hanyar daki da gudu, Ammi tace Kardai ka cutar min da d'iya, dan bazan kyale ka bah, Yusuf yace Kinaji fah Ammi wlh karya take min Abba yace mum yarda karya take amma kada ka Bari wannan watan ya Kare baka kawo mana suruka bah kaji na fada maka, Yusuf yace aba Abba wata daya fah, ina laifin shekara, yanzu ni ina zanje na samo budurwa na nawa maka cikin wata nan, Abba yace Oho duk inda Kaga yayi maka ka samo , mudai burin mu ka kawo ta mugan ta, inba aka bah da kaina zan aurar dakai. Shagwaba fuska yusuf yayi, yana mai fadin Ammi kinajin mijinki koh wai ni zai aurar, kenen auran dole za'a min. Ammi tace kwarai kuwa auren dole za muyi maka, danna ga idan bah auren dolen muka makaba, toh bazaka futo mana da suruka bah. Yusuf yace Tom shikenen zan futo da mata,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89