Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 62

Chapter 62

Aljanar ruwa Ce Book 1 Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

zuru, Kabir yayi yace, Mom" shin abunda Salma ta fada gaskiya ne koh kuwa karya take miki? Shiru Mom tayi, ta rasa wane karya zata Kuma yi a wannan karan. Grandma tace, ba shiru aka ce kiyi bah Karima, tambaya ce mai sauk'i, shin kece kika kashe Ummi, kuma kika batar da Salamatu, Mom" tace wallahi karya take yi, saboda me zan kashe Ummi, me ta, tare mun, menene riba ta idan na kasheta, wallahi wannan abun kawai hadamin akayi domin kawai aga an rabani da gidan aurena. Kabir" yace toh Salma kindai ji abunda Mom ta fada, tace ita batasan wani batun kisa bah, Salma tace Aba Mom, ramin fah karya kurarre ne, say the truth and shame the devil, kiji tsoron Allah Mom, duda cewar ta sanadiyan ki nazo duniya amma akan bazai sa na rufa miki asiri bah, Kiyi hakuri Mom, ke mahaifiya ta ce, amma dole yau sai gaskiya tayi halinta, tabbas babu karya ke kika kashe Ummi, a gaban idona, ta dunga baki hak.. Bata karasa bah kuka ya kufce mata, sosai take kuka idanuwanta suka koma ciki sukayi jajirr. Cikin sheshekar kuka, Salma tace, babu abunda Salma bata ce bah, don kawai ki rabu da ita, babu koh d'igon tausayi kika samu, kwalba kika fasa mata Kai, akan baisa ta daina rokon ki bah, na dafa kafanki, nace kidau raina a madadin nata, amma kika ki, saboda son zuciyar ki, aka kika samu wuka kika kashe wacce bataji bah, bata gani bah. Ta karashe maganar tareda fashewa da wani kukan. Jikin kowa na parlour ne ya dau zafi, wani iriyar kasala ya ziyarci kowannen su. Kalisat tace, koh yanzun mah Baku yarda bah, toh inada wani prove din, zira hannu tayi cikin aljihun rigarta ta dauko waya, Sannan tayi connecting da TV, tasa play, Mom ce bayyane akan screen din TV , inda Ummi ke bata hakuri, amma samm tsabar rashin imani, ta kashe ta. Cikin kowa ne ya duri ruwa, a Hatake Mom ta hade rai. Cikin dak'a tsawa Dad yace Karima! Shin wannan kece da gaske. Mom ta Bashi amsa da fadin kwarai kuwa nice, tabbas nice nan bah kowa bah, kuma ba iya ita kadai bah, sai na hallakar da kowa na wannan family kamar yadda na tsara, Kabir kamm ji yake kamar mafarki yake, Dad yace Karima why? Dama Allah ya Barnum raina ne domin na ga wannan bakar ranar, Dama cin amanar ahalin nan kike da koh Y'ay'an ciki kin ki, baki Bari bah, why Karima? Why? Mom ta Bashi amsa da fadin, FANSA, tabbas na shigo wannan ahalin ne badan komai sai dan na dauki fansar abunda aka aikata min na wajan shekara da shekaru, Kuma tabbas saina dauki fansa akan wannan ahalin, Tana kaiwa nan ta kwashe da dariya, Tana mai fadin, wallahi Baku ga komai bah, Kai kuma Kabir, tabbas bani ce mahaifiyar ka bah kamar yadda Amriya ta fada tun farko, ni kawai na rike Kane a matsayin d'ana domin idan lokacin salwantar da rayuwar ka yayi wa qungiya ta, saina kashe ka. hawaye ne suka Fara bin kuncin Kabir yace, Mom please na roke ki kice min karya kike, wasa kawai kike yi. Hade rai Mom tayi tace, kwarai kuwa bah karya na ke fada bah, gaskiya na fada nidin, bah mahaifiyar ka bace, Jiri ne ya fara diban shi, faduwa Kabir yayi sumamme. Hankali tashe su Dad sukayi kansa, da sauri, Tareda fara jijigashi, babu abunda kakeji a gidan sai kukan su nadira. Ruwa Khalid ya dauko, sannan ya watsa masa, amma still bai koh Motsa bah, hankalinsu bah karamin Kara tashi yayi bah, Cikin baccin rai Dad ya shake wuyan Mom yace, Dama da tantiriya, nake rayuwar aure ban sani bah, ban taba zaton aka daga gareki bah, tabbas dole ki girbi abunda kika shuka. Ture Dad Mom tayi, ya fadi, da sauri su Sadiq suka nufi inda yake, d'aga shi sukayi. Tareda zaunar dashi. Babu bata lokaci high blood pressure din Dad wato BP, ya tashi, Hankalin kowa na gidan bah karamin tashi ya karayi bah, fashewa da dariya Mom tayi, tace ina farin cikin ganin wannan ahalin cikin kunci da damuwa, kamar yadda kuka sakani kunci, nima saina ga bayan ku, Cincibar Dad da Kuma Kabir sukayi, suka nufi hanyar waje dashi, cikin mota suka nufa da su, Khalid ya tada motan, sannan yayi wa su body guard magana dasu bude kofan. Ganin koh yunkurin bude kofan basuyi ba, yasa ran Sadiq baci, futowa Sadiq yayi daga cikin motan, yace bakuda hankali ne, Baku ga rayukansu na cikin had'ari bane, maza ku bude kofan kafun, ranku ya baci. Daya daga cikin body guard din yace, ba'a bamu umarnin mu bude muku kofa ba. Aka zalika, wannan gidan mallakin uwar shedanu ne, babu wani ma'aluki da ya isa yayi kokarin futa daga gidan nan, domin wannan gidan makabartar ku ce. Mutuwar tsaye Sadiq da Khalid sukayi! Ya rasa abun cewa, jiyayi gabadaya duniyar ta isheshi. Dariya gabadayansu suka kwashe dashi, daya daga cikin su yace kuna mamaki ne, toh mudin bah body guard dinku bane, kamar yadda kuka tsammani, mudin yan qungiyan asiri ne, uwar shedanu kawai muke wa aiki, Baku bah, mun zo gidan nan ne badan komai bah, sai don mu taimaka mata, ta cika burinta, akan ku. Hada hannayen sa, Sadiq yayi waje guda, yace, Dan Allah badan mu bah, ku taimaka, ku barmu, mu futa, kuna dai ganin rayukansu yana cikin hatsari, kubari mu kaisu, asibity, Dan Allah, ya karashe maganar hawaye na shirin zubo masa. Dariya suka kuma kwashe dashi a karo na biyu, suka hada baki wajan fadin, kuda futa, saidai gawar ku, baku bah, ran Sadiq da Khalid ne ya baci, lokaci daya, sukayi kan body guard din, domin, su koya musu hankali. Kokawa suka farayi da juna. Cikin rashin sa'a kuwa ,yan qungiyar asirin suka hadu, suka dunga dukan su Khalid, babu gaggauta wa. Gasu Dad da kabir rai a hannun Allah, saida suka farfasa wa su Khalid jiki, sa'anan suka wurgar dasu. Basu jisu a ko ina bah, sai jikin bishiyar gidan, yayinda kan sadiq ya fashe, yafara jini, shi Kuma Khalid ya suma. Cikin tsanani da ciwo, Sadiq yayi yinkurin mikewa, amma akan ya cutura, Hatake jiri suka dibe shi, ya fadi sumamme. Wallahi Baku ga komai bah, saina azabtar daku, irin azabar da ko da sunan ku baza ku iya tunawa bah. Fatima dake d'ad'aure, tace Karima, ki dakata aka, kin ruga da kin azabtar da ahalin nan, ya isa aka, Dan Allah, kiyi hakuri, ki yafe Duk abunda akayi miki, koh Allah munayi masa laifi yana yafe mane, bare Kuma mutum Dan Adam. Mom tace, ni kuma Banida zuciyar yafiya, bana yafe Duk abunda mutum yayi mun, kamar yadda na fada tun farko, dole saina kawo karshen wannan ahalin tukunan zan samu sukuni. Doct khadija tace, Karima why, shekaru kenen kina gallaza wa wannan ahalin Ba tareda kowa yasani bah, aka kika rabani da ahalina kikamin sharri akan abunda ban aikata bah kika ce nayi, mene kuma ya rage, muguntar ta isa aka, kodan kinga baki samu wacce zata taka miki Burki bah, Toh ni inada wacce zata taka miki Burki, wallahi, saikin gana wa aya zakinta. Mom tace

Table of Contents

Chapters

89 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});