Chapter 82
Chapter 82
ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ ALJANAR 🧜♀️ RUWA CE🌊🌊 PAGE 5️⃣5️⃣▶️5️⃣6️⃣ WRITTEN & DIRECTED ✍️ BY AISHA M.B💞💞 (Zinariyar 🪙 Jajirtattu) -------------------------------------- Gurnani Amriya ta fara yi!, cikin kankanin lokaci, halittar ta ya fara sauya wa, yayin da idanuwan ta ya sauya launi. Babu bata lokaci tayi kan Mom, ba tayi wata _wata bah, ta shake mata wuya tare da daga ta sama. Da sauri su Yusuf suka nufi inda Doct Khadija ke a yashe, kuka ne yaci karfin Yusuf ganin cewa tabbas mahaifiyar shi ta rasu. rungume ta yayi tare da fashe wa da kuka. A fusa ce! su Nadira da kuma su Grandma suka yi kam Mom da Zainab, yayin da su Kabir suka nufi inda su Mom suke sannan suka dauke Hydar. Kama Zainab suka yi, yayin da suka rufe ta da duka, sosai suke jibgar ta babu gaggautawa... Kokawa suka shiga yi a tsakanin su, inda Amriya tayi nasaran buga kan Mom akan jibgegiyar bishiya dake zaman kanta acikin wannan dajin. Wani irin kara Mom ta saki!, yayin da ta fara ihuun ceton rai!, ba babu tausaya wa Amriya ta kara yowa kanta sannan ta daga ta sama, kakari Mom ta shiga yi yayin da idanuwan ta suka yi jajir saboda shaka. Rintse idanuwan ta Amriya tayi, sannan ta zalalo harshen ta Wanda yake dauke da mugun dafi, ganin aka yasa jikin Mom ya fara bari,ta fara rokon Amriya ta barta da ranta. Cike da bakin ciki da takaici Amriya tace, "menene abinda wannan baiwar Allah ta aikata miki da zaki kashe ta?, "wana laifi ta yi miki, "me yasa ni baki kashe ni bah, saki rabu da ita," bayan kin raba ta da ɗanta tsawon waɗan nan shekaru, shine yanzu zaki kashe ta. Hada hannayen ta Mom tayi jiki na kakkarwa tace, ki gafarce ni, dan Allah kada ki kashe ni, ina bukatar na rayu, nayi miki alkawari zan chanza hali na, ki taimaka ki rabu dani, wallahi inajin radadi sosai Rintse idanuwan ta Amriya tayi hawaye na bin kan kincin ta tace, "Allah sarki Ummi, aka ta dunga rokan ki ki barta da ranta, amma sabo da rashin imani irin naki kika kashe ta, idan har kina jin radadi a matsayin ki wanda kika dade kina aikata zunubi kina kashe rai, toh kiyi tunanin irin radadin da waɗan nan bayin Allah da kika kashe za su ji". Kuma babban kuskuren da kika yi shine bari na da kika yi a raye, kuskure na biyu da kika yi shine kashe Doct Khadija da kika yi, yanzu lokaci yayi don gurban abubuwan da kika shuka. Amriya na kaiwa nan, ta dauki Wuka za ta chaka wa Mom, ba zato ba tsanmani taji an rike mata hannun ta baya, waigawa Amriya tayi don ganin wanenen. Da mamakin ta kuwa, taga Fatima da kuma Ammi gaba daya fuskokin su yayi shaɓe- shaɓe da hawaye. Cikin sheshekar kuka Fatima tace, "Ki rabu da ita Amriya, koba komai itadin mahaifiyar mu ce, ta sanadiyar ta muka zo duniya. Ammi tace kwarai kuwa Amriya", koba komai ita ɗin yar uwa tace ta jini, bayan ita juran ganin za'a kashe ta bah, Please Amriya ki rabu da ita, Ammi ta fada tare da hade hannayen ta guri guda". Hawaye masu zafi ne ke saukowa daga kan kuncin Amriya, daga bisani ta hajiye Mom sannan ta wurgar da wukan. Sannan ta kalli Mom tace, Kalla ki gani, mutanen da kika dade kina kuntata musu, amma sabo da imani da kuma tausayi wanda yake tattatare dasu suka ce na barki, kije na barki da ranki, Allah kuma zai saka wa mutanen da kika kashe, saboda mugan ci irin naki. Tana kaiwa nan, tabar wajan Mom, Mom na ganin aka tayi saurin daukar wukar da Amriya ta yar, sannan ta nufi kan Amriya za ta chaka mata. Kabir na ganin aka ya nufi wajan da gudu, yayin da yayi saurin janyo Amriya jikin sa, ya juya bayan sa, Mom na ganin aka ta chaka wa kabir wukan. Wani azababban kara Kabir ya saki!, zaro idanuwan gaba daya suka yi, yayin da suka saka ihuu!, a fusa ce suka nufi kan Mom, "Mom na ganin sunyo kanta, tayi saurin daukan zoben Amriya sannan ta fada a katuwar teku dake cikin dajin, wanda samm ba'a ganin karshen ta. Sannan ta kwashe da dariya, Ba zato, ba tsanmani, taga kowane halitta na cikin ruwan na yoo wa kanta, yayin da su Aljanun ruwan suka yi kanta a fusa ce!, zaro ido tayi, sannan ta saki ihuun ceton rai, amma me karfin tayi wani yinkuri, suka janye ta cikin ruwan. Ganin akan yasa kowanen su yin hamdalah cewa ta mutu kenen. faduwa Kabir yayi yayin da jini ya fara ƙetowa ta jikin sa. Jijjigashi Amriya ta soma yi hawaye na bin kan kuncin ta, Aa Kabir zan ceci rayuwar ka bazan bari ka mutu bah, kada kayi min aka. Kuka ne yaci karfin kowannen su, yayin da suna ji, suna gani, sun kasa cetan Kabir. Kallon Amriya Kabir yayi yace, me kika ce, yau Karo na farko da kika Ambaci cikakken sunana, tabbbas ina matukar farin ciki da faruwan aka, ki taimaka ki yafe min Amriya, wannan azabtuwar da nayi ma kadai sun isa, ban ki na mutu bah, indai harke zaki rayu, farin ciki na shine na ganki cikin koshin lafiya, ba tareda wani abu na cutar wa ya same ki bah. Aa Kabir ni na yafe maka duniya da lahira, ina matukar sonka Kabir, bazan iya rayuwa ba babu kai. Ina zuwa yanzu zan yi maka magani, Tana kaiwa nan ta mike tsaye, sannan ta shiga cikin bishiyoyin dajin ta fara tsinko ganyayyaki, sannan ta komai gare su, murza ganyayyaki 'n tayi sannan ta hade su guri guda, sannan ta dora a wajan ciwon, cije leɓen sa yayi, yayin da yake jin wani zugi da raɗaɗin a ciwon. Dora leɓen ta Amriya tayi kan nasa, sannan ta fara zuba masa dafi,a hankali Kabir yake jin zugin da raɗaɗin na raguwa. Saida Amriya tatabbatar ciwon yadai na mai zafi sannan ta cire leɓen ta daga nasa. Yayin da ta fara jin jiri na diban ta, dishi-dishi ta fara gani, Babu shiri ta fadi a wajan wajan, yayin da numfashin ta fara sama-sama. Hankalin gaba dayan su ba Karamin tashi yayi bah, ganin Amriya cikin mummunan yana yi. Da sauri Kabir ya nufi Inda Amriya take, ganin idanuwan ta sun komai jajir, yayin da bakin ta ya fara kakkarwa. Kallon su Aunty Amarya tayi tace, " Kabir ya kama ta mu nemo zoben nan, lokaci yana dada kurewa, share hawayen sa Kabir yayi, sannan ya girgiza kai yace shikenen, zan shiga cikin wannan ruwan sannan na dauko zoben. "Aa Kabir wannan tekun yana da matukar hatsari sosai, zaka iya illata, kuma sannan kai baka iya ruwa bah, zaka iya samun matsala, cewar Ammi". Kabir yace," ban da mu ba, Koda zan rasa raina, mundin indai zan samu zoben nan toh komai ya wadatar". Aunty Amarya tace, inda wani hajiyayyen ƙwai, Wanda malan Haruna ya taba bani idan ina son kowane Karfi koh wani abu ya lalace, indai na fasa shi a gefen Wanda nake son
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89