Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 61

Chapter 61

Aljanar ruwa Ce Book 1 Complete Hausa Novel 1,194 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

fadan irin wannan magannanun, koh kunya baki ji bah, toh maza maza koh wa ya watse kafun na bata muku rai. Kwan kwasa kofan gidan, doct khadija tayi, tashi daya daga cikin body guard din yayi, yanufi wajan gate din Tareda bude kofan, ganin doct khadija ne, ya sashi yin sauri ya bude kofan. Shiga ciki doct khadija tayi, Ta Kalli koh ina na harabar gidan, sa'anan ta girgiza kanta tace, shekara da shekaru kenen, rabon da na dora kafana akan wannan gidan, wacce tayi sanadiyan barina gida nan, itace takuma yin sanadiyan dawowa ta, yau bah gobe bah, kowa zai San abunda kika shuka Karima. Chan cikin gidan ta nufa Tareda Kwankwasa kofan parlour, Aunty amarya tace Grandma kamar naji Hana Kwankwasa kofa, barana je na bude kofan. Bude kofan Aunty Amarya tayi, taga bakuwar fuska, gaisheta Aunty amarya tayi, doct khadija ta amsa , sannan doct khadija tace, Karima na nan kuwa?, Aunty amarya tace Eh Tana nan, shigo Shigowa ciki doct khadija tayi, kamar ance Mom ta juya , Juyowa Mom tayi ,lokaci daya suka hada ido da doct khadija. Gaban Mom ne yayi mumunan faduwa! , yayinda zuciyar ta ya fara Duka uku uku, Murmushi doct khadija tayi tace, kina mamaki ne, Kinga ban mutu bah koh, bakici galaba akaina bah, Cikin fusata, Dad yace meya dawo dake gidan nan, bayan bakin ciki da kuncin da kika sanya mu aciki, wato Kara dawowa kikayi domin ki kara, saka mu a wani kuncin kamar yadda kikayi shekarun baya da ya wuce. Maza zo ki futa, Bamua bukatar, ma Yaudariya, maciya amana, Grandma tace Muhammad barta tukunan, ni zanyi maganin ta Ke khadija, kalle ni nan, Kallon ta doct khadija tayi, Grandma tace kalle ni da kyau, baka nake bah fara nake bah, wato Kara dawowa kike, domin kikara haddasa wani fituna koh, toh ta Allah ba taki bah, baki isa kin kara yiwa wannan ahalin komai bah, Dan aka maza ki fuce, kafun na dauko tabarya, hawaye nee suka Fara saukowa daga kuncin doct khadija tace, bazan ga lafin ku bah, laifin wacce ta hada mu daku, zan gani, nazo gidanan ne badan komai, bah sai Dan na tona asirin abunda Baku sani bah, na tsawon shekara da shekaru, inason ku bani Dama, Dan Allah zan fada muku gaskiyar abunda ya faru, Kallon Dad doct khadija tayi tace, tabbas abunda Amriya ta fada muku gaskiya ne, babu karya, first wife dinka , wato Fatima Tana raye bata mutu bah, Kuma tana kulle ne acikin wannan gidan na tsawon shekaru, batareda ansani bah, Amriya ce kawai ta iya gano, inda Matarka take. Kallon ta Dad yayi, yace Dama wanda ya ruga ya rasu yana dawowa ne, wato zuwa kikayi domin ki cusa mun bakin ciki a zuciyata koh, leave now, banason jin komai dazai futo daga bakin ki. Doct khadija tace, zan tafi, amma bazan bar gidanan Ba Tareda na tona asirin wannan shedaniyar bah. COMMENT & SHARE PLS ALAKALAMIN AISHA M.B(BABY ISHA) BISSMILLAHI RAHAMANI RAHEEM. ALJANAR RUWA CE PAGE 46 ?47 WRITTEN & DIRECTED BY AISHA M.B (BABY ISHA) ----------------------------------------- Murmushin k'eta Mom tasaki sa'anan tace, Yanzu khadija wane laifi na aikata da kike son wargaza gidana, mene na aikata miki? Wane abu na tsare miki a rayuwar ki . Meyasa kike son ganin baya na ta karfi da yaji, Grandma tace, Karima ki rabudani ita, so take ta lalata miki aure, toh ta Allah na Tata bah, maza zoki futa kafun na sakar miki karnukan gidanan, suyi hawan gaba da ke. Wani kukan bakin ciki ne ya ziyarci Doctor Khadija, doct khadija tace, ku yarda dani wannan matar shedaniya. Mom tace DAD Kabeer Dan Allah ka roke ta, ta bar mana gida, saboda wannan matar munafuka ce. kece dai babbar munafuka!" sukaji kalisat tafada! ,ta cigaba da fadin kwarai kuwa, kece munafukar, Tsinka mata mari doct khadija tayi tace, Duk abunda zai faru, karki kuskure kikara ce mata munafuka, saboda a haifa ta haifi sama dake. Kuma itadin a matsayin mahaifiyar ki take. Allah ya kiyaye, Allah ya mun katangar karfe da wannan shedaniyar algunguma, mara imani. Wannan matar bata cancan ci akirata da Kalman uwa bah, domin kuwa yin akan kuskure ne. Dad yace, ke Kalisat," kinsan abunda kike fada kuwa, kina da hankali, bakisan cewar, Tana a matsayin mahaifiyar ki bane, ya karashe maganar ranshi a matukar bace kalisat tace, Dad am sorry to say", gaskiya, ita ba'a matsayin mahaiyata take bah, saboda mahaifiyata ta fita daraja da kima, kuma ita wannan azzaluma ce, mara zuciyar tausayi. Magannanun tane suka sauka akan dodon kunuwan Khalid dakuma su Kabir dake sauk'owa daga upstairs, bata hankara bah taji sauk'an mari akan kuncinta, Dafe kuncinta kalisat tayi, Idan ran Khalid ya Kai dubu toh ya baci, yace kalisat, kina cikin hayyacin ki kuwa, wacce ta raine mu, ta kula damu tamkar yaran ta, ta nuna mana soyayya kamar yadda itama Mami iya karkarin abunda zata iya kenen, shine yau kike kallon tsabagen Idanuwanta kina fada mata magana son ranki, kamar itadin sa'ar kice. Kalisat tace wallahi matar nan, bata son mu Illah son cutar da mu da take kokarin yi, Amriya ce kawai take dakatar da ita, amma na tunan ta gama da yahya kabeer ya kashe kowa na wannan family. Fashewa Mom tayi da kuka!, tace, Yau a gaban idona ake min karya cewar ina kokarin cutar da ahalin nan, meyasa zanyi muku aka, kalisat. Duda irin alkhairy da nayi muku amma da irin wannan abun zaku saka min dashi Dama ance Dan adam butulu ne, Hatake ta Fara tarin karya, tana zubda hawaye Hakuri su Kabir da Dad suka Shiga bata, cikin fusata Kabir ya nufi inda kalisat ke tsaye, Ba tareda bata lokaci bah ya fuzgo ta, sa'anan ya shake mata wuya yace, ke mahaifiyata sa'ar ki ce, wallahi Kuma idan wani abu yasami mahaifiyata saikin dandana kudarki, Murmushi kalisat tayi tace, mahaiyar ka, ko mahaifiya yar basaja, ta dolantar daku, tasaka ku cikin duhu, babu abunda idanuwan ku ke gani sai duhu, Amriya tayi kokarin fidda ku cikin aske, amma kuka ki ku fahimce tah. Da wacce kake Kira mahaiyar na sonka baza tayi kokarin cutar da rayuwar ka bah, idan akane meyasa ta kashe Ummi. Da sauri Kabir ya sake ta, ya dago da idanuwansa wanda suka kad'a sukayi ja. yace, what nonsense are you talking about. Kalisat tace am not saying nonsense, amma ni nasan tabbas Mom itace ta kashe Ummi, kuma sa'anan ta batar da Salma. Gabadaya suka hada Baki wajan fadin what! Dad yace toh menene hujjar ki na fadin akan, gayamin Wacece hujja. Nice hujja . Sukaji an fada, juyawar su keda wuya suka ga, Salma duk ta bi ta rame, tayi baki. Da sauri su nadira sukaje suka rungume ta, fashewa Salma tayi da matsanan cin kuka mai taba zuciya. Nadira tace, Salma Wacece tayi miki aka, ina kikaje cikin wadanan kwana kin, ba Tareda kin dawo bah, Salma tace babu inda naje, asali mah Mom ita ta bayar dani, ba Tareda kowa ya sani bah, kuma tabbas itace makashiya, wacce ta raba Ummi da rayuwar ta, saboda son kanta da son abun duniya. Dafa kanshi Kabir yayi Wanda yake mugun saramai, Kallon Mom wacce tayi zuru

Table of Contents

Chapters

89 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});