Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 81

Chapter 81

Aljanar ruwa Ce Book 1 Complete Hausa Novel 1,218 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

dan darajar ma'aikin Allah, idan kina kaunar mahafin mu da gaske, toh dan Allah ki bamu zoben nan, dan Allah . Dan Allah ki bamu, we don't have much time, and we need to rescue Amriya's life. Dan jimm Mom tayi, kamar tana tunanin wani abu, lokaci daya kawai suka ga ta zari zoben ta mika wa Ammi", Da Kallon mamaki kowa ke binta dashi, ganin babu musu ta miko zoben, share hawayen ta Ammi tayi tace, kin yarda na karba?, Girgiza mata kai Mom tayi tace, kwarai kuwa na yarda, Amma da sharadi duk abinda na tambaye ku shi zaku bani, Mike wa Ammi tayi tace, munyi miki alƙawarin duk abinda kika ce kina so zamu baki, murmushin mugun ta Mom tayi, tare da fadin, tom shikenen ku karbi zoben ku tafi. Karbar zoben Ammi tayi daga hannun Mom, ta kalli Doct Khadija tace, yanzu a ina zamu fara neman Amriya "Khadija?, Doct Khadija ta bata amsa da fadin ba zai wuce guri daya bah, ni nasani wajan, inda muka fara haduwa da ita, hanan tace min burin ta, shine ta mutu a chan, yanzu ina da tabbacin cewa tana chan. Yusuf yace, Togo me muke jira, mu tafi kafun lokaci ya kure. Nufar hanyar waje gaba daya suka yi, yayin da kowannen su ya shiga mota, tare da tada motocin, suka fuce daga gidan..... Ana Karima, ta yaya zaki basu wannan zoben, meyasa zaki barsu su tafi?, cewar Zainab, amsa Mom ta bata da fadin, ni kadai nasan abinda nake shirya wa, ke an gaya miki cewa na yafe musu ne, ina sane na bada zoben, sobada abinda zan tambaya saiya ninka na zoben, ni bana ya fiya, fansa ce kawai take guda na a jini na. Maza-maza ku tashi gaba daya, nuni bayan su, mimmike wa gaba daya suka yi, yayin da suke jin jikin su na musu radadi.. Fucewa suka yi daga harabar gidan, sannan suka bi bayan su Kabir. Saida su Kabir suka dau tsawon lokaci suna tafiya, daga bisani kuma suka isa wajan. Koh gama parking baiyi bah, ya futo daga cikin motan, tare da kallon gaba daya jejin. Futowa suma suka yi gaba-daya, yayin da suka fara kalle _kalle, Koh zasu gano Amriya. Parking su Mom suka yi, yayin da suka laɓe a bayan bishiya, Kiran sunan ta suka shiga yi, amma suka ji shiru, cikin karfafa gwiwa, suka cigaba da kiran sunan ta batare da sun sare bah. Sheshekar kukan tane yaja hankulan su baki daya, waigawa su kayi, yayin da suka ga ta zauna a bakin Kogi tayi rufff da ciki. Kabir na ganin aka yayi saurin nufar inda take, karasa wa wajan ta suma su kayi. Zama kusa da ita yayi, tare da ɗago haɓar ta, zaro ido yayi ganin yadda idanuwan ta suka yi jajir duk sun Ku kumbura, uwa uba kuma ta rame tayi baki. Baki na rawa Kabir yace, mene ne ya same ki?, meyasa kika tafi kika barni?, shin kin san irin halin da na shiga da kika tafi, na shiga wani yanayi na kunci da bakin ciki, na roke ki kiya femin kurakurai na, bazan iya rayuwa ba babu ke. Dago kanta Amriya tayi hawaye na sauka kan kuncin ta, sannan ta dora idanuwan ta akan nass, daga bisani ta dauke kanta, tareda maida Kallon ta kan su Ammi. zuwa Ammi tayi kusa da ita, tareda tsugunnawa ta rungume Amriya, sannan ta fashe da kuka!", tana mai fadin, ki gafar ce ni ƴata, tsawon wadanan shekarun bansan cewa kina raye bah, tabbas ban miki adalci bah, na baki dama ki yanke hukunci daidai da laifin dana aikata miki. Rintse idanuwan ta Amriya tayi, yayin da take jin zuciyar ta na mata zugi da radadi, ɓanɓare jikin ta tayi daga na Ammi, Tare da mikewa tsaye, ta maida kallon ta kansu tace, mene ne ya kawo ku?, me kuke nema a gare ni?, Doct Khadija tace, Amriya mun zone domin mu baki zoben ki kada ki mutu, share hawayen ta Amriya tayi tace, shin nace muku ina bukata ne?, banaso ku rike shi a wajan ku, saida lokaci ya kure tukunan zaku kawo min zobe, Togo bana bukatar na cigaba da rayuwa, ku tafi ku kyale ni, Khalid yace, aba Amriya ke kinsan baza mu taba iya tafiya mu barki bah, ki taimaka ki karbi zoben nan, kafin lokaci ya kure. Tafi suka ji daga bayan su, juyawa gaba daya suka yi domin ganin waye, da mamakin su kuwa suka ga Mom rike da Hydar a hannun ta. Cikin baccin rai Ammi tace, Karima mene aka?, ya zaki dauki jaririn, dariya Mom da Zainab suka kwashe dashi!", sannan Mom tace, wannan yaron shi nake so, kamar yadda na fada idan zan baku zobe saina tambayi wani abu, toh jinin wannan yaron nake sonsha. Karya kike!",Amriya ta fada a tsawa ce!, Jinin ɗana bazai shawu bah, domin kuwa ɗaci gare shi, maza_maza ki bani yaro na, in bah aka bah na lahira sai ya fiki jin dadi. Dariya gaba daya yan qungiyan suka kwashe dashi, yayin Zainab tace, Togo zaki karbe shi mana idan zaki iya, kallon yan qungiyan Mom tayi sannan tace, maza yanzu nan ku kashe su gaba daya. Tana kaiwa nan, gaba dayan su suka yi kansu Kabir hannuwan su rike da wuka da takobi, Fada gaba-daya ne ya gauraye wajan, yayin da suka fara fada a tsakanin su ba gaggau tawa. Rintse idanuwan ta Amriya tayi, yayin da ta fasa wani kara!, wanda saida gaba daya dajin ya amsa. Sa'annan tayi amfani da karfin ikon ta, ta fara sama dasu daya bayan daya, tana wurgasu jikin manya_manyan duwatsuna da bishiya, hatake gaba daya kowanne su yake faduwa mutacce. Saida Amriya ta gama dasu tass yayin da ya rage saura Mom da kuma Zainab, ganin AMRIYA na yowa kansu yasa Mom ta cilla jaririn sama, zaro idanuwa gaba daya suka yi cikin tsoro, Amriya na gannin aka tsalle daya tayi ta chafko yaron. Kuka jaririn ya fashe dashi, rarrashin shi Amriya ta shiga yi, yayin da ta mikawa Salma jaririn. Ganin hankulan su nakan Amriya, yasa Mom yin saurin janyo Doct Khadija, sannan ta dora mata wuka a wuya tace, zan kashe ta idan baku bani jaririn nan bah. Maida kallon su suka yi kan Mom, zaro idanuwa suka yi ganin yadda ta dora wuka kan wuyar Doct Khadija, Haɗa hannun ta Amriya tayi, sannan tace dan Allah kada ki cutar da ita, na roke ki. Mom tace indai har bakua so na cutar da ita, toh ku bani wannan jaririn. Kallon su Doct Khadija tayi tace, Aa Amriya karku kuskure ku bata wannan yaron, ni na yarda na mutu, Amma karku bayar, . Zan yanka ta fa idan baku bani yaron nan bah, Cewar Mom. girgiza kai Amriya tayi tace A'a, Aa, karki kashe ta, Dariya Mom tayi tace toh ai shikenen, tana kaiwa nan ta yanka wuyan Doct Khadija. Aaaaaaaaaa!", Amriya ta saki wani razananniyar kara, wanda yasa hadari da walkiya wanzuwa, faduwa Doct Khadija tayi a wajan, kafin kace mee rai yayi halin sa... COMMENT & SHARE PLS🙏🙏 ALKALAMIN✍️ A'ISHA M.B💞💞💞 (Zinariyar 🪙 Jajirtattu) Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JYYV16dbYaX1dykLX7EE9https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa

Table of Contents

Chapters

89 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});