Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 77

Chapter 77

Aljanar ruwa Ce Book 1 Complete Hausa Novel 1,215 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

inda kuka je?, Tun daga abunda ya faru har karshe Khalid ya zayyane musu. Jinjina kai kawai Doct Khadija tayi, sannan tace shikenen abunda nake gudu shi yake shirin faruwa, Kallon ta Aunty amarya tayi tace, menene yake shirin faruwa Khadija?, Kafin Doct Khadija ta bawa Aunty amarya amsa, wata nurse ta futo daga daga room din, Ganin nurse din yasa dukkan su mikewa, sannan suka ce ya jikin nasa?, Nurse ta basu amsa da cewa alhamdulilah mun samu ya farfado, amma munji yana kiran sunan wata wai Amriya, da alamun itadin wata ce a rayuwar sa. kuma bincike ya nuna cewa yana saka tunani a ranshi sosai, kuma yana yawan shiga damuwa akan wani abu, a gaskiya kuma ya kamata ace idan kuna da abun kuyi gaggawar bashi, in bah aka bah, wannan abun zai iya affecting kwakwal war sa. Gaban kowannen sune ya fadi, yayin da kowa ya rasa ta cewa, Yusuf ne yayi karfin halin fadin shikenen insha Allah zamu bashi duk abinda yake bukata, shin yanzu zamu iya shiga mugan sa?. Yes of course Why not, zaku iya shiga, amma dan Allah banda haya niya, domin mara lafiya yana bukatar hutu, zaku iya shiga, yanzu zanje pharmacy ne domin siyo maganin da doctor yayi prescribing za'a bashi, tana kaiwa nan ta fuce daga wajan. Cikin room din suka shiga, inda suka tarar da kabir sai zubda hawaye yake, gefe guda kuma sunan Amriya kawai yake kira. Tausayi sane yaka masu, tabbas so yayi wa Kabir mugun kamu. Kallon sa suka yi, yayin da suka ji yana fadin. Ki dawo rayuwa ta, zan baki kulawar da baki taba tsammani bah, kada ki gujeni, domin idan kika barni zan shiga wani hali, sonki a raina ya riga daya zama dashashe, wanda babu wanda ya isa ya iya cire sonki a raina, Please Amriya, i need you, i want you to stay with me for the rest of my life, dan Allah ki bani last chance, Ya karashe maganar hawaye nabin gefen fuskan shi. Zuwa Mommy tayi daff dashi sannan ta rungume sa, tare da fashe wa da kuka, kuka sauran yan dakin suka fashe dashi, yayin da aka rasa mai rarrashin wani. Jin koke-koke, yayi yawa a dakin yasa su doctor's saurin nufa dakin, tarar dasu suka yi kowannen su na kuka. Gyaran murya daya daga cikin doctor's din yayi yace, aba dan Allah, wannan mara lafiya fah muna tunanin zaku tafi dashi gida,saboda jikin shi yayi kwari sosai, amma dubi yadda kuka sashi a gaba, yana kuka kuma nayi , an rasa mai rarrashin wani acikin ku, Please ku futo. Futa gaba daya suka yi daga cikin dakin, bayan hours aka sallame su daga asibityn, bayan sati daya, jikin Kabir yayi sauki sosai,kamar bashi bah, Amma har yanzu bai daina tunanin Amriya bah. Inda gefe guda kuma aka saka auren Khadija kanwar sadiq da kuma A'isha, sosai aka sha shagalin aure, akayi buki na buga wa a jarida, babu wanda bai halarci bikin bah, amma duda akan babu walwala a fuskokin su, Bayan nan aka kaisu gidan mazajen su, inda Doct Khadija, da kuma Mommy sukayi musu nasiha mai ratsa zuciya. ,tsaknin amare da mahaifyar amare wato hajara, suka dunga kukan rabuwa, da kyar aka kwace hajara daga hannun su, sannan suka bar gidan su amare, kowa ya koma gidajen sa....... .BAYAN WATANNI BIYAR. nakuda take ba gaggau tawa, yayin da take jin marar ta nayi mata radadi da ciwo, rintse idanuwan ta tayi, hawaye na bin kan kuncin ta. Ba zato taji marar ta ya rike, ihuu! ta fasa wanda ya gauraye gaba daya ilahirin dajin. hatake kowane halitta na ruwa ya fara fito wa, suna nufan inda take, yayin da aljanun ruwa da kuma yan ruwa suka fara zagaye ta, suna shafar cikin ta, wani karan! ta kuma fasawa, Gaba daya ta jigata, yayin da numfashi ta ya fara sarke wa, huxu ta fara yi, inda gumi ya fara keto mata, Shafa kan Amriya daya daga cikin aljanun ruwa tayi, sannan ta fara hura mata iska ajiki, yayin Da gefe guda wata Aljanar ruwaye ta fara tura cikin dan tayi nasaran haifi ?an cikin nata. Danna Cikin Aljanar ruwar tayi, hatake Amriya ta fasa wani irin razanannen kara, wanda yasa aka soma iska mai mugun karfi, Numfashin tane ya fara kasa, inda daga karshe tayi nasaran numfashi wanda yasa santalele jariri fadowa. Hatake kukan jaririn ya gauraye dajin, kwanciyar Amriya tayi tana saukar da hajiyan zuciya. ??♀???♀???♀???♀???♀???♀???♀???♀????????????????? COMMENT & SHARE PLS??? ALKALAMIN?????? A'ISHA M.B??? (Baby Isha) Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JYYV16dbYaX1dykLX7EE91 https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ 🌹BISSMILLAH RAHMANI RAHIM🌹 ALJANAR RUWA CE 🧜♀️🌊🌊 PAGE 5️⃣3️⃣▶️5️⃣4️⃣ WRITTEN & DIRECTED✍️ A'ISHA M.B 💞💞 (Zinariyar 🪙 Jajirtattu) ----------------------------------------- Farin ciki ne ya bai baye fuskokin aljanun ruwan, hajiye jaririn suka yi kusa da Amriya, sannan suka yi tafiyar su. Maida kallon ta Amriya tayi kan jaririn, abunda ta gani ne yayi matukar bata mamaki, ganin yaron tayi kafan mutane ne ajikin sa bana Aljanun ruwa bah. Shafa kafar tayi, wanda suke farare gwanin ban sha'awa, share hawaye ta tayi, sannan ta mike, ta nufi bakin Kogi domin ta kimtsa jikin ta da kuma na yaron, Saka yaron tayi cikin ruwa, amma ga mamakin ta, taga bai sauya daga jinsi mutane bah, Kallon shi tayi tace me akan yake nufi?, meyasa bai koma aljanin ruwa bah?, tunda ni ALJANAR RUWA CE, kama ta ai ace danda zan haifa ya zama irina, amma meyasa kaikuma baka zamo kamar ni bah. Wani tunani ne ya fado mata akai, kenan akan yana nufin jinsin mahaifin sa yayo kenen, toh tayaya akan zata kasance,. Murmushi wanda yafi kuka ciwo tayi, sannan tace, kada ka damu Allah shine abin dogaro. Tana kaiwa nan, tayi masa wanka, sannan itama ta gyara jikin ta wanda ya baci da jini, Tana gama wa, ta mike sannan ta hajiye yaron, ta fara tsinto kara tana hadawa guri guda, Sai data gama har hada karan, sannan ta hura masa wuta da bakin ta, babu bata lokaci ta fara gasa wa yaron cibiyar sa, kukan yaron ne gaba daya ya karade dajin, daukan placenta tayi wato mahaifa, sannan ta tona rami ta bunne shi. Bayan ta gama bunnen placenta, ta dauki jaririn, sannan ta nufi wajan bishiya ta tsinki ganye, ta saka shi acikin ganyen. Ƙare mai kallo tayi taga sakk kamar mahafin sa, kamar harta baci, shafa sajen yaron tayi wanda suka kwanta suka yi luff, tace kyakkyawan yaro na, ni na kusan tafiya na barka, zanyi kewar ka soaai dana, ina fatan koda kaji labari na a wajan mahaifin ka, kada ka taba manta wa dani kaji. Kallon sama tayi taga rana ta fadi, hawaye taji na shirin zubo mata, da sauri ta share hawayen ta, sannan tace, ranar da na dade ina jira yau gashi tazo, yau zan tafi na barku baki daya, zan kaika wajan Ammi, uwa ta gari, na tabbatar kulawar da zan iya baka, shi itama zata baka, zaka samu farin ciki da kulawa mara misaltuwa. Mike wa tayi, yayin da yaron keta faman kuka, rarrashin shi

Table of Contents

Chapters

89 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});