Chapter 59
Chapter 59
tayi tace, Eh wallahi, hayyuka ne suka min yawa shiyasa kika ga bana zuwa office. doct Amina tace wa nake gani aka kamar Amriya, gaishe ta Amriya tayi, amsawa doct Amina tayi da fadin lafiya kalau y'ata, ya mijin naki, da fatan yana cikin koshin lafiya. Sosa Kai doct khadija tayi tace yana lafiya, Tareda fadin Amina inason mudanyi wata magana dake a sirrince, doct Amina tace, okay bah Damuwa, Kallon Amriya doct khadija tayi tace Amriya ki shiga daki kinji, Tom Amriya ta tace tareda mikewa tsaye, ta nufi cikin guest room. komai da komai, daya faru doct khadija ta zayyane wa doct Amina, amma doct khadija bata ce mata Amriya ALJANAR RUWA CE bah. Girgiza Kai Doct Amina tayi tace, Dan Adam ba'a iya masa, babu komI kawa ta, zan kular miki da ita har Dan cikin ta, kada kidamu itama ai tamkar y'ata take. godiya doct khadija tayi wa Doct Amina, doct Amina tace Aba kawa tah ai a tsakanin mu babu godiya. tashi doct khadija tayi tace, shikenen ni zan tafi, inaso zan kai wa yan uwana ziyara, shikenen toh Allah ya kaiki lafiya cewar doct Amina, amma shin bazaki tsaya kici breakfast bah, Aa wlh na koshi. saina dawo tana kaiwa nan doct khadija tayi fucewar tah. bayan fucewar doct khadija, doct Amina taTaShiga dakin da Amirya ta Shiga, Amriya na ganin ta ta Mike, Aa y'ata zauna mana cewar doct Amina. me kike so kici zan dafa miki, Girgiza kanta Amriya tayi tace na koshi, wannan Kuma bazai yuwu bah, babu abunda kika ci fah amma shine kike cewa kin koshi, toh ki taso akwai abinci akan dining kitawo muje muci koh, sannan na baki magunguna kisha. Amriya tace Aa na koshi, banajin yunwa, doct Amina tace toh shikenen nima bazan ci abinci bah,kowa ya zauna aka. murmushi Amriya tayi hawaye na son zubo mata Saurin share su tayi tace shikenen, Doct Amina muje zanci .murmushin jin dadi doct Amina tayi tace Yauwa y'ata ko ke fah, taso muje koh, bayan mungama cin abinci zan ce da babban dana yusuf ya kaiki shopping kiyi siyayya ,shima kidauke shi tamkar yayan ki kinji . tashi sukayi suka nufi dining, inda suka tarar Abban yusuf da yusuf na Zaune, da alama su suke jira. serving dinsu doct Amina tayi ,inda itama taja gefe ta ibi nata, suka Fara ci. oh my God sir Kabir ne yau a gidan mu, Kuma wai yazo hira wajena, Tsaki Kabir yaja, yayi murmushin takaici yace, ke ni yanzu zan tafi, idan na tafi ki kira Mom kice mata bakya sona bazaki iya aurena, bah inba aka ranki ya baci. zainab tace Aba masoyi yaushe kazo, da har zaka tafi, shikenen zan fada mata amma Dan Allah inason ka kaini shopping, yau ranar fah masoya nee Valentine day, ya Kama ta ace ka bani babbar kyauta, toh nida ke naga Ba soyayya muke, bah Dan aka, ki kiyaye ni kinsan ni bah tsarar ki bane wallahi, aba sir Kabir please, and please, Dan Allah, ke naji shikenen, zan jiraki a waje, wlh idan baki futo bah nan da 20second, tafiya zanyi, Dan bazai yu nazama, bawan ki bah tohh. yana kaiwa nan yayi fucewar shi , Kai na rawa Zainab ta dauki gyale Dan karami wanda dashi gwanda babu. futowa tayi ta Tarar dashi yana shirin tafiya, Saurin daka tar dashi tayi sannan ta Shiga cikin motan, yabar harabar gidan. Yauwa Yusuf inason ka kaimin kanwar ka shopping, kaji, yusuf yace Ammi consider it done. ni naga shirya wa, ban dai sani koh kanwa ta taga ma shirya wa bah. Amriya tace ni a shirye nake, bayan sun gama cin abinci, yusuf ya dau mukullin mota yayi hanyar waje, hijabi, Ammi ta bawa Amriya, saka wa Amriya tayi ta bi bayan yusuf, bude mata gaban mota, Yusuf yayi ta Shiga. tareda barin harabar gidan. direct shopping mall, suka nufa, Daidai lokacin suma su kabir na isa wajan. bude wa Amriya kofa yusuf yayi , futowa Amriya tayi daga cikin motan suka nufi cikin mall din. Rike hannun kabir zainab tayi wafce hannun sa kabir yayi yace ,are you normal, kada ki karamin irin wannan abun in badan Mom bah Allah koh a matsayin yar aiki bazan iya daukan ki bah bare Kuma azo kan wai mata. hakuri zainab ta Bashi inda suka Shiga wajan mall din. inda ake saida kyaututuka suka nufa, gabadaya masoya sun cika wajan, kowa yana siyawa budurwarsa kyauta. saida su yusuf suka gama siyayya sa'an nan suka nufi wajan saida gift, Yusuf yace kan wata yau fah ranar masoya nee bazaki siya wa masoyinki kyauta bah, Amirya tace bani da masoyi. yusuf tace toh muje ni na siya miki saina baki kyauta a matsayinki na kanwata, Aa wallahi ka barshi, nagode, Yusuf yace no bazan yarda bah, wato kina k'in kyauta daga wajan yayan ki. wajan da ake saida Valentine Gift yusuf ya nufa da Amriya. wata kyauta Kabir ya dauko ya damka wa zainab, Cikeda farin ciki zainab ta rungume shi,a bai nan nasi. Daidai lokacin idanuwan Amriya suka sauka akan su Kabir. Cikeda bakin ciki da takaici, Amriya tajawo yusuf tace inason mubar nan wajan, Dan Allah, yusuf yace why? baki ga wasu masoya bah sun rungume juna, Dan aka kawai ki bari na siya miki. Saurin cire jikinshi kabir yayi daga na zainab yace, ke wace mahaukaciyar ce, taya zaki rungume ni a gaban jama'a. bakida hankali ne, kayi hakuri, kaji my love. Cikeda takaici Amriya ta dauke idanuwan ta daga kansu, ta Kalli yusuf tace, sweetheart, ni wannan nakeso tayi nuni da hannun ta,. da sauri kabir ya juyo jin kamar yasan wannan muryar, hada ido sukayi da Amriya Hatake gaban shi ya fadi. Amriya ta cigaba da fadin Sweet, wannan nake soo, yusuf yace kada kida mu, zan siya miki koma Wanne, wani irin kishi ne ya turnuke zuciyan Kabir, nufan inda suke yayi tareda Jan hannun Amriya yace, waya baka izinin futa da matar wani, kaidin waye ke Kuma ya fada yana Kallon Amriya, Dama Ashe ke yar iska ce, uban waye ya baki izinin futa da wani na mijin, Dama abunda ke faruwa kenen idan ka auri karuwa, Tasssss Amriya ta tsinka wa Kabir mari. zaro idanu jama'a wajan sukayi. nuna Kabir Amriya tayi da Dan yatsan ta tace... . COMMENT & SHARE PLS KUYI HKR JIYA KUNJI SHIRU WLH WAYANA NE YASAMU MATSALA, AMMA INSHA ALLAHU ZAN GYARA ALKALAMIN AISHA M.B ( BABY ISHA) BISSMILLAHI RAHAMANI RAHEEM ALJANAR RUWA CE PAGE 45&46 WRITTEN & DIRECTED BY AISHA M.B (BABY ISHA) --------------------------------------- Cikin baccin rai Amriya tace, har kai waye, Da zaka zo ka neman cimin zarafi agaban jama'a, shin na taba ganin ka ne ,koh kaidin mijina ne, da zaka zo kana ci min mutunci, Bansan ka bah, baka Sanin bah, toh ina ruwan ka dani, kazo da masoyiyar ka, nima nazo da nawa, shin akwai laifi ne aciki, toh ka sani, aure ce ta hada ni dakai , Kuma yanzu ta raba, Dan aka baka da iko akaina, baka San irin muguwar tsanan da nayi maka bah, tsanan da nayi maka koh ma'auni, bazai iya aunawa bah, Kuma kayi na farko, kayi na karshe. Kada koda gigi yasa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89