Chapter 64
Chapter 64
amma gaskiya sai an karamin lokaci, danni bah yaro bane bah, Ammi tace kaji dashi dai, ----------------------------- Cikin tsorata gabadaya suka juya don ganin wanene, juyawar su keda wuya suka ga Mom a tsaye ta dora wuka akan wuyan Fatima wato matar Dad, dayan hannunta kuma rike take da files, Gyaran murya tayi sa'anan tace kuna ji kuna gani zan kashe ta a gaban ku batareda kun ceci rayuwarta bah, Dafe zuciyarshi Dad yayi wanda yakeji tamkar zata fashe sabida kunci da takaici, Cillawa Dad document din hannunta mom tayi, tana mai fadin wannan itace kadarorin ka gabadaya, ka saka hannu, kasaka cewar wannan kadarar Ba taka bace ta Karima ce, in Kuma bah aka bah, kana gani zan kashe ta har lahira. Kallon Fatima Dad yayi wacce ta rintse idanuwan ta hawaye na zubowa kan kuncin ta, sannan yace dama Fatima kina a raye ban Sani bah, meyasa baki fadamin cewar kina raye bah Tsawon wadanan shekarun, kinsan wane Hali na Shiga tsawon wadanan shekarun da bakya tareda dani. Kallon shi Fatima tayi tace, Bah lafi na bane, danasan aka zata kasance daban saka rayuwar ku da d'ana a cikin hatsari bah. Aunty amarya tace bake kika saka rayuwar mu a hatsari bah, wannan shedaniyar matar ce, Cikeda baccin rai Mom tace kwarai kuwa, nice nan, Wato har kun manta abunda kuka aikata mu shekarun baya da suka gabata kenen, kun manta yadda kuka Shiga tsakanina da yar uwata kuka saka mu cikin kunci da bakin ciki, Dad yace wai waye yasa kaki kunci,shin nasan ki ne a da? Fadamana me muka aikata miki, Mom tace bani zaka tambaya bah mahaifin kah dake Kabari zaka tambaya, danshi yasan komai da komai da yafaru, abunda ya aikata shi yake shafar y'ay'an sa kuma gashi harda jikokin da yatara, Wato kun taru kuna cin Dukiya kuma kudin haram, kun taru kuna siyan tufafi abinci, yin abunda kuka gadama da kudin da ba naku bah , Kuma a akan kuke tunanin zan barku ku sha, akan bazata faruba, maza maza kasa hannu akan takardan nan in bah aka bah na yanka wuyan ta yanzu nan. Cikin fusata Dad yace bazan saka bah, Kuma baki isa kiji mata koda kwarzane ne, Murmushi mom tayi ta cilla mahaifiyar kabir gun Dad, babu bata lokaci Dad yayi Saurin riketa, Mom ta kallesu tace, na baka nan da 24hours, da zaka sa hannu akan files dinnan, in bah aka ba, toh na rantse da ubangijin da nake bautawa, gabadaya saina kona ku da ranku, karasa maganar ta keda wuya ta fuce daga cikin dak'in. Rungume Mahaifyar Kabir Dad yayi, yana mai fadin, ki gafarce ni Fatima, kiyi min aikin gafara, danasan kina raye kuma kina cikin gidanan, dana saka police sun kama Karima. Kiyi hakuri, murmushi Mahaifyar Kabir tayi tace, babu abunda ka aikata min, yanzu burina shine na sanya d'ana a cikin idona, ina d'ana yake, Nuna mata inda Kabeer ke kwance Dad yayi, Kallon wajan tayi, yayin da ta sauke idanuwanta akan kabeer, Wanda ke kwance har yanzu ba ya motsi. Tashi tayi da sauri tareda nufan inda yake, kuramasa idanu tayi hawaye na sauka kan kuncin ta, tace Allah sarki d'ana, wancan azzalumar matar ta rabani dakai, bata Bari naji dimin ka bah, ta dauke min Kai, yanzu bah lallai ka soni kamar yadda ka sota a baya bah. Tabbas yanada wuya ka iya yarda cewar ni asalin mahaifiyar ka ce, domin kuwa zaka kuma dauka ko wani raina mah hankali za'a kuma yi, tunda na haifo ka wannan duniyar baka taba ganina bah, bare ka kirani mama, ka taimaka ka kirani mahaifiyar ka koda sau daya ne kafun numfashi na na karshe, tana kaiwa nan ta fashe da kuka mai ratsa zuciya, Jikin gabadayan su ne yayi sanyi, yayin da su kaji tausayin ta ya matukar kamasu. Hawayen dake shirin zubowa Dad yayi Saurin sharewa, tareda fadin, kada kidamu Fatima" yanzu ai kin dawo rayuwar shi, tabbas nasan bazai guje ki bah, Kuma na tabbata zai rike ki hannu bibbiyu, Fatima tace da wuya ya yarda ni Mahaifyar sace, kasan yadda zuciya ta ke kuna da radadi, kasan yadda naji yayin da ina ji, ina gani, aka raba ni da dana daya tilo, shin meyasa bata dau raina bah ta barni a raye tana gallaza mun azaba, babu irin azabtarwar da bata yi min bah, tabbas laifi na ne, dana dora mata yarda ta, daban dora mata yarda ta ba, da bata aikata akan agareni bah. Cikin rashin fahimta Dad yace, kamar ya? Shin dama kin San tane tuntuni? Shiru Fatima tayi ba tareda ta bawa Dad amsa bah. Daga sama sukaji Doct khadija tace, Kuyi hakuri, ku gafarta min, duk abunda ke faruwa da ahalin nan gabadaya laifi na ne, Tabbas a yau zan bayyana muku gabadaya abunda ya faru, da har kukaji nice da laifi, Dakatar da ita Dad yayi da fadin, Bamua son jin komai daga gareki, kawai kiyi shiru khadija, hawayen ta Doct khadija ta share, tareda fadin Yahya a matsayina na kanwar ka, ka taimaka kabani Dama daya kacal, zan bayyana Duk kulla kullan da Karima ta aikata. Kaima kasan bazan taba maka karya bah. Ka yarda dani, Dad yace khadija a matsayin ki na kanwata ai bai kamata ki aikata aka a garemu bah, meyasa kika ci amanan wannan ahalin, meyasa kikayi mana karya, ga mama nan kema kinsan yadda mama take matukar kaunan ki duda cewar bah ita ta haife ki bah, amma tafi rubuta ki akan mu. Lokacin da Abban mu ya kawo ki gidan mu a matsayin marainiya, aka muka dauke ki tamkar yar ahalin mu har kika girma, soyayya, kulawa, da qauna, babu wanda bamu nuna miki bah, bamu taba bamban ta kan mu da ke bah, amma akan bai hanaki guduwa da wani namijin a wajan bikin ku wanda za'a muku keda Maryam bah, sannan kika je kika aure shi. kinsan halin da muka Shiga da muka ji labarin kin gudu da wani saurayin, Kinsan kunya da bakin cikin abunda kika aikata ya sanya mahaifin mu har silan akan yasa ya rasa rayuwar shi, meyasa tun farko baki fada mana ga wanda kike so bah, ai dashi zamu baki, basai kin kunyata mu a idanuwan jama'a. Amma bakomai komai yayi farko zaiyi karshe. Hawaye ne yafara gangaro wa daga idanuwan Doct khadija, cikin sheshekar kuka tace Dan Allah kubani dama daya zan fada muku duk abunda ya faru , tabbas kun yimin gurguwar fahimta ne, ku tsaga ku saurare ni. Grandma tace toh shikenen y'ata munajin ki, Muhammad Kabari ta fada mana abunda ya faru, Dad yace Tom shikenen muna jin ki, Kallon su Khalid da su nadira Dad yayi yace, ku bamu waje zamuyi magana. Dakatar da Dad doct khadija tayi da fadin Aa zuyi zaman su, suma aiba yara bane, ka barsu Suji abunda ya faru. Amma dan Allah kafun na fara inaso kowa ya bada hankalin shi wajena. Zama sukayi baki daya, yayin da kowa ya nutsu, tattaro nutsuwan ta Doct khadija tayi, ta fara magana kamar aka. Asali nida Karima babban kawaye ne tun muna bording school, zaro ido gabayansu sukayi, what! Dad yafada. Kwarai kuwa nida Karima babban kawaye ne, Kuma itadin sunan ta hassana ne,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89