Chapter 57
Chapter 57
kunci, ga abun farin ciki ya riske ki, toh na taya ki murna kinada juna biyu, Zaro ido Amriya tayi gaban ta yayi mummunan faduwa, tace juna biyu fa kika ce, nidin Kuma, Kallon ta doct khadija tayi tace, me ya faru, kamata ai ace kina farin ciki, da irin wannan abun. Amriya tace, bawai bana farin ciki bah, tunanina daya ne shine nasan Kalb bazai taba son Dan da zai futo daga kar kashi na bah. Saboda nidin ALJANAR RUWA CE, Kuma babu abunda yafi tsana a duniyar nan sama Da jinsi na wato na Aljanar ruwa. Kuma ni ina matukar sonsa. Yanzu Gashi lokaci da ya rage min a duniya kalilan ne. Doct khadija tace kada Ki taba sare wa akan abunda kike so ,dole da jajurce warki da Kuma adua, shine zaisa ki cimma burin ki wanda yake kyakyawa. Bai ka mata ace ki shiga gidan cikin bakin ciki bah, ka mata ai ace kishiga cikin farin ciki da annashuwa, Yanzu ki kwantar da hankalin ki, kije gidan cikin karfin gwiwa, Kuma ki fada masa cewar ki nada juna biyu, Nasan tabbas bazai k'i ki bah. Maza ki tafi, ki Kara karfafa wa kanki gwiwa kada ki saduda tun,kije ki fuskan ce shi, nasan tabbas zai fahimta. Godiya amriya tayi wa doct khadija, cikin farin ciki ta bar wajan. Tareda nufa hanyar gidan su Kabir. Aunty amarya lafiya na ganki acikin wannan lokacin, murmushi Aunty Amarya tayi tace, kwarai kuwa lafiya, Shawara nazo na baka, badan ko bana sonka bah, sai don soyayya da nake maka da Kuma, yan gidan nan. Okay Tom ina jinki Aunty. Aunty Amarya tace , Kabir inason ka saura reni da kyau, inason fada maka abu dake cin rai na na wajan shekara da shekaru, Kabir! Dago wa yayi ya kalle ta sannan yace na'am aunty, Aunty Amarya tace, ina son na fada maka cewar, Duk abunda Amriya ta fada dazu babu karya acikin ta, tabbas abunda ta fada gaskiya ne. Mom itace ta kashe Ummi Kuma.... Bata karasa bah taji yace, Aba Aunty, aba Aunty, koda kowa zai biyi bayan aci dun duniyar mom ai bazaki ciba . Na tabbatar miki da cewar karya Amriya tayi wa mom, so take ta hada mu nida mom dina, Kuma bata San Allah yafi karfin tah bah. Murmushi Aunty Amarya tayi, sannan tace, Allah sarki Amriya baiwar Allah, kina taimako, kina sa rayuwar ki a hatsari amma basu San kina yi bah, Kace ka tabbatar cewa karya Amriya take koh! Kabir yace yes of course, am 100% sure that, karya take yiwa mom. Aunty Amarya tace tunda ka tabbatar, toh menene hujjar kah. Kabir yace ni Banida hujja amma nasan mom can never do such thing, idan mah tayi ribar mee zata ci, Amriya kawai yar leken asiri ce, maybe wani ne ya turo ta gidan nan. Wai kai Kabir Meyasa baza ka yi nadamar abunda kakeyi bah? Saboda mahaifiya ta, ta tsaya min, Kuma Duk mahaifiyar da ta iya tsaya wa domin Kare rayuwan danta, babu wata ma'alukiya da zata iya cin galaba akan tah. Kenen kana nufin Amriya bah mutuniyar kirki bace, Dai dai lokacinda Amriya ta karaso cikin gidan. Jin muryar Kabir tayi, taji yace kwarai kuwa, Amriya bah mutuniyar kirki bace, Chakk Amriya ta tsaya, Tareda jigina ajikin kofan Tana jin abunda yake fadin. Kabir yace tunda yarinyar nan ta dora kafa fuwanta a gidan nan, toh tun lokacin masifa da baka'i suke ta faruwa, tabbas yarinyar nan bah mutuniyar arziki bace. Da nafara dana sani abunda na aikata mata, amma shigowar ki yanzu, yasa na tuna da cewar tabbas mashekiya ce , muguwa Kuma, Mara imani. Baby macen da nafi tsana a duniyar nan sama Da itah. Na tsane ta, na tsane ta, tsana mafi muni, kinga Kare war Ta mah, bana son na kara hada ido hudu da ita, banason na Kara Ganin ta har abadan abada. Hawaye ne suka Fara gangaro wa daga idanuwan Amriya, hannunta ne suka Fara Kar kar wa, kuka ne ke shirin subuce mata Saurin rufe bakin ta tayi, Tareda rintse idanuwanta jin zuciyar take kamar zata futo.. Tashi tayi daga jikin dakin, inda kuka ya ci karfinta. Juyawa gabadayan su sukayi, inda Kabir yace waye a nan. Saurin rufe bakin ta tayi, Tareda Saurin barin gidan. bude kofan Kabir yayi yaga babu kowa, futowa Aunty Amarya tayi tace shikenen, ni zan wuce, ina fatan ka gane gaskiya. Tana kaiwa nan tayi fucewar tah. Ya mutse fuska kabir yayi tareda rufe kofan ya koma kan gado ya kwanta. Tafiya Amriya ta farayi batare da tana cikin hayyacin ta bah. Dafa kanta tayi wanda ke mugun Sara mata. Jiri ne yafara di banta, a daddafe ta karasa wajan junction. Tareda samun guri ta zauna. Kallon kanta tayi, ta fashe da matsancin kuka mai cin rai. Meyasa, Meyasa, wannan wace iri yar jarabbta ce, wannan wace iriyar bakar kaddara ce, Meyasa na ka sance a raye har yanzu. Dama na kasan ce a raye ne don kawai naga wannan ranar bakin ciki, ranar da bata da gobe. Meyasa tun tuni ban mutu bah, na tsane ka Kabir, na tsane ka, bana son sake hada ido dakai, bana kaunar kah, Kuma wannan ajiyar da ka bani, zan Adana tah har karshen rayuwa ta. Zan kula da abun ciki na har numfashi na, na karshe. Tabbas zan Nisan ceka, kamar yadda ka bukata , bazaka sake haduwa da koh inuwa ta bah. Karuga da ka Gina min tsanan ka acikin zuciya ta. Rayuwa tah da komai nawa, nasa a hadari don kawai naga, baka cutu bah, amma akan baisa ka gani bah. Ta karashe maganar tana mai fashewa da kuka, mai ratsa zuciya. 馃ス馃ス馃ス馃ス馃ス馃ス馃ス馃ス COMMENT & SHARE PLS 馃檹馃檹馃檹 ALKALAMIN 馃枈锔忦煐婏笍馃枈锔? BABY ISHA 馃挒馃挒馃挒 (AISHA M.B) 2/28/24, 22:12 - AISHA M.B (Baby isha): https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v JAJIRTATTAU WRITER'S ASSOCIATION 馃枈锔? (J.A.W) Rubutu baiwa ce daga Allah,jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan kasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauk'i鉁忥 ALJANAR RUWA CE PAGE 44?45 WRITTEN & DIRECTED BY BABY ISHA (AISHA M.B). ----------------------------------------- Kallon wajan gidan Amriya tayi tace, ya Allah, kada ka kawo abunda zaisa na Kara sanya kafafuwa na acikin wannan gidan, insha Allah baza ka Kara ganina bah na har abada, har abadan abada. Mike wa tayi, ta Fara tafiya, Chan cikin dajin wajan ta nufa ta tarar da doct khadija a Zaune, Kallon ta doct "khadija tayi cikin rudewa tace, yata Amriya, me yafaru?, Meyasa kike kuka? shin Kabir ya Kara bata miki rai nee? tambayar da doct khadija ta Shiga yi wa Amriya kenen. kuka Amriya ta Kara fashe wa dashin cikin, kuna da bakin ciki, tace doct khadija na aikata wani kuskure mara goguwa a rayuwa ta, wai shin yaushe kuka na da bakin ciki zai zo karshe, Nayi dana sani futowa daga ruwa nazo duniyar mutane, Meyasa banyi za mana a ruwa bah, Kalb ne yayi sanadin futowa ta daga ruwa , abunda na futo karba daban, abunda na tarar daban, Meyasa na tsane shi, banason sa, tunda aka yake so zaiga asalin tsana Daga Aljanar ruwa, wallahi, yanzu ji nake kamar na kashe shi nima na kashe kaina. Saurin rufe mata baki doct khadija tayi tace, Aa Amriya kada
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89