Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 9

Chapter 9

Galadima Family Book 1 Complete Hausa Novel 1,262 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

sakandiri sai aka cireta, Laure ma tana samun kula sai dai takasance tun tana karama take da wasu dabi'u sam marasa kyau. A kwana a tashi babu wuya Muhammad yasamu kwalin diploma dinshi,a lokacin ne Kuma harun ya aura masa bodejo inda suka tare anan gefen gidansu bodejo din, Muhammad yataso mutum ne mai tsananin hazaqa da kokari uwa uba kuma kyau,auren su da wata uku yakoma makaranta. Lokacin da yagama Digree dinshi na farko a lokacin harun yadamqa mishi gadon su wanda tuni ansai da raqumayen,anjuya musu kudadensu inda ya habaka sosai,lokacin bodejo ta haifi danta mai santalele namiji kyakkyawa aka sanya masa Taleeb sunan mahaifin Muhammad,sai dai kiri² Muhammad ya hana a boye sunan,bayan bodejo tagama wanka Muhammad yadauke ta ya maidata cikin gari inda yayi musu gini, Laure Kuma tana zaune wajen harun da matarsa. Bayan shekaru 28 aiki ya maida Muhammad garin kaduna inda yake zaune a zaria akuma lokacin yaran Muhammad su shidda ne maza hudu mata biyu,Taleeb ne babba sai Sadeeq,Haroun,Labeeba, Maryam sai auta Hasheem. A lokacin anyi auren Taleeb da Sadeeq don rana daya akayi bikinsu. Taleeb ya aure matansa 'yar maidugri ne don shuwa ce itadin gaba da bayanta,inda Sadeeq ya aure 'yar zaria wajen fada,duk cikansu Allah ya hadasu da mata nagari. Matar Taleeb sunanta Aisha,matan Sadeeq kuma bilkisou. Shekarar da suka cika shekara guda da aure Allah yabaiwa Taleeb karuwar da namiji inda yaci sunan Muhammad Taleeb Muhammad,waton sunan kakansa inda ake cemasa Sauban,bayan cikin Sauban suka sake haihuwar mace inda aka sanya mata sunan mahaifiyar Aisha Safeena suna cemata falmata wacce take sa'a da Dan wajen Sadeeq wato Ahmad ake masa laqabi da Taufeeq. Wasa Wasa sai da Aisha tayi haihuwa hudu, Sauban,falmata, Mashahuda, Laila. Amma bilkisou tundaga kan Taufeeq bata sake haihuwa ba. A lokacin shima abba yayi aure sai dai matansa shima bata haihu da wuri ba 'yar kaduna mai suna hauwa'u. Hasheem yayi aure inda yake aure da 'yar wan mijin Guggo Laure, me suna Rabi.Yaransa uku,babban Bashir ana cemasa Aseef sai muneefa inda takeda ciki a lokacin itama bilkisou tasamu cikin nabiyu. Anyi bikin Labeeba da Maryam, Labeeba tana zaune a Canada tare da mijinta yaransu biyu muhsin da musaddiq.Inda Maryam ke Lagos sai dai ita bata haihu ba. Rabi ta haifi yaronta namiji Mai suna yassir tsakaninshi da Laila wata daya,inda itama hauwa'u ta haifi diyar ta mace akasanya mata Nihal. Alokacin da cikin jikin bilkisou itama ya bayyana sosai ahalin Muhammad suka shiga farin ciki kowa yaqosa ace tahaihu,sosai akayi zumudin cikin,lokacin haihuwa tayi ta haifi yarinyar ta kyakkyawa Masha Allah anan ne fa akashiga turka turka inda bilkisou tace sunan mahaifiyar ta za'a saka mata,shikuma Sadeeq yace sunan mahaifiyar sa zai saka Fatima. A lokacin rashin kawaicin bilkisou yafito muraratan inda tace to muddin yasa sunan bodejo to bazatayi farin cki ba,sosai ran Sadeeq yabaci dana ahalinsa sai dai su suka danne,bodejo kuwa duk bakinta haka tazuba ma bilkisou Ido, Guggo Laure kuwa tasamu bilkisou tayi mata tijara tundaga lokacin ta tsani bilkisou. Aiko aka sanya sunan bodejo wato fateematuz zahra'u suke cemata zuhra. Da farko bilkisou tace bazata shayar da jaririyar ba,sai da mahaifinta da mahaifiyar ta sukazo har gida sukayi mata tatas inda mahaifinta yace muddin Bata shayar da zuhra ba sai yayi mata baki,sannan yatasa ta taje tabaiwa bodejo hakuri da Muhammad da mijinta Sadeeq. MUHAMMAD kafin kace mene yayi fice saboda kudinsa da kuma ilimi irin na 'yayansa ga uwa uba kyau,don alokacin Taleeb Yana aiki a NNPC inda yaran gidan ke kiransa da Daddy,Sadeeq kuma yana aiki a wani company a Lagos inda yaran gidan kekiransa da Abbie sunan da Sauban yasa masa, Harun wanda suke cema Abba kuma yana lecturing a KASU ne,shima Hasheem wanda suke Kira da Baba yana lecturing ne a ABU zaria. Allah yarufama iyalensa Muhammad asiri da shi kansa dai² gwargwado,sosai sunanshi yayi fice inda a wancan lokacin zamanin sarkin lokacin ya nada masa sarautar galadiman zazzau shikenan kuma sai sunan yabisa,an nada masa sarautar babu jimawa kuma don ba'a wuce shekaru uku ba yakoma MAIDUGRI gabadaya da iyalensa,banda Abba da Abbie inda Baba Hasheem yakoma University of maidugri yacigaba da lecturing dinsa. Zuhra kuwa sosai tasha wahala a hannun mahaifiyar ta bilkisou vwacce suke kira da Ummie,duk da kuwa tataso 'yar gatace Amma sam batajij dadi ta wajen Ummie yana daya daga cikin dalilan da yasa Abbie yake tsananin son ta kenan,tunda yayi fadar har yagaji yasama Ummie Ido,mommy ce a kaduna tamaye mata gurbin mahaifiyar ta. Inda sosai mommy ke tsananin tausaya ma zuhra tare da bata cikakkiyar kular da tadace komai tare take musu ita da Nihal har Allah yabata ciki tasake haihuwar junior yasir,takuma sake haihuwan mace maimoon. Dalilin dayasa zuhra tataso da tsoron Ummie kenan tare da shakkar ta,idan kuwa ace Abbie baya gari zama takeyi kamar mara lafiya. Wannan kenan. _Cigaban labarin._ Ji kake tassss! Jikinta babu inda baya shaking tsaban rudun da take ciki hawaye ne kawai ke tsiyayowa daga idanuwanta,dafe kuncinta tayi don sosai Marin ya shige ta. Lokaci daya parlon yadauki shiru sosai Taufeeq, Mashahuda, Laila, Nihal jikin su yayi sanyi ganin irin marin da Ummie ta zabga ma zuhra,cikin kakkausar murya tayi pointin dinta tare da cewa. "Karyan rashin hankali kikeyi zankoya miki natsuwa ne,stupid kawai. Takarisa maganar tare da jan tsaki cikin muryan tsawa tace"Get out !!! Da wani irin sassarfa zuhra tafita inda jikinta babu inda baya rawa, Taleeb kuwa sunkuyar dakanshi yayi idanuwan shi sunyi jajazur. Kaitsaye apartment din Ammi zuhra ta wuce,kicibus tayi da Ammi a kofar hawa stairs din Daddy, fadawa tayi jikin Ammi tare da fashewa da wani irin kuka mai tsuma zuciyar duk wani mai sauraro,cikin rawar murya tace. "Ammi...Am...Ammi don Allah Ummie ne mama na? Ummie ne ta haifeni?meyasa Ummie tatsaneni?please kuje kubata hakuri kuce tasoniiii...taja kalmar saboda wani irin kuka da yazo mata. A hankali Ammi takai hannu tana shafa kan zuhra cikin tsananin tausayin ta wani kwalla taji ya taru mata a idanuwan ta,kama hannunta tayi tanufi hanyar wani corridor inda zai sadata da parlon ta,zaunar da zuhra tayi akan sofa. Facing dinta tayi tare da kakalo murmushi takira sunan zuhra, dago dara²n idanuwan ta tayi wanda suka tasa saboda kuka ta zubawa Ammi. "Kiyahakuri kinji?kidauki duk wani abu da zaifaru dake a matsayin kaddara da kuma jarabawa kinji?Allah Yana sane dake Koda wasa kuma kada nasake ji kinkuma fadar maganar nan,watarana fah sai labari kinji zuhra na? Daga kai kawai tayi tare da amsawa Ammi,murmushi Ammi tayi tace"kinci abinci? Cikin sanyin muryan ta tace"A'ah yanzu zanje wajen Mommy na amsa alale na. Ammi tace"yawwa to taaji kije Allah yamiki albarka. Mikewa tayi cikin sanyin ta tafita,kaitsaye apartment din mommy tanufa dai² dan lungun shuke shuke tsakanin apartment din Mom dana mommy taji anfisgo ta tafada jikin mutum. A tsananin gigice ta dago tare da kokarin sanya ihu,Ido biyu sukayi da Aseef inda yake binta da wani irin matsiyacin kallo Yana lashe lips. Jikin zuhra ne yatsananta kadawa,kirjinta na tsananin bugawa,baki yakai da zummar yimata sumba Allah kuwa yabata sa'a ta dunkule hannu takaimasa punch a hanci. Ai tuni yasaketa yana me dafe hancinsa,itakuwa zuhra dagudu ta falla bata tsaya ko inaba sai apartment din Mom banda nishi babu abinda takeyi,hawaye kuwa

Table of Contents

Chapters

87 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});