Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 13

Chapter 13

Galadima Family Book 1 Complete Hausa Novel 1,265 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kewar mutanen kadunan. *_IDAN NAGA RUWAN COMMENTS ANJIMA NASAKI DAYAN PAGE DIN😃._* Xahratty CE🥰 Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️. 19/2/23. [3/21, 22:27] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳 Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar⤵️ A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page 10 _Bismillahir-rahmanir-raheem_ _____Ayau Saturday ne kuma su zuhra zasuyi jamb dinsu,tun wajen 7:30 tatashi tayi duk abinda yakamata. Don Daddy yace 8:00 zai dauketa su tafi wajen bodejo taje don mata sallama ita da galadima a parlon taciddasu su duka sanye da medical glass suna kallon tashan aljazeera. Amsa sallamar da tayi sukayi suna maida hankali akanta,duban tsanaki bodejo kemata sosai take mamakin girman zuhra don zakayi tunanin takai shekara 18 koma 20 saboda yanda Allah ya halicceta da diri sosai ko ina tubarkallah Masha Allah. Sanye take da Dubai gown Army Green sai white flatshoe duk da cewa face nata babu makeup sai dai tayi kyau sosai. Gaishesu tayi cike da kulawa suka amsa mata,bodejo tace"Har anfito za'a tafi? Daga kai zuhra tayi tace"Eah bodejo zanje wajen Daddy ne mutafi. Galadima yace"toh Allah yabada sa'a ubangiji yasa kifito da 300 score. Dariya suka sanya gabadaya zuhra tace"Ameen my Galadima na tafi. Fatan dawowa lafiya suka mata sannan suka fita, apartment Baba Hasheem tafara shiga, Mom tasamu a kitchen don haka tafara gaisheta tana tambayar Baba,cike da fari'a Mom ta amsa anan take sanar da ita baima tashi daga bacci ba. Sanar mata tayi da yanzu zata tafi wajen exam din jamb idan ya tashi ta gaisheshi. Fatan alheri Mom tamata. Koda tashiga apartment din Ammi a dinning ta taddasu itada Daddy,cikin shauki takarisa garesu face nata dauke da yalwataccen fari'a. "Good morning Ammi, good morning Daddy. Cikin fari'ah suke dubanta, Ammi tace"Morning my zuhra antashi lafiya? Daddy yadubeta yace"ah lallai mamana har anfito ne? Murmushi tayi tace"Ea. "To kizauna kiyi breakfast tare da Daddyn naku kafin shima Sauban yafito. Sosai kirjin zuhra yabuga saboda batason haduwa da Sauban din. Cikin sauri ta girgiza kai tace"A'ah Mom nayi breakfast Alhamdulillah bari naje dakin Aunty Mashahuda nayi mata bangajiyan jiya. Ammi tayi murmushi tace"ai bata tashi daga bacci takoma gashi ansamu hutun hadda. Cikin sanyin jiki zuhra tajuya don komawa parlon ta zauna, clashing sukayi da Sauban wanda fitowanshi kenan,suit ne a jikinsa blue black da covershoe black agogo kirara Gucci yake daura bakajin kamshin komai sai na perfume din da yasanya. Hada ido sukayi da zuhra wani harara ya gallamata,itakuwa cikin sauri ta dukar dakai tana murguda baki a hankali tace"Ina kwana. Ko amsawa beyi ba yasamu waje ya zauna,tare da gaisar da iyayen nasa. Cike da kulawa suka amsa,Ammi tace"Son kanwarka na gaisheka. Dan yamutsa face yayi sannan yace"Sweetheart banji bane hankali na na wani wajen,daganan sai ya cigaba dacin abincin sa. Daddy da Ammi kuwa murmushi kawai sukayi,a gurguje suka gama cin abincin,mikewa Daddy yayi Sauban ma yamike. kaitsaye parking space suka isa inda Daddy yashiga gidan baya zuhra kuwa gaba tashiga. Sauban ne yaja motan tare da sanya karatun alqur'ani na Abdullah Abba Zaria,zuhra kuwa a ranta tace"wannan mutumin mayen karatun Abdullahi Abba ne idan anbibiya ma baisan shi ba. "Idan ni bansanshi ba aike kinsanshi koh?taji muryan Sauban yajefeta da wannan tambayar a rikice zuhra tadago tana dubansa. Don sam batayi zaton karatun zucin da takeyi yafito fili ba,idanuwanta gabadaya ta diddilo waje tana duban Sauban. Shikuwa ko kallon inda take beyi ba yacigaba da driving dinsa. Koda suka kariso center da zatayi Jamba din Daddy dakanshi yashiga yakaita don har anfaffara shiga hall din. Nan Daddy yace tanatau tamaida hankali tayi exam din cikin nutsuwa,cike da girmamawa ta amsa masa da toh. Sai wajen karfe 11:30 su Zuhra suka fito daga wajen rubuta Jamb din,cike wajen yake da maza da mata,wasu sa'o'inta wasu sungirme mata wasu kuma ta girmesu sai hayaniya yake tashi a wajen cikin sanyin ta itakuwa take tafiya a kofan gate din center tatsaya tana tunanin ta inda zata koma gida gashi ita bawani sanin maidugri tayi ba. Hankalinta gabadaya yakoma gida saboda yanda taga anata zuwa daukan wasu daga gidajensu wasu kuma suna tsare adaidaita sahu,da yawansu zuwa daukansu akeyi. Samun gefen gate din tayi tatsaya. Duk wanda yazo wucewa sai yadubeta fuskar nan a hade wayanta taciro da niyyar kiran Ammi sai taji magana daga gefenta,cikin natsuwa ta dago don ganin me maganar. Wani saurayi tagani a tsaye yadubeta tare da nuna mata bakin titi yace"Wai kije inji brother naki,a hankali zuhra ta sauke wani gwauron ajiyar zuciya cikin nutsuwa tanufi motar. Sukuwa gabadaya student dinnan hankalinsu yakoma kan motar da ya Sauban ke ciki,'yan mata kuwa da dama ganinsa yasa sun susuce. Sallama tayi iya labba har tanufi gidan baya da niyyar shiga sai tatuno da maganar Aunty Mashahuda don haka sai tabude front seat tazauna,tare da gaidashi. Da kamar bazai amsa ba sai kuma zuwa can ya amsa. Sunyi tafiya babu wanda yayi koda tari sai zuwa can Sauban yadan dubeta, gyaran murya yayi tare da sake dan tsuke face yace"wannan Jamb din da kikayi tamkar aikin banza ne don basan karatun kike ba. Cike da rashin fahimta Zuhra ke dubansa,ta wutsiyar ido yake dubanta,gane bata fahimci abinda yake nufi ba yasashi cewa. "Zansamu Abbie nafada masa cewa keba karatu ne a gabanki ba aure kikeso tunda nakama ki sau biyu kenan. Da sauri tadago tana dubanshi tare da tsantsar mamaki da razana da kalamanshi mouth dinta har rawa yake tace"a'ah wallahi Yaya burina nayi karatu nazaba journalist don Allah kada kafada mai niba aure nakeso ba,kuma ma wazan aura?cike da yarinta tare da tsantsar shagwaba take maganar. Shi Aseef din dana ganku tare ba soyayya kukeyi ba?sannan yaron da yakawo ku gida keda Mashahuda ba soyayya kuke ba?cikin sauri tafara girgiza kai tace"wallahi duka babu Wanda nake soyayya dashi kuma nibansan wani abu soyayya ba niko friend namiji bantaba yiba Allah. Ta sake magana cikin tsantsar yarinta,shiko Sauban dage kafada yayi irin ko a jikinshin nan ya cigaba da driving dinsa cikin kwanciyar hankali. Itakuwa zuhra gabadaya neman natsuwa tayi tarasa burinta yace bazai fada ba.A haka dai suka karisa gida. Da sauri ta balle murfin motar tafito kaitsaye apartment din Ammi tanufa,shikuwa Sauban koda ya ajeta juya kan motan yayi yasake fita. Da sallama tashiga parlon babu kowa sai Aunty Mashahuda,ganin ta yasa tasaki murmushi tana cewa. "Yawwa Zuhra naje nemanki ai dazu shine bodejo tace kinje rubuta Jamb kinsan menene? Girgiza kai Zuhra tayi. Mashahuda tasaki murmushi tace"guy din jiyane da muka hadu a supermarket yakira wai Shuraim koh?shine fa yace nahadashi dake nace baki kusa kinje zana Jamb. Waro idanuwa Zuhra tayi tare da dafe kirji tace"please Aunty Mashahuda kirufamin asiri wallahi adena maganar sa kinsan idan Daddy ko Abbie sukaji zanshiga uku,sannan za'ace guda nawa nake. Mashahuda takama baki tace"toh yanzu zuhra cemasa za'ayi baki sonsa? gaskiya nibazan iya fada masa haka ba sai dai ke kice masa. Zuhra tace"ni bazan iya waya dashi ba Aunty wallahi inajin tsoro kawai abar maganar kirabu dashi Allah,takarisa maganar tana mike tare da fita daga parlon. Murmushi kawai Mashahuda tayi sannan tamike tanufi stairs din Daddy. _____+++_____ A bangaren su Guggo Laure kuwa sai shirye-shirye suke saboda Galadima yakirata cewa su Abba zasu

Table of Contents

Chapters

87 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});