Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 22

Chapter 22

Galadima Family Book 1 Complete Hausa Novel 1,266 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

please kici abincin kinji?ko so kike kitayar ma da mutane hankali? "Rashin Abbie bake kadai kikayi ba amma tabbas ke zaifi miki zafi kiyahakuri, Nihal takarisa maganar. "Yawwa ku kwantar mata da hankali, Laila maza kishiga dakina kidaukomin makullin dakin yayanku da aka gyara masa dazu. Mikewa Laila tayi tanufi bedroom din Ammi don dauki keys din. Cin abincin kawai takeyi badon tanajin test nashi a bakinta ba,sallamar mommy ne yasasu dagowa. "Zuhra yanzu kika fara cin abincin ne?mommy tayi maganar. "Eah mommy yanzu nafara. "Ok to kiyi kigama zamu koma kd yanzu tare da Ummien ki kizo muje kiyi mata sallama. "Nidai mommy kubarta tatafi don Allah nidai ina gaisheta".Tayi maganar cikin sanyin murya. "A'ah haba zuhra taya mahaifiyar ki zata tafi kice agaisheta? a'ah tashi kije kiyimata sallama. "Ammi inajin tsoro ne please Ummie tace nadena bari tana ganin bakar fuskata,tayi maganar hawaye suna zuba. Kamota Ammi tayi taahare mata hawayen sannan takama hannunta tace"Hauwa muje nasan sun fito tun dazu ko? Mommy tace"sunanan wajen mota. Farfajiyar gidan suka fito inda su Mom, Bodejo, Amma Adda Zainab suke tsaye dasu Aunty Maryam,zuhra kanta a kasa tana tafiya idanuwanta ya cika taf da hawaye. Har gaban Ummie Ammi takaita,da dan hanzari Ummie ta matsa,duk wadanda ke wajen basuji dadin hakan ba,cikin rawar murya zuhra tafara magana. "Ummie ku gaida gida Allah yatsare, Allah yakara hakuri da juriya",tana gama fadar haka tajuya tatafi. 'yan labba Ummie kawai ta amsa,anafa kowa yafara musu sallama don ya Sauban ne zai kaisu airport,mota biyu sukayi dayar Aseef kejanta,haka suka jera sukayi na airport din. Haka suka tafi suna dagawa juna hannu, Ummie kuwa haka tadake saboda kukan dake neman kwace mata,hajiya Amma tadan dube Ummie tare da tabe baki taciro medical glass dinta ta sanya tare da kankance idanuwa. "Yanzu ke fisabilillah Bilkisou bazaki iya daukar diyarki takoma hannunki ba?kijata a jiki? Nannauyan ajiyan zuciya Ummie ta sauke tace"To Amma taya zan daukota alhalin school tafara zuwa anan?kuma Abbie nata shida kanshi suka yanke hukunci dasu Galadima da Yaya kan tadawo nan. "Yo ba dole ba?ai dole suyi haka,kada kinemi sabauta masu diya,kinga ko babu komai sun nuna miki sunfiki sonta da sanin darajar ta,ance tana fama da ciwon zuciya zasu barmiki itace ki karasa musu?takarisa maganar tana kawar da fuskanta kamar ba itace tayi maganar. Duban Adda zainab Ummie tayi tace"Adda don Allah kiyima Amma bayani ta fahimceni bawai fa banson zuhra bane..... "Kinga Bilkisou ni babu wani bayani dazanyi miki kiyi kokari kawai kija diyarki ajiki,tayi maganar tana sake tamke fuska. Sosai Ummien nashi tabashi tausayi saboda ganin yanda duk suke mata kallon mai lefi. "Ni Amma sai nake ganin kaman maganar su Yaya da gaskiya da sukace lamarina da yarinyar can kamar akwai sihiri a ciki. Gyara zama Amma tayi tamaida hankalinta wajen Ummie tace"ko Bilkisou? Daga kai Amma tayi tace"Ea nima kuma sai nafara zargin hakan,saboda me zuhra tayimin ne da nake mata haka?nice fa uwar dana tsuguna na haifeta... "Kinji Kuma wani magana Amma?asiri kike nufi?to taya za'a muku asiri?kudai kudena daukar wa kanku jita-jita da zargi kuna sanyawa zukatanku,wallahi Bilkisou duk lefinki ne amma kinki yarda ai shikenan. A daidai nan suka kariso filin jirgin. Duk firfitowa sukayi daga motar,anan Amma kecewa bataga Taufeeq ba,shine Abba yace ai Galadima yace yabari sai jibi yakoma. Murmushi kwance a saman fuskar Amma tace"Haroun kunadai nema ku kwace duka yaran su koma maidugri da zama,ba za'a bar mata ko guda daya bane anan? Shima Abba cike da dattaku yace"a'ah hajiya Amma taya za'a kwacesu?ai Bilkisou tananan a gidanta shima Taufeeq din sako yatsaya ya amsar mata wajen Galadima. ****** Duk cikansu sunyi jugum suna sauraren babban Aminini Galadima, tsoho Mai ran karfe shima masani ne akan abinda ya shafi sihiri kuma yana karya sihiri da yardan Allah yazama kamar ba'ayi ba. "Lallai lallai muhammadu farraqu akayima yarinyar nan da uwarta don bokan da yayi wannan aikin bakaramin ahedani bane,sannan a yanzu haka ba zaiyuwu in karya asirin ba har sai anje kasan gadon ita mahaifiyar yarinyar andauko wani tukunyar kasa wanda aka tsafacesa sosai akawo. "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un!!!!sautin dake tahi Kenan a babban zauren Malam Baba. A kofar shiga sashen nata gefen fulawoyi shima anhaka rami anbinne wani abu, wallahi muhammadu ban isa nakarya wannan abin ba har sai an binno wadannan abubuwan don tabbas wacce tayi wannan abin ta zalincesu kuma taci amanar su. Bodejo tace"Malam Baba itakuwa wacece wannan?don Allah kafada don a hukunta ta. Dan murmushi Malam Baba yayi yace"ai hajiya bodejo fadar baida wani amfani saboda lokaci na dauka wacce tayi abin da kanta zata kawo kanta gareku amma tabbas hatsabibiya ce. Daddy yace"lallai koma wacece mu bazamu yafe mata ba Allah ma yagani. Duban Taufeeq Malam Baba yayi yace"yanzu malam Taufeeq Kaine aikin nan ke gabanka,zaka iya?. Cike da kwarin gwiwwa Taufeeq ya dagama Malam Baba kai yace"anya kuwa?saboda anason mai dakakken zuciya wanda sam bashida tsoro,yakarisa maganar yana kurawa Taufeeq Ido. Shiko tsakani da Allah Taufeeq yariga yasan kansa akan tsoro don haka sai ya girgiza kai. Murmushi Malam Baba yayi yace"toh kunemi wanda zaije Taleeb,idan kunyanke hukunci kubashi wannan man yashafa,man zaitun ne dana habba akayi mishi hadi da magunguna"yakarisa maganar yana dauko wata 'yar kwalba wacce sai kamshi take zubawa inda yacce da andauko ko kwana biyu kada abari yayi ba'a kawo masa ba. Sosai sukayi mishi godiya inda anan ne kuma akasa almajiran Malam Baba suka dinga shigo da buhunhunan abinci,dama duk shekara Galadima na aiko masa da zakka amma wannan ihisani ne kawai. Daddy anan yabashi dubu hamsin, Baba Hashim yakara mishi da ashirin. Almajiran kuwa Galadima yaraba musu 'yan dari bibbiyu. Anan akayi sallama suka baro kauyen su Bodejo sukayi cikin gari,da yake mota biyu sukayo a mota kowa da abinda yake sakawa,basu suka shigo gida ba sai bayan isha'i. ****** *KADUNA* ***** Anguwan rimi kaduna gidane hadadde na gani na fada sai dai ko kai gidansu Ummie beyiba. Hankalinta atashe yake banda gumi babu abinda takeyi jikinta har rawa yakeyi tana magana. "Hajiya Aliya don Allah kidena wannan maganar asirina nagab da tonuwa fa,nidai mushirya muje nijar din tunkafin su sa akarya musu asirin nan,kina gani a lokacin da akayi wani irin asara ne banyi ba na kashe kudade da kadarori. "A'ah ba nufina kenan ba ai ba asara bane tunda bukata ta biya nasani amma wallahi banaso akarya nibanki har Bilkisou tabar gidan duniyar nanba batare da tashirya da diyar ta ba. Tadan tsagaita saboda maganar da ake acan bangaren. "Toh menene?wancen ma ba maradin mukaje ba?nidai bukata kawai nake nema,ke ko nawane zan iya kashewa idan har zan samu abinda nakeso. Magana aka cigaba da mata tacan bangaren. To Shikenan kikirashin don Allah bakiga yanda na tsure ba inama taoro ne kada asiri na ya tonu,wallahi nayi zawo babu adadi tsaban tsoro. Nagode nagode hajiya Aliya babu abinda zance miki don kina temakona. Aje wayan tayi tana sauke ajiyar zuciya,gumi kuwa haka yake tsattsafo mata. ( _Itakuwa wannan ni fatsimaπŸ€” reader's ko ku kunfahimci wacece ita?_ ) Xahratty CEπŸ₯° π‹πšπ₯π₯𝐚𝐒 𝐀π₯πͺ𝐚π₯πšπ¦π’πŸ–ŠοΈπ˜πšπŸπ’ π­πšπ€π¨π›π’πŸ—‘οΈ 19/3/23. [3/21, 22:27] Xahratty (OUM AJMAL): πŸ‘¨πŸ½β€πŸ¦³ *_GALADIMA FAMILY_*πŸ‘¨πŸ½β€πŸ¦³ Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar‡️ A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_*

Table of Contents

Chapters

87 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});