Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 25

Chapter 25

Galadima Family Book 1 Complete Hausa Novel 1,264 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

tayi tace"Ok na fahimta to kikiyaye gaba maganar gaskiya kuma kada ki rufa a sonsa da yawa na fada miki. "Insha Allah momy"Akeela tayi maganar tana rungumo hjy dahara zuwa jikinta. ** *GALADIMA HOUSE* ** Zuhra cike da gajiya tadawo daga makaranta kaitsaye apartment din Ammi tanufa,babu kowa a parlon don haka tanufi dakin Aunty Mashahuda,koda ta isa tacidda ta tana waya kuma da alama da ya Taufeeq take wayan saboda yanda take maganar. "Shikenan Darling T bari zankira ka zuwa anjima ka gaishe da ya Sauban din Allah yakara sauki. Nan takatse kiran tana duban Zuhra. "Yanzu kika dawo? "Ea wallahi Aunty ai nadawo da matsananciyar gajiya ne a jikina shiyasa. "Ok toh kisamu ki watsa ruwa zakiji normal insha Allah. Zuhra tace"insha Allah yanzu kuwa Aunty,takarisa maganar tana zare turkey gown dinda tasanya kallon ruwan powder wanda yayi mata kyau sosai,towel din Aunty Mashahuda dake kofan bathroom tadauka tasanya. Dan murmushi kadan Aunty Mashahuda tayi bayan Zuhra tashige toilet a hankali tace"zuhra duk namijin da ya aure ke yamure, Allah ya hadaki da miji nagari. *KADUNA JABI ROAD* Daqyar yatashi yayi sallan la'asar shima da temakon Abba don mommy batanan taje gidansu suna,tare sukaje da Nihal da Laila,kuma sai gobe zata dawo. Zuwa wajen sallar magrib jikin nashi yadanyi dama sosai don haka bayan sallar isha'i yafara haka inda malam Baba yayi masa kwatance, Taufeeq na tayashi shidai Abba yana tsaye yana kallon wannan abin al'ajabin abu kamar a mafarki,suna cikin hakin ne hayaki yafara tashi sosai bakinkirin,sannan sai akafara wasu maganganu da wani irin yare wanda sam sunkasa fahimtar abinda ake cewa,jikin Sauban ne yafara rawa saboda jawo wani bakin tsumma daya farajawo wa daga ramin. "La'iala ha illalllahu muhammadan rasulillah"kalman da yaketa ambata kenan shikadai yasan azaban da yakeji gashi yaki sakin kyallen,yana gama jawo wa atake anan yafadi sumamme,daga Abba har ya Taufeeq wajensa suka runtuma suna ambatan sunan sa. Abba kuwa banda salati babu abinda yakeyi,a dai-dai kuma wannan lokacin ne itama Ummie tayanke jiki tafadi sumammiya don haka cikin rudewa Baba sa'a metayata zama kawar Amma ne tanufe ta tana ambatan sunanta tana girgizata. Da gudu tafito inda ta taradda wani tashin hankalin ma nufar su Abba tayi tana cewa"innalillahi wa Inna ilaihirraji'un haruna wannan wani irin musiba ne yau ya tunkaromu a gidan?ga Bilkisou can itama rai a hannun Allah ta yanke jiki tafadi.....ai ko gama magana batayi ba Taufeeq yanufi cikin sashin Ummie cikin tsananin rudu. Abba kuwa banda salati babu abinda yakeyi megadi yashiga kwala ma kira"safiyanu!safiyanu!!!kana inane?shima cikin rudu ya iso yace. "Ranka shidade gani,maza kamamin Sauban munufi dakinsa dashi,aiko nan suka ciccibeshi sukayi na dakin don dama Aseef baya gidan,number Galadima yashiga nema. Aiko babu jimawa yadauki wayar. "Assalamu alaikum, Galadima barka da rana?nace don Allah meza'a baiwa Sauban yaciro dayan abin ne gashi jikin yafi bayama rikicewa ance Bilkisou ma tayanke jiki tafadi kuma ina zargin duk sanadin Ciro abinne. Cike da dattaku da jarumta a muryan tsoho yasanar dashi cewa bari yakira Malam Baba yaji mezaice. Katse Kiran yayi ko minti goma ba'ayi ba yakira Abba nan yashiga sanar dashi abinda zaiyi wato zaihada garin maganin nan da wannan man nacikin kwalba ya cakuda tare da karanta suratu ikhlas,falaq,nass sai yashiga shafa mishi Yana durza mishi a goshinsa,da toh Abba ya amsa tare da fara shafama Sauban maganin. ***** Banda sintiri babu abinda takeyi tare da duban kawarta tsoro karara bayyane a fuskar ta tace"nashiga uku hajiya Aliya inatsoron tonuwan asiri na 'yan uwana sun yarda dani gashi kince boka yayi fushi dani. "Hmmm aminiyata cewa fah yayi kinja anata Kona masa aljanunsa gashinan sunyi mummunan fushi dashi don haka nema yace"gobe da sassafe yana neman mu a dajin katamu inba haka ba duk abinda yafaru kiyi kuka da kanki. Dora hannu aka tayi tafara kuka rurus tamkar wata karamar yarinya"innalillahi wa Inna ilaihirraji'un yazanyi hajiya Aliya?wani karya zanyi har Alhaji yabarni naje nijar?nashiga uku wallahi da nasan wannan tsinannen tsohon zai iya gano Shirin mu da dajin da babu wanda zai iya zuwa zansa abinne, "Sannan wayaje har karkashin gadon Bilkisou yaciro wannan tukunyar?kadafa kimance boka yace"duk Wanda ya koda taba tukunyar ne mutuwa zaiyi balle ace wai andauko shi kacokar? Xahratty CE🥰 Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️. 22/3/23. [5/4, 14:36] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳 Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar⤵️ A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page:- 27/28 _Bismillahir-rahmanir-raheem._ _____kamar yanda aka shafama Sauban maganin haka Baba sa'a ta shafawa Ummie,cikin hukuncin Allah Sauban yasamu dan dama sosai a jikin nashi,itakuwa Ummie da azababben ciwon kai tatashi dole tasa su Abba suka garzaya da ita asibitin giwa hospital ba'a dau wani lokaci ba aka bata gado saboda yanda Doctor din yasanar da Abba cewa jinin ummien yahau sosai. Don haka Abba yakira Daddy yasanar dashi, Baba sa'a itace tayi zaman jinyar inda su Abba basu bar hospital dinba har kusan 10:30. ***** Tunda Alhaji yakirata cewa bazai samu dawowa ba sai jibi yana da meeting aiko taji dadi don a daren gidan hajiya Aliya ta kwana. Washegari kuwa da sassafe driver dinta yajasu a mota suka nufi nijar duk da tafiya ce me tsaho kuma da alama za'a wahala hakan bata shafesu ba sudai burinsu susami biyan bukata. Haka yadinga falfala uban gudu dasu a hanya. *OLD MAIDUGRI* A washegari Sauban yadawo batare da taufeeq ba don shi yana tare da Ummie shima don saboda sakonin ne,koda yadawo babu jimawa suka kama hanya,Galadima, Daddy, Baba Hashim,Sauban suka nufi kauye don ganin malama Baba. Basu wani jima ba suka kariso,tarba na mutumci malam Baba yayi ma aminin nasa,don zabi guda biyar yasa aka gasa musu shi sai madarar shanu mai dumi wanda banda maiko babu abinda yakeyi. Sai da suka natsu gabadaya don har sallan azahar sukayi kafin malam Baba yayi musu ison shiga wani daki a cikin zauren nashi,ba wani wadataccen haske bane a dakin. Duban Sauban yayi yace"malam muhammadu kawo sakonnin,yakarisa mahanar cike da raha. Hannun Sauban na rawa yamika masa,aiko wannan kyallen yafara hayaqi inda akafara magana cikin wani yare,babu bata lokaci malam Baba yasaka kyallen cikin wata qatuwar kwalba,tare da rufe kwalban da murfinsa. Aiko abin al'ajabi kyallen ne kewani irin girgiza a cikin kwalban,inda hayaki ya turnuke cikin kwalbar. Tukunyar nan yadibo wani ruwa a kwarya yakafa baki alamun addu'o'i yakeyi kafin kuma yafara watsa ruwa a jikin tukunyar kasan,aiko nan tashiga daddarewa ko ina yana tsagewa a jikinta har yafashe dakansa inda wadu kulle-kullen layoyi suka shiga bayyana. Hankalinsu Daddy ne yayi kololuwan tashi saboda cin karo da sukayi da hoton Ummie da zuhra ranar suna fuskar ta dauke da murmushi a kasa an rubuta, _Mummunan farraqu,har subar gidan duniya basu babu juna wutar kiyayyar diyarta shi zai cigaba da wanzuwa a zuciyar ta._ "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un!!! Kalmar dasu Daddy suka shiga maimaitawa kenan, Baba Hashim yashare ruwan hawayen da yakawo masa, Galadima dukar dakai yayi Daddy da Sauban kuwa jijiyoyin kan nan tayi baro-baro. "Ya Salam hasbunallah wa ni'imal wakeel,malam baba wannan wane irin musifa ne haka?wane mara imanin ne ya aikata haka?tabbas ko waye wannan yacika cikakken mara imani. Galadima yayi maganar. "Huhhh Sauban yafitar da wani huci idanuwan nan sunyi jajazur,kansa

Table of Contents

Chapters

87 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});