Chapter 2
Chapter 2
Laila kai alamun eh. Nihal kuwa kyabe baki tayi don Allah yasani tana tsananin takaicin wannan miskilancin na zuhra. A hankali tacigaba da cin abincinta aqasan zuciyarta kuwa tarasa dalilin da yasa Ummie tatsaneta tun tasowarta,inda sabo yaci ace tasaba sai dai sam hakan taqi yuwuwa,ita da zasubi ta nata dasun maidata maidugri wajen bodejo don tafi samun natsuwa da kulawa,maganar mommy ce takatse mata tunani. "Zuhra kiyi kigama ci mana yanzu fa kusan 11:28 yakamata ace kinje har kindawo. Cikin sanyin muryanta tace"tohm mommy ai yanzu zan gama,cikin natsuwa tagama cin abincin tare da daukan tisue tagoge bakinta, miqewa tayi tare da rataya jakanta tace"Ummie,mommy natafi,sister's sai nadawo. Laila tace"Bari nazo narakaki sis,murmushi zuhra tayi najin dadi tace"yawwa aiko naji dadi, duban ya taufeeq Laila tayi tace"Yaya pls ko zaka saukemu al shagon ne?kafin yayi mgn mommy tace"a'ah kuda kukeda shiririta?taufeeq sauri yake zashi company don yakusa ma late sai dai Aseef yakaiku. Wani irin dadi Aseef yaji a ransa,sai dai kafin wani yayi magana taufeeq yace"No no no no mommy bari na'ajesu sharp ² saina wuce. Fuska kwance da fari'a mommy tace"toh shikenan taufeeq ka ajesu,duban nihal yayi yace"keba zakiyi rakiyar ba nihal? Murmushi tayi tace"a'ah Yaya bazani ba,dariya Laila tasaki cike da sharri tace"ae Yaya nihal tana takaicin zuwa saloon taga yanda ake wankema masu gashi kai Amma ita kai kamar na jariri dan wata hudu😃 Gabadaya farlon dariya akasa harda Ummie idan kacire Nihal da tataso aguje tabiyo Laila tana zazzage mata kwandon masifa,da gudu Laila tafita tana dariya, Nihal dinma baya tarufa mata,mommy tace"Kai Laila Laila akwai sharri. Fita ya taufeeq yayi yana dariya, Ummie ma miqewa tayi tanufi main farlo. Daqyar ya taufeeq yadawo da Nihal ciki sannan suka tafi,a mota kuwa banda dariya babu abinda zuhra keyi,sosai hankalin ya taufeeq dana Laila yakoma kan zuhra don rabonda tayi irin wannan nishadin tun ana saura sati daya Abbie yatafi Indonesia,sai gashi yau tayi,hakan baqaramin dadi ya taufeeq yajiba dagashi har Laila,a haka suka karisa shagon saloon din,saukesu yayi sannan yajuya yatafi,sukuma suka shiga cikin shagon. WAI WACECE ZUHRA?MENENE MATSAYINTA A CIKIN GIDAN?AKWAI TURKA-TURKA DA HAUTSIMA ANAN GABA KUDAI KUBINI MUJE Xahratty Ce🥰 Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️ [3/21, 22:27] Xahratty (OUM AJMAL): https://chat.whatsapp.com/LNYjzpjYlHH8OHTK0bdHGw 👨🏽🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽🦳 Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar⤵️ A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page 02 A can kuwa Zaune suke gabadaya a farlon Galadima Daddy,Abbiey,Abba,baba hasheem, Galadima ne zaune a lallausan kujeran sa mekama da gado na irin wanda ake kishingidar nan akai cikin muryanshi me kama dana babban mutum me cike da dattako yafara magana tare da gyaran muryan"Taleeb a matsayinka na babba acikin family dinnan idan kacire ni da bodejo da Kuma guggon ku Laure to kaine babba,magana guda ne ta taramu anan kowa yasan magana ce baiwuce na yaran nan ba tundaga kan Sauban har zuwa kansu mashahuda,wai boko hauka ne?meyasa kuke nema kukoma koyi da yaren yahudawa ne?yaranku sun girma kuma ko wannensu idan aka masa aure zama zeyi to akan mene?ga Sauban nan dashi da taufeeq sun cika ko wannensu ba master's ne dashi ba? Galadima yayi maganar yana dubansu cike da nazari, Daddy yace"hakane Alhaji munaso ne dama munemi yaran idan anzo saka ranar su mashahuda kan maganar saka nasu ranar idan yaso komai yazo yanda kowa keso sai a hada bikin nasu rana daya ayi ko sadeeq?yayi maganar yana duban Abbie. Abbie yace"Ea yaya nima inaso nakira Ummien yaran ne nace sutaho gabadaya dama abinda yahanasu zuwa maganar jamb class dinda zuhura keyi ne so zankirasu zutaho nan din kawai.Galadima yace "gaskiya kuwa,anjima idan an idar da sallar la'asar inaso muje daku gabadaya mu duba jikin Laure ance tanata zazzabi tana kwance. Gabadaya suka amsa da insha Allah sannan suka miqe suka nufi masallaci gabadayansu harda Galadima. Zaune yake a dakinsa yana duba wani saqo a laptop dinsa da aka turo masa ta Email dinsa,wani company a qasar maleyshia taturo dashi kan suna son daukanshi aiki idan babu damuwa suna nemanshi Nanda 4days kan yazo za'ayi musu interview a cikin su goma Sha shida 'yan nan Nigeria. Sosai yaji dadin hakan aransa wanda inba kalura dakyau ba bazaka fahimci hakan ba, duk da fuskanshi takasance me tsananin kyau tamkar jinin larabawa,dama shidin jinin shuwaarab ne,miqewa yayi a fili yafurta"ALHAMDULILLAH,Masha Allahu laquwwatu illa billah,jallabiya wata blue black yadakko ta yasaka wacce tayi tsananin yimishi kyau yafita,kaitsaye masallacin dake layinsu ya nufa. Koda aka idar da sallah tare suka fito dasu Daddy,wajen Abbie yanufa fuskanshi dauke da murmushi duk cikansu da mamaki suke dubansa baba hasheem yace"A'ah Sauban yaushe Kuma kadawo garin?Abba yace"tambayeshi dai kam.Dariya yayi tare da dan rissiniwa yafara gaggaishesu, cike dajin dadi gabadayansu suke amsawa. Murmushi yayi wanda yasa dimple din gefen kumatunsa lobawa yace"Ai Ina ajesu kawai najuyo don banma shigo gida ba sai wajejen asubah. Galadima yace"kunji koh?kunji irin gangancin nasa Koh?inbanda kasada mezesa kadawo a wannan lokacin kamar Wanda ake kora? Abbie yace"Sadauki ba na hanaka tafiyar dare ba?ai wannan ganganci ne kadena sam baida amfani. Rissinawa yayi kadan yace"insha Allah za'a kiyaye. Shiga cikin gidan sukayi gabadaya inda su suka nufi farlon Galadima,domin muddin Abbie da Daddy na garin sun shigo to a farlon Galadima akecin abinci,shiko Sauban kaitsaye apertment dinsu yanufa. Da sallama yashiga cikin farlon hayaniya yaran dake farlon keyi Amma jin sallamar shi yasa farlon yakoma shiru inda banda sautin amsa sallamar da yayi bakajin komai, 'yan matan kuwa dake zaune ko wacce wayarta tasaqe suka fara boyewa. "Barka da shigowa Bro Sauban!!!abinda 'yan matan suka fara fada kenan,suko sauran yaran oyoyo suka nufoshi suna mai,sai sai suna qarisowa gabansa sukaja birki suna dariya don sunsan basu isa suyi hugging nashi ba donbshi mutum ne wanda befiye son daqunar yara ba. Murmushi yayi iya lebe tare da cewa"yawwa sannunku,ina Ammi take?nuna masa wani dogon corridor sukayi,yamike kenan da niyyar zuwa sai gata tafito. Da murmushi yatare ta yace"sweetheart,dan hugging nata yayi,hararar wasa ta aika masa dashi wacce da alama babbace don zatayo sa'a da Ummie. Murmushi yayi yace"Me Kuma nayi sweetheart?irin wannan harara haka?Ammi tace"Hmmm zaka sani Ina ganin sanda kashigo gidan nan,wallahi Sauban bakajin tsoro zaka sani ne,muje dinning kaci abinci. Dariya yayi tare da dan kamo shoulder dinta suka nufi hanyar kitchen suka shiga,babu wani jimawa ya Sauban ya fito hannunshi rike da plate biyu ya aje akan dinning yajuya baijima ba yafito riqe da ruwan gora cup,zama yayi kan dinning din yadubi inda 'yan matan suke yace"Mashahuda kije kitchen ki amsa abincin su Daddy kikai farlon Galadima,kekuma muneefa kizo kidauki na boddejo,da to suka amsa don kafin ma ya ida maganar suk sun miqe. Sallama akayi tare da shigowa,Kareem ne yashigo abokin ya Sauban da sauri yaran suka nufeshi suna Oyoyo bro Kareem,bude musu hannu yayi duka su ukun suka fada jikinshi,itakuwa inteey kaitsaye inda ya Sauban yake tanufo,ta wutsiyar ido yadubeta don yasan yarinyar mayyanshi ce duk abinda zai mata tananan kwafufe dashi,kusa dashi tazo ta tsaya tace"ouncle mommy na tace zaka siyomin hollandia idan kadawo tace koka manta natuna maka idan batazo daukana ba kai zaka maidani gida. Dago manyan idanuwansa yayi yana duban yarinyar don yana tsananin mamakin wayon yarinyar don inteey bata wuce 4 yrs
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87