Chapter 85
Chapter 85
so taji ya....a ciki,shiyasa ya koma yi a waje. Sai wajejen magrib sannan ya maido ta gida,hararar kawai Ammi ta masa inda tace"to lallai Zuhra ta koma ɗakin ta don ba za'ayi abin kunya a sashin ya ba. Laulayin cikin na damun ta don ma ta samu sauƙin jirin sannan Dr jamila tana iya ƙoƙarin ta wajen bata kulawa,ranar Laraba Sauban yayi mata kyautar motar ta ƙirar MERCEDES_BENZ G - CLASS G500 MODEL 2022,babu wanda beyi farin ciki ba don motar babu ƙarya ta haɗu iya haɗuwa,ƴan uwa hakan suke kira suna taya Zuhra murya,da yake su Aunty labeeba duk basu tafi ba,kai kowa da murna yake, Zuhra kuwa jitayi kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta shiga,don koda wasa bata taɓa kawo za'a siya mata mota nan kusa ba,ba wai don babu ba a'ah sai don ko maganar sam basuyi dashi,ya bata a matsayin tukwici akan abubuwa da dama a cewar sa ma harda baiwar da Allah ya mata. ******* After one week gidan kamar ba'ayi sha'ani ba don duk sun wawwatse,inda Sauban shi ya cigaba da rainon cikin Zuhra tare da yimata duk abinda takeso,aikin gida ma kuwa tare sukeyi,shi yake kai ta school ya ɗauko inda da haka yake mata dubarin koya driving,weekend kuwa me gasken sukeyi, sosai Sauban ya dage da koya ma Zuhra driving Kuma lokaci guda ta iya,duk wanda ya gansu sai yaso kasancewa tare dasu,ranar da zata dawo daga school haka suka ci karo da Akeela inda wani me daidai ta sahu ke ta mata rashin mutumci kan kuɗin da tabashi be kai ba,har yana kiran ta ƴar maɗigo sai wulaƙata ta yake mutane har sun fara taruwa. Akeela kuwa sosai take kuka,idan ka ganta duk tayi laushi tunda bata rame ba,kawai da ka kalle ta zakasan lallai Akeela ta tuba tayi nadama,long hijjab ne a jikinta , gabaɗaya tayi sanyi, Zuhra da kanta tafita taje ta ƙwato Akeela don Sauban hanata yayi ita kuma taƙi, a motar tazo ta sanya ta,inda kuka sosai Akeela keyi, ta buɗe hand bag ɗinta takaima me adaidaita kuɗin da ita kanta bata san ko nawa bane, sannan tazo ta shiga sai lallashi Akeela take, sauvan ko yayi kicin kicin da face,babu alamun rahama ko kaɗan,nan Zuhra ta shiga bata baki har gida suka kaita, Zuhra na ƙoƙarin fita Sauban ya galla mata uban harara hakan yasa dole ta haƙura, Akeela buɗe motar tayi sannan ta zagayo ta dubi Sauban tace"Don Allah Sauban ka yafemin nasan ni mai lefi ce a gare ka,naci amanar ka amma Allah sheda ne na tuba,tuba irin na taubatun-nasuha don Allah ka yafemin"tayi maganar tana fashewa da kuka, Sauban yace"Allah ya yafe mana,ai ke yanzu duniya ma ta isheki"yana gama faɗar hakan ya zuge glass's ɗin motar ya mata key,beyi wata² ba ya fisgeta ya bar layin,wani irin kuka Akeela keyi don harga Allah tasan cewa lallai ta cuce kanta rashin Sauban matsayin miji asarar ne. 1months Sauban yayi suna zuba soayyayn su daga ƙarshe ya tattara yana shi ya nashi ya koma,wanda Zuhra taji kamar tayi ta kururuwa. ____________ Sauban koda ya koma sau biyu ya dawo a lokacin har anyi azumi har anyi babban salla don lokacin Zuhra cikin ta kusan six months ne dawowar da yayi na farko,cikin yayi girma na hankali duk wanda ya gani sai yayi magana,a lokacin da ya cika seven months wani kumburi Zuhra tayi kota ko ina,ga damuwa da ta sanya ma ranta na mutuwa,ita a kullum gani takeyi mutuwa zata yi hakan yasa lokaci guda jininta ya hau,sosai su Daddy ke mata faɗa don ransu ya ɓaci,gashi wannan karan da yake sun samu hutu har na wata guda hakan yasa duk inda ta zauna sai ta tsaya ma kowa a rai kowa na jinta,ita kanta Boɗejo wani nan nan takeyi da ita,haka Ummie itama sosai ke nuna mata kulawa, ɗaki guda suka cika da kayan baby unisex,don Sauban duk kayan da akasaa ɗakin daga abrod ne. A lokacin Mashahuda ta haihu baby boy ne hakan yasa yaci sunan Abbie suna kiran sa da Ashraf, hakan yasa tadawo gida bayan anyi suna acan,don ko sunan Zuhra bata je ba Sauban ya hanata,shiyasa bata da aiki kullum sai na tambayar Mashahuda yaya haihuwa yake da zafi ko kuwa? Sometimes Mashahuda murmushi takan mata tace"kada ta damu idan lokaci yayi zataji don shi haihuwa ba lallai wahala da wancan ya sha ba shi wannan ke sha,wani yana zuwa masa da sauƙi"kowa cikin tattalin ta da nuna mata kulawa. Sai alokacin Muneefa ta samu ciki na wata huɗu,inda daga Laila har Nihal ke ƙunshe da cikin su ɗan wata bibbiyu. Rammat itama haihuwa yau ko gobe. Haka rayuwa ta cigaba da daɗi babu daɗi har Rammat ta haifi Baby boy inda mahaifin Kareem ya sanya masa sunan Daddy suna kiran sa Aslam. ******** Bayan wata biyu lokacin Sauban ya dawo gida gabaɗaya saboda Zuhra cikin ta ya shiga watan haihuwa,sosai ta sake kumbura sai dai anci Sa'a jinin ya sauka,kullum da la'asar sai Sauban ya jata zuwa struggling hakan yasa yake ɗan jin dama dama. Wata ranar Lahadi ƙarfe 11 na dare naƙuda ya sako ta gaba,tun tana abinta ita kaɗai har Sauban dai ya tashi dama baccin sa rabi da rabi ne hankalin sa na kanta always. "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un"ta furta tana yarfe hannu tare da duƙewa,cikin azama Sauban ya diro daga kan gadon a gigice ya nufeta yana faɗar haihuwa ce Baby? ɗaga masa kai Zuhra tayi ta kasa magana saboda azaba. Hakan yasa a gigice Sauban ya fice daga gidan ƙoƙarin fita yake but ya kasa hakan, gabaɗaya ya gama ruɗewa da gigice wa lokaci guda. Wayan shi ya ɗauka ya lalubo number Ammi,kusan 2misscall sannan ta ɗauka muryan ta da alamun bacci tace"Assalamu alaikum Sauban ya akayi? "Ammi Zuhra kizo don Allah"cikin sauri Ammi ta miƙe tace"haihuwar ce? Sauban yace"i think cuz tana shan wahala"Ammi ce tayi hanging call ɗin, Daddy ma tashi yayi,hakan yasa cikin sauri ta nufi apartment ɗin Mom ita da Daddy, Daddy da kanshi ya kira Baba Hasheem a waya ya sanar dashi,babu jimawa suka fito shida Mom ko wacce zani ɗaure akan kayan bacci tasa hijjab. Wayan Ammi ne yayi ringing cikin sauri ta ɗaga Sauban yace"Ammi ganinan a mota a waje". Amsa mishi tayi sannan suka fice wajen su suka shiga inda su Daddy suka ce duk halin da ake ciki su sanar dasu. Sauban kiran Dr Ahmad ya sanar dashi,inda akayi Sa'a Dr yana asibitin cuz night duty zaiyi. Suna Isa cikin hanzari aka karɓe ta sai labour ward. Nan fa aka shiga bata kulawa gabaɗaya Sauban ya ruɗe,cikin yardan Allah wajejen 3:00 ta sunkutu yaran ta biyu mace da namiji,ihun su ne ya cika ward ɗin. Aifa nan su Ammi sukaji sanyi ya ratsa musu,babu jimawa Dr jamila ta ƙarisu hannun ta ɗauke da Baby wata nurse ma ɗauke da Baby,atake anan Sauban yayi sujudur shukur,inda banda hamdala babu abinda su Ammi keyi, Sauban cikin sauri yace"yaya take?zan iya shiga na ganta?cikin sanyin jiki Dr jamila tace"dama tace"akira mata kai, Ammi tace"muma zamu iya shiga? Dr Jamila tace"Ea ai angyara ta". Koda suka shiga a kwance suka taradda ita inda sai murmushi takeyi,hannu ta miƙa ma Sauban tace"Yaya kaga Babyn mu ko?nasan ni ba
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87