Chapter 40
Chapter 40
bane,kawai mutanen mu na yanzu rashin wayewar kai ta musu yawa ne shiyasa,hajiya daharatu dake rike da hannun amarya tadubi yarinyar wata busasshiya da ita taci mai ta kwaile tace" 'Yar caras kashe mp nan mana. Kashewa tayi suka shiga katon gidan wanda da damansu sai da suka raina kansu atake anan wasu hassada ya darsu musu sukaji inama ace sune suka shigo cikin wannan ahalin, lallai Akeela ta dace saurasu,wasu kuwa da yake ba auren ne a ransu ba hakan be wani damesu ba sai dai suma sunji sha'awar kasancewa a gidan. Tundaga yanda Galadima family sukaga amarya da kawayenta sukeyi suka san lallai basuyi dace da sirikar kwarai ba amma ba anan gizo ke sakar ba kila tana da wasu halayyan, Ammi kuwa tayi bala'in jin kunyar kallon Akeela a matsayin sirika,don ko rufe fuska batayi ba,sai dai baka isa kagane hakan a face dinta ba Saboda murmushin da take tayi,tsakanin Rammat dasu Suby kuwa banda kallon banza babu abinda suke aikama juna,nan aka gama mata nasihohi aka fito da ita tare dasu Aunty Maryam don kaisu gidan amarya dake jikin nan gida,koda suka isa nanma mutanen Akeela sun raina kansu don ita da kanta ware ido tayi tana kashe kwarkwatan idanuwan ta. Barosu su Aunty Safeena sukayi bakunan su cike da abubuwan mamaki tare da tausayin Sauban don da alama zasu wahala. Bodejo ce tanufi dakin don dauko furar da ta'aje ma yallabai๐Turus tayi saboda ganin mutum da tayi kan gado"Wanene nan?shiru taji,dan matsawa tayi cikin tsoro tasake cewa"Nace Wanene nan?ina magana ana jina eyye?mutum ko aljani?wallahi ko aljanuni sharri na yafi naku, hatsabibanci na yafi naku"takarisa maganar zuciyar ta fal tsoro shahada tayi ta yaye duvet din, Zuhra tagani banda rawar sanyi babu abinda jikinta ke mata,da sauri ta taba goshinta,gau haka taji shi da zafi sosai"Oh ni fatsima dama yarinyar nan kina sashin nan kikazo kika boye kina neman kashe kanki da ciwo?kinji jikin ki kuwa?tayi maganar tana bubbuga mata jiki. A wahalce tadan bude idanuwan ta,tanajin wani irin azaba,sake lumshe idon tayi cikin tsananin azaban da takejin kanta na mata kamar zai rabe biyu. "Ke Zuhra tashi kizauna lafiyanki kuwa?meke damunki ne haka?kinji yanda jikin ki yadauki zafi gau?gaskiya ba lafiya ba bari nazo,tayi maganar tana fita batare da tadauki abinda tazo daukan ba,ko minti goma bata kara ba tadawo ita da Taufeeq dasu Aunty Maryam,suka shigo,duk cikansu nufar gadon sukayi"Taba jikinta kaji Taleeb,zazzabi ne mezafi ya lullubeta"Bodejo tayi maganar,hannu yadora akan goshin nata,da sauri ya cire"Kai gaskiya kuwa, Aunty labeeba tace"Zuhra!Zuhra!!tayi maganar tana tabata. A wahalce tadan bude ido tasake lumshewa,dagota Aunty Maryam tayi tasa kanta a cinyar ta tace"Zuhra bude idanuwanki, Zuhra"Uhum! Abinda tace kenan tana rufe idon ruffff "Ikon Allah jikin nata ya canza mata ne lokaci daya,duban Aunty Maryam Taufeeq yayi yace"Aunty ya kamata muje asibiti da itane ko? Aunty labeeba tace"Gaskiya kam don wannan zazzabin ya bigeta gaskiya,dagata.Kamata sukayi suka mikar da ita,jikinta babu inda baya rawa saboda sanyin da takeji,face din har wani pink pink yake na wahala,wani mahaukacin amai ne taji yazo mata,ai kafin kace me tafara kelayarwa,haka jikinta ke cigaba da rawa,amai take sosai,sosai su ma hankalinsu yatashi,cikin muryan kuka take fadin"Abbie!Abbie!! Kamata sukayi ai ganin zata wahala ga jikinta yayi bala'in saki wani yaraf kawai take yasa Taufeeq cak yadauketa,biyosa sukayi,anan ma parlon ragowar 'yan biki suka taso ana tambayar lafiya?kowa yaganta yanda ta canza sai ya tausaya mata. **** Daddy ne da Abba da Baba Hasheem suke farfajiyar gidan da alamun daga masallaci suke,gefensu Sauban ne kansa a tsaye,gani sukayi mutane duuuu sun fito daga apartment din Bodejo, Taufeeq dauke da mutum a hannu,cikin tashin hankali suka nufi wajen suna tambayar abinda ke faruwa,a rude Taufeeq ke tambayar ya Sauban akwai car key a hannunsa?batare da yabashi answer ba yayi saurin nufar motar sa yana mata key, banda bugawa babu abinda kirjinsa keyi,tambayar kansa yake me kuma ya sameta?batare da yasan maganar zucin da yayi tafito ba yaji Aunty Maryam na bashi answer"wallahi muma haka muka sameta a sashen Bodejo,sakata a motar Taufeeq yayi yana zaunar da ita kanta akan kafadar Aunty labeeba, Aunty Maryam ma tashiga,da sauri Ummie takariso a rude take sai tambayar inda zuhran take takeyi,tayi matukar rudewa,haka Ammi dasu Mom,nufar dayan motan tayi tana cewa Taufeeq ya tada"No Ummie ki zauna a gida insha Allah komai zaizo da sauki,wani kallo ta aika masa dashi jikinta yana rawa cikin rawar murya tace"Ace min ka dauko 'yata kamar gawa?shine kake tunanin zan iya samun natsuwa?lallai Taufeeq baka da hankali"cikin daga murya tace"kabudemin mota nace! Bude mata motar yayi Saboda ganin yanda ta canza lokaci daya,Ammi ma tashiga,Adda Zainab ne tabude bayan itama da sauri tafada banda salati babu abinda takeyi,nan fa kowa yayi jugumยฒ. Su Laila kuwa sai kuka da kuka Saboda a yanayin da kowa yaga anfito da ita hankalinsa dole yatashi,a 360 Taufeeq ya figi motar,tuni securities din gidan suka wawwangale gate din. "Ya Allah ya tayar da kafadunki Fatima, Amma ta fada hakan tana me juyawa,lallashin su Laila Rammat ta shiga yi tana yimusu fadan so suke su sake tayar ma da mutane hankali?su yahakuri insha Allah zata samu lafiya. Koda labarin ya isa ga Akeela sosai tayi farin ciki da hakan don har addu'ah tayi kan Allah yasa kada ma ta tashi daganan ta mace kota huta da kallon ta tana kwasar takaici da haushi. Xahratty Ce๐ฅฐ Lallai Alqalami ๐๏ธ yafi takobi๐ก๏ธ. 9/6/23. [6/11, 12:36] Xahratty (OUM AJMAL): ๐จ๐ฝโ๐ฆณ *_GALADIMA FAMILY_*๐จ๐ฝโ๐ฆณ Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyarโคต๏ธ A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page 47/48 ๐พ๐จ๐ต๐ต๐จ๐ต ๐ท๐จ๐ฎ๐ฌ ๐ซ๐ฐ๐ต ๐บ๐จ๐ซ๐จ๐ผ๐ฒ๐จ๐น๐พ๐จ ๐ต๐ฌ ๐ฎ๐จ ๐ด๐ผ๐ฏ๐จ๐ด๐ด๐จ๐ซ ๐ฒ๐จ๐น๐ฌ๐ฌ๐ด,๐ฎ๐ถ๐ซ๐ฐ๐๐จ ๐ด๐จ๐ฐ ๐ป๐จ๐น๐ฐ๐ต ๐๐จ๐พ๐จ ๐จ๐ณ๐ณ๐จ๐ฏ ๐๐จ๐ฉ๐ฐ๐๐จ ๐ด๐จ๐ฒ๐จ ๐ฉ๐ผ๐ฒ๐จ๐ป๐ผ๐ต ๐ฒ๐จ ๐จ๐ฒ๐จ๐ต ๐ต๐ผ๐ต๐จ ๐ฒ๐ถ๐ฒ๐จ๐น๐ฐ ๐ซ๐จ ๐ฒ๐ผ๐ณ๐จ๐พ๐จ ๐จ๐ฒ๐จ๐ต ๐ฉ๐ถ๐ถ๐ฒ ๐ซ๐ฐ๐ต.......๐จ๐ต๐ฎ๐ถ๐ต ๐น๐จ๐ฏ๐ด๐จ(๐น๐จ๐ด๐ด๐จ๐ป) ๐จ ๐ฉ๐ถ๐ถ๐ฒ ๐ซ๐ฐ๐ต ๐ฎ๐จ๐ณ๐จ๐ซ๐ฐ๐ด๐จ ๐ญ๐จ๐ด๐ฐ๐ณ๐๐ ______wani Private hospital suka isa me kyau da tsada da alama nanne asibitin da ahalin suke hidimarsu,da isar su kuwa nurses din asibitin suka sanya ta akan gadon marasa lafiya kaitsaye emergency ward aka nufa da ita,likitoci uku ne suka tsaya akanta gefe guda kuma nurses biyu,su kuwa ahalin banda zarya babu abinda suke a dan dogon corridor din ward din sauran kuma duk sun zazzauna,idan ka kalle fuskokin su cike da alhini banda shi da yake zaune ya lumshi ido tare da jinginar da kai a jikin kujerar da yake zaune. Sunanan dai zaune har 9:30 amma babu wani likita da ya fito bare a musu cikakkiyar bayani,dubansu Daddy yayi ya soma magana"Ku tashi kuje gida dare nayi muzamu jira har Doctors din su fito muji abinda ke wakana,matan ku koma gida"yakarisa maganar yana juyar dakai gefe daya. Ummie ce tadago da niyyar yin magana amma sai takasa don Allah yasani tana tsananin girmama Daddy don musu bai taba hada ta dashi ba bare gaddama,cikin sanyin jiki suka mimmike,kallon Daddy Ammi tayi tace"Amma Daddyn su day kun bar daya a cikin mu ko kun manta cewa dole macece zata maida hankali wajen kula da ita?fuskan Daddy babu wani wasa yace"babu bukata zaku iya tafiya ga Sauban nan inma anbata gado zai zauna da ita ya kula da ita"Cikin mamaki suka dago suna dubansa,shima da sauri yabude idanuwan sa yana duban Daddyn nasa.Aunty Maryam tace"amma Yaya kamar hakan be kamata Saboda
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87