Chapter 4
Chapter 4
ta bangala tare da karkada kafafuwa. Abbie ne yayi ajiyar zuciya yace"insha Allah za'a ma bullowa lamuran komai zai daidaita. Cike da masifa guggo Laure tataso mishi kamar zata dakeshi tace"toh karere kayahakuri badakai ake magana ba tukuna, Kuma bamaga ake akan danka taufeeq ba. Da mamaki duk suka dago suna dubanta,bodejo ce tabude baki da niyyar magana Amma sai Galadima yakatseta ta hanyar fara magana"Laure kenan har yanzu rashin iya maganarki yananan,kinada shekaru sittin da wani abu kina shirin cika saba'in Amma ace baki iya kalamai masu dadi ba?ai abubakar yafi karfin karere tunda jinina ne nine nan nahaifeshi kuma Sauban danshi ne tunda dan Dan uwanshi ne kingako yafi karfin karere a ciki. Yayi maganar yana me miqewa tare da gyaran sandar sa,duk miqewa sukayi harda bodejo ta gyara mayafinta tace"ai kafata kafarfu don nima zan wuce Laure dai taji sauqi,tayi maganar tana aikama da guggo Laure harara,inda itama akaikaice ta rama sam bazakace su din tsofaffi ne ba. Duqawa su Daddy sukayi har qasa tare da mata sallama Kuma kowannensu sai da ya ajemata kudi, murmushi tafara tare da samusu albarka tana memikewa. Harara bodejo ta aika mata dashi a fili tace"daso samune kadama a amsa na karere,duk cikansu sun fahimci abinda bodejo ke nufi amma kowanne ya basar. Guggo Laure kuwa tace"ai dadin abin ma na 'yayan Dan uwa nane. Ko wanne a cikinsu dariya suka sanya banda bodejo wacce dama duk ta rigasu fita,sai da akazo tafiya ne sukaga cewa motar bazai ishesu ba duk da cewa ba wani girma ne dasu ba Amma ko babu komai zasu so mutumta iyayen su susakasu a wake guda,motan Alhaji sani ne tashigo farfajiyan gidan da sauri ya fito daga cikin motan cike da muntuntawa,domin Daddy da Abbie da Abba duk sun girme mishi. Kai tsaye wajensu yafito fuskansa dauke da tsantsar fari'ah,cike da ladabi yaduqa yana gaishe da bodejo da Galadima,sukuwa sauran mazan hannu yamiqa musu tare da musabaha yana dan tsokanar su abinka da abokan wasa. Duban Galadima da bodejo yayi yace"Kawo ku shigo na maidaku gida a cikin tawa motar.Haka kuwa akayi don Kai tsaye suka shiga motocin biyu suka nufi old maidugri don ba wani nisane dasu tsakaninsu da gidan direbi ba. A garin kaduna kuwa zuhra ce tsaye a bakin kofan shiga farlon nasu sai dai ta kakire a tsaye ita bata shiga ba kuma ita bata juyawa ba inda ka kalli fuskanta kuwa zaka sha mamakin irin mugun kallon da take watsama wanda ke tsaye a bakin kofar. "Please ya Aseef ka kama mutumcinka don ina ganin mutumcinka ba kuma zan iya maka rashin kunya ba Amma inaso kasani nisam ba irin watsattsun matan da kake tunani bane.Tayi maganar cike da fusata. Matsowa Aseef yayi inda take tare da fara lasan labba yace"zuhra kenan 'yar kakkyawan kanwata kina tunanin bansan irin sheqe ayar da kikeyi bane?duk gidannan anhanaki saka English wears Amma kinki ji,idan zakisa kisa na mutumci mana irin wanda su Laila ke sawa Amma kinasa abu jiki a dame kiyi tunanin ire-ire na bazamu bibiyeka? Wani dogon tsaki taja saboda yanda ranta yayi qololuwan back,wanda kuma yayi dai² da isowar Ummie wajen zata wuce. Da sauri Ummie ta juyo tana duban zuhra cike da mamaki tace"zuhra!Ashe dama rashin kunyar taki har takai haka?kidubi idon Aseef kiyimasa irin wannan tsakin?saboda yace yana sonki?so hauka ne da har haka zai baki damar yimasa rashin kunya?to bari kiji zaki sha wuya a cikin gidannan muddin bazaki dena rashin kunya ba. Kai kuma kada son da kake mata ya rufe maka Ido ka kasa hukunta ta ka zaneta to nonsense ni nasa,mara kunyan banza kawai.Taqarisa maganar tare da gyara zaman medical glass dinta tana wucewa apartment dinta kaitsaye. Wani kuka ne ya tahoma zuhra saboda tsananin takaici tarasa menene tayiwa Ummie take nuna mata irin wannan tsaanar sam bata jawota a jiki irin na uwa da da,anya kuwa Ummie ce tahaifeta?a ranta tayiwa kanta wannan tambayar. Shiko Aseef cike da murna yayi wani irin murmushin gefen lebe yajuya yanufi BQ nasu kaitsaye. A haka ya taufeep yashigo ya iske zuhra da sauri yayi parking din motar sa yafito tare da karisowa inda take,miqar da ita yayi yace"me akamiki zuhra ke da wanene?bude baki tayi da niyyar masa bayani Amma ina?tuni kuka yaci karfinta. Lallashinta yashiga yi har yasamo tayi shiru banda ajiyar zuciya babu abinda takeyi. Kaitsaye apertment din Ummie yanufa cikin disasshiyar murya zuhra tace"zanje bangaren mommy ne. Ya taufeeq yace"Ok muje,shiga farlon sukayi sallama dauke a bakin taufeeq,sun cidda mommy dasu Laila,gefe guda kuma ateek ne ke wasa shida maimoon,da gudu yaran suka taso suna hugging din zuhra da taufeeq,daga ateek ya taufeeq yayi sama yaron na qyalyqalewa da dariya. Jikin mommy zuhra tafada tare da kara fashewa da kuka,a hargitse mommy tafara tambaya"A'ah taufeeq meyasameta daga dawowan ta jamb class dinnan? Murmushi ya taufeeq yayi yace"shagwaba gurl! Mommy kenan nafa rarrashe ta tun a wake kafin munshigo dama nasan shagwaban nata akanki zai kare. Hararan wasa mommy ta wurga masa tace"Allah taufeeq ka kiyayeni me aka mata kuma? Yace"ai kinsan halin 'yar mulkin taki ko nima rarrashin ta nayi batare da nasan ko dawaye neba don na tambaye ta bata fadamun ba. Dariyar qasa² Laila tayi tace"ko dai ita da Ummie ne? Zuhra kuwa kaman antsikare ta tadago tafara zayyane ma mommy abinda yafaru a waje tanayi tana kuka tace"Kuma wallahi ya Aseef dinnan dan iska ne gwara na konawa na gidan Galadima saboda nagaji. Gabadaya dariya suka saka,nihal tace"chabdi saboda wani nabar gidan mu gaskiya I can't kema fah kamar harda rashin fahimta da yashiga tsakaninku kedashi. Mommy kuwa tace"tabbas nihal ninarasa gabadaya irin wannan abu haka tsakaninsu gaskiya taufeeq kayima Aseef magana matsayinka na wansa nisam banga amfanin hakan ba. Ya taufeeq tace"sudai suka sani ai idan ma bazasu dena ba sai aje wajen Ummie don itace zata bulloma lamarin. Zuhra ta zunburo mouth gaba tace"ni bazanje wajen Ummie ba,Ummien ma da goyon bayansa take ni kullum cikin lefi nayi mata,wallahi Abbie zai dawo shizan fadawa don ma wayana babu credit ne kuma bani da kudi a ccount dina bare na siya dana kirasa na fada masa. Ya kabani wayarka nakira shi kaji? Harara ya taufeeq ya zabga mata yace"ni?lallai yarinyar nan bada wayata ba,sai akace miki nima mara hankalin ne irinki koh?ga dai mommynki nan ki amsa tata...da sauri mommy tace"wah don Allah taufeeq ka rufamin asiri sai kuma akace bamu da tunani gabadaya? Dariya su Laila suka sanya,zuhra kuwa a fusace tamike tafita daga farlon. Gabadaya dariya suka bita dashi. Koda tashiga farlon su bata samu Ummie ba don haka kaitsaye bedroom dinta tashiga tare da fadawa akan kayataccen gadon ta tafashe da kuka,itasam takan rasa abinda ke mata dadi sam ita da gidan su da mahaifiyar ta araye amma kamar wacce take mara uwa(niko nace hmmm zuhra kenan nibanga abinda akai miki nakaman rashin uwa ba.) Xahratty Ce 🥰 Lallai Alqalami🖊️ yafi takobi🗡️ [3/21, 22:27] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽🦳 Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar⤵️ A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page 04 _Bismillahir-rahmanir-raheem._ _____Haka zuhra takarisa tunane tunaneta tamiqe tashiga toilet ta dauro alwalan sallan magrib kaman yanda taji anata kiran
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87