Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 59

Chapter 59

Galadima Family Book 1 Complete Hausa Novel 1,370 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

mamaki suka tsaya duban ta parloun yayi tsit bakajin komai sai gunjin kukan ta, Mom ce fuska a daure tace"Amma wannan yarinyar anyi ja'irar banza, Kinga wallaphi kikeyaye mu,idan baki son auren mu munaso aikin banza kawai"Mom tayi maganar tana jan tsaki,sosai Zuhra take kuka wanda yasa jikin Ammi yin sanyi,mikewa tayi ta isa ga zuhra ta kamo ta tace"kiyahakuri Zuhra kinga mahaifinki wasiyya yabari na auren ki da son,ki temaka ki aure sa,inaji a jikina ke alkhairi ce agaresa"Ammi tayi maganar tana murmushi Wanda sosai tabama mutanen parloun tausayi, Ummie kuwa a fusace ta taso domin idan bata daki Zuhra ba bazatayi sukuni ba,ganin haka yasa Zuhra fusge hannunta ta nufi dakin da take zama,cikin muryan kuka tace"wallahi banason sa"kamo hannun Ummie Ammi tayi tace"Menene zakiyi haka bilkisou?wai meyasa kina mantawa da zuhra yarinya ce?dole a bita a hankali fa, menene amfanin abinda kike shirin yi? Ummie cikin bacin rai tace"Haba haba Ammin yara Zuhra ce yarinyar?hmmm taga ana lallabata ne"Mommy tace"babu maganar lallabo Aunty bilkisou gaskiya ne zuhra yarinya ce,so sai anbita a hankali,cikin bacin rai Ummie tabar apartment din, Mashahuda da Muneefa ne suka shiga bedroom din da Zuhra ta shiga, Aunty muneefa cikin bacin rai ta dubi Zuhra"yarinya ina guje miki ranar nadama,wai kuwa kinsan waye ya Sauban?kin kuwa san yanda mata suka rikece akansa?mata da dama sun mutu a son sa wallahi idan kika auresa keda kanki sai kinyi alfahari da auren",cikin kuka Zuhra tace"nidai bana son sa,meyasa Abbie zai yanke wannan hukuncin?i know Abbie bazai taba zabamin mijin da zai cutar dani ba,sai dai why not zuciya ta takasa amincewa dashi matsayin miji,bazan iya yarje ma batun iyaye nabaaa.....takarisa zancen tana sakin wani irin kuka me tsuma zuciya"meyasa aure na yazo a haka?duban Aunty Mashahuda tayi"Aunty Mashahuda meyasa baza'ayi irin shagulgulan da akayi a naku ba,bikin ku is d best biki a wannan year din"dafa ta Mashahuda tayi tana murmushi tace"bikinku ya fita daban dana kowa,kiyarda cewa rayuwar auren ku ne kukuma zai zama abin kwatance, cuz Allah zai albarkaci aurrn ku trust me"shiru Zuhra tayi tana jan ajiyan zuciya, Laila tayi dariya tare da cewa"Aunt duk fa munafunci ne itama tana son Yaya, amma zuciyar ta takasa yardan mata da haka, Nihal itama dariyar tayi tace"wallahi kuwa hhhhhh"a fusace Zuhra ta dubesu"Ni banson sa bantaba son sa ba,mutum daya naso a duk duniya akan shi nasan menene so,wato ya Shuraim.....Tasss! Karar mari ya sauka akan kumatun Zuhra,huci kawai yakeyi idanuwan nan sunyi jajawur,cikin sauri Mashahuda,muneefa, Laila, Nihal suka bar bedroom din, Sauban kuwa banda rawa babu abinda bakinsa yake masa,cikin muryan tsawa ya nuna Zuhra"ke...kk..kkee da aure na akanki kike fadar kina son wani?yayi maganar yana nufo Zuhra yana huci,girgiza kai Zuhra keyi"A'ah yaya don Allah kayahakuri bazan sakeb......hannu ya dunkule kamar zai kaimata punch,sai kuma yakaima wall din bedroom din,ita kuwa runtse ido tayi jikinta na rawa,juyawa yayi yafita,cikin takunsa wannan karan dai-dai da tafiyar cikin fushi yakeyi. Mommy ce tashigo dakin cikin sauri,kamo Zuhra tayi"Wai ke bakida hankali ne?sai yaushe zakiyi hankali my Zuhra,kike fadar bakison mutum agaban mahaifiyar sa gatsal haka?cikin kuka tace"Mommy shima fa baya sona"cikin fusata mommy tace"inji uban wa ya fada miki haka? kuka Zuhra ta fashe dashi hankalinta a tashe sai dai takasa furta komai,kukan kawai takeyi,ki tashi kije ki shirya zakije saloon,cikin sanyin jiki ta mike ta fita,babu kowa a palourn na bodejo,kaitsaye apartment din Ummie ta wuce,a palourn kasa ta taras da ita da Taufeeq suna magana,sallama tayi duk suka amsa sannan ta haye stairs,shiryawa tayi cikin riga da straight skirt,harta dau mayafi tasa kome ta tuna?sai kuma tanemo after dress ta dora akan kayan tafita. Duban ta Ummie tayi"inane zaki haka?cikin sanyin ta tace"Mommy tace nashirya nazo za'a wankin kai"daga mata kai Ummie tayi,hanya ta Kama har takai kofan palour tajuyo cikin raunanniyar murya tace"Ummie ki yafemun"tana karisa fadan haka da sauri ta fice. Sai la'asar suka dawo daga wankin kan,a lokacin ne kuma me henna ke jiranta,abinci taci tayi la'asar sannan Aunty Labeeba da Mommy suka fara yimata dilka,bayan an gama aka mata wankan lalle, fara shiryata cikin wata hadaddiyar net wanda aka mata dinkin wedding gown,blueblack tayi kyau dinkin ya hadu,me make-up tafara zane mata face dinta,light make-up aka mata,tayi balai'n kyau,fito da ita akayi farfajiyan gidan,kanofi ne guda uku,mutane ne zazzaune daga familyn gidan,sai makota da kawayen matan gidan don abune da akayi a kurarren lokaci,anyi decoration din filin sosai,kaitsaye aka kaita wajen rumfarta wanda yayi balai'n haduwa da tsaruwa sai wani walwalin wuta ke tashi ajikin wani rubutu ansa *_HENNA DAY,HAPPY MARRIAGE LIFE, MUHAMMAD TALEEB MUHAMMAD&FATEEMA SADEEQ MUHAMMAD._* Zaunar da ita akayi a hadadden carpet din dake wajen,gefe me lallen ne,aiko nan tashiga yima amarya lalle,sosai kida yafara tashi tare da gude² na farin ciki,haka me lalle ta cigaba har tagama na kafa ja dana hannu,anfara baki a kafa.....sautin kidan ne ya canza salo,nan Mc ya fara sanarwa"Ga ango nan ga ango nan don Allah a bashi waje,Zuhra kuwa zuciyar ta kaman tayi tsalle tafito,nan kuwa aka saki waqar illela bille illela,lamshi sharahni,sosai kidan ke tashi,ya Sauban ne a gaba cikin wata mahaukaciyar boyel blueblack,sai bakar zanna bukar,kafansa wani hadaddiyar covershoe ne kirar gucci baki,hannunsa dauke da agogon Cartier, yayi bala'in kyau,murmushi yake wanda yakara fito da ainahin kyansa,sosai aka fara tafi da ihu,bayansa abokan sa ne 'yan nan maidugri su biyar sai Taufeeq,Kareem,da Aseef su kuma cikin fararen boyel,kaitsaye wajen Zuhra ya nufo,nanfa yashiga watsa mata daloli,sai da ya watsa mata fin dari,ihu ne kawai ke tashi na mutane,hannu ya mika ya Taufeeq ya saka masa meant na 1000 aiko ballewa yayi yana watsa mata,aiko waje yasake kacamewa da ihu,Suma ya zuba sosa,dukawa yayi dai-dai saitin kunnenta inda kanta ke duke ya fara magana cikin rada tare da kamo hannunta"kinyi kyau matata sosai,am proud of you my beauty"cikin sauri ta dago,don tabbas jitake kamar tana mafarki,a dai-dai nan aka fara daukan su hotuna,waje nasake cika da ihu,nan yaja tawagar abokan sa suka bar wajen,aiko cigabawa akayi, ba'a watse ba sai wajejen 9:30 sannan. Cikin matsanancin gajiya Zuhra take,lallabawa tayi tanufi bedroom dinta ta rufe sai bacci,sosoai Sauban yaso ganinta amma ina Zuhra tayi bacci. ****** Washegari cigaba akayi da shirye-shirye duk da kuwa botsarewan da Zuhra keyi domin daru sosai tasa kan naqin auren,sai da Baba hasheem ya mata hauka² kana tashiga taitayin ta,karfe biyu akafara walima zuwa la'asar angama duk anwatse sai yarage gidan sai iyasu ahali,da yake Amma ma ta iso tare da matan yayyen Ummie da kannen ta,haka dai aka cigaba, hayaniya ce ta fara tashi,a dalilin shigowan Guggo Laure gidan. "Munafukan banza munafukanp wofi,ai dama tun tuni nasan Yaya Bodejo ta tsaneni tatsane jinina, Allah sai ya yimin sakayya tsakanina dakuu"takarisa maganar tana sakin kuka,tsit gidan ya dauka kowa yayi cirko-cirko, Akeela kuwa wajen Zuhra ta nufa tare da nuna ta da yatsa tana huci"matsiyaciya nadawo kanki,'yar iska karuwa kawai,dama tuntuni na fahimci manufar ki akaina kina kokarin rabani da farin cikina karuwa kawai"tayi maganar Cikin karaji,murmushi Zuhra tayi tana duban Akeela"Hmmm Akeela kike da suna ko wane?I don't have time for you cuz ni din nafiki ajiki,kima da kuma mutunci,niba 'yar iska bace,kuma ba karuwa bace,abarshi ma a hakan haka nake,ai gara karuwa da 'yara madigo la'ananniya,domin zunubi da girman madigo ya taka

Table of Contents

Chapters

87 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});