Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 36

Chapter 36

Galadima Family Book 1 Complete Hausa Novel 1,328 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

duka ukun,sai dai shi gogan face nasa a dore,ba kamar taufeeq da kareem ba,duk da shi Kareem na ciki na ciki. Cikin sauri Zuhra ta nufi inda suke sai dai kaitsaye ta wuce Sauban ko kallon sa batayi ba ta nufi wajen taufeeq,kamo hannunsa tayi,"yawwa Yaya ga ya Shuraim can kazo ku gaisa, bata jira mezece ba tafara jansa. Tun kafin su kariso Shuraim ya karisu,cike da girmamawa yadan rissina kadan tare da mikawa Taufeeq hannu yace"Yaya sannu da zuwa,shima Taufeeq face dinsa babu yabo ba fallasa yamika masa yace"sannu ko malam Shuraim ya mutanen gidan? Shuraim yace"kowa lafiya lou Yaya,dubansa Taufeeq yayi sannan yadubi Zuhra,sake maida duban sa yayi ga Shuraim din yace"Ko zan iya sanin matsayin ka a wajen kanwata malam Shuraim? Shuraim na kokarin magana cikin sauri Zuhra tace"he's my friend...tayi maganar tana sakin murmushi,gyada kai Shuraim yayi yace"yes Yaya,murmushi Taufeeq yayi yace"Ok nice to meet yhu malam Shuraim,insha Allah zansa mana lokaci musake gaisawa da kyau,dariya Shuraim yayi cikin jindadi yace"babu damuwa Yaya a shirye nake don amsa kiranka. Taufeeq yace"Ok ka gaida mutan gidan. "Insha Allah zasuji Yaya. Wucewa yayi a ransa yana kissima abubuwa da dama inda lokaci guda ya fahimci inda Shuraim ya dosa,kaitsaye apartment din Ummie ya nufa. "Kingani ba?tun yanzu nafara samun shiga a family naki ko?to dana fito da maitata nasan za'a amince,dariya Zuhra tayi tana kokarin yin magana ne ta hango Laila ta doso inda suke kaitsaye,nuna ma Shuraim Laila tayi tace"kaganta ko?duban inda tanuna masa yayi yace"who is she?dariya Zuhra tayi tace"her name is Laila, she's my lovely sister nd my abokiyar fada,dariya Shuraim yayi itama Laila dariyar tayi don taji amsar da zuhran ta bada,duban Shuraim tayi tace"Barka da zuwa! Dariyq Shuraim yayi yace"Barka dai fatan kina lafiya?ya shirye-shiryen biki? Laila tace"Alhamdulillah shiri ananan anayi sai dai mujira ranar daurin aure,maida dubanta tayi ga Zuhra tace"Ummie na kiranki, Zuhra tace"Okay to bari naje tayi magnan tana duban Shuraim"Ya Shuraim nizan wuce please don Allah kagaishe da mutanen gidan. Takarisa maganar tana me wucewa tabarsu tare da Laila yana janta da hira. Xahratty CE🥰 Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️ 26/5/23. [6/7, 15:49] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳 Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar⤵️ A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page 41/42 ______Kareem ne yadubi Sauban yace"Ango kiran kafa akeyi da alama kawayen amarya ne,kuma nasa akan maganar kudinsu ne"Cikin bacin rai Sauban yace"I don't have time for wadannan 'yan iskan ladies din masu fama da hayakin kai,nine zanbasu 10 millions naira na hidimar biki?to ai banfito a cikin jerin ahalin karuna ba idan har abinda nayi niyyar basu bazai musu ba sai dai subar hidimar da zasuyi. "Calm down! Friend abin bana daukan zafi bane haka,please kabisu a sannu nisam banason abinda zai sanya kabata ma kanka rai ka bata mata ita.... wayar ce aka kara Kira, Sauban ko kalla beyiba duk da face dinsa bazaka ga mahaukacin fushin nan ba,Kareem ne yayi picking call din. Cikin muryan shagwaba tare da karairaye murya,gyaran murya Kareem yayi yace"bashi bane amarya,barka da Rana amaryan bakya lefi koda kin kashe dan masu gida. Batare da gaisuwa ba Akeela tace"uhum Kareem kenan,nace please sweetheart din baya kusane kadauki phone din?dan murmushi Kareem yayi ta hanyar danne bacin ransa yace"aiko baya kusa yabar wayan a dakina ne kafin yaje yadawo but insha Allah idan yadawo zan sanar masa kinkirani"Da sauri Akeela tace"no ba wani abu bane dama tuni akan maganar hidimar kawaye naje haryanzu baku nemesu bane kuma time na tafiya ya kamata abasu abinda kikace. Kareem sosai yasan abokin sa magana daya yakeyi daganan baya canjawa"kingani Akeela abinda yasa bamu nemeku ba maganar gaskiya Sauban yace bazai iya bada 10 millions ba,idan kuma kum matsa sai hakan tofa sai dai ku fasa hidimar taku. Wani kululin bakin ciki da takaici Akeela taji ya ziyarce ta lokaci guda,tanaso tayi rashin kunya amma tsoro ya hanata,cikin karfin hali"Yanzu fisabilillah a ganinka Kareem ya kamata Sweatheart yace bazai bani wannan kudin ba?me akayi akai 10 millions please?meyasa yakeso yamaidani wata karamar yarinya wajen friend's dina?alhalin ansan wanda zan aura Muhammad Taleeb Muhammad nefa haba haba,dage kafada Kareem yayi tamkar tana gabansa yace"to kinji nidai abinda yacemin kenan kije kiyi shawara don yace daga 3 millions bazai kara wani abu b.....batare da yakarisa abinda zaice ba daga bangaren Akeela yaje tace"Kutumar uban can!!! Atake anan kuma wayar ta gimtse alamun ta gane katobarar da tayi kenan.Wani dariya Kareem ya kunshe saboda tabbas tasan Akeela ba irin tsarin macen da abokinsa yakeso bane,dogon tsaki Sauban yayi tare dayin kwafa batare da yace komai ba yamike ya shiga toilet. Acan kuwa gidansu Akeela tabotsare sai masifa take zazzagawa a dakin Guggo Laure tare da kuka,tana fadin itafa Sauban baya sonta,sosai hankalin Guggo Laure ya tashi ranta ya baci matuka amma haka ta danne gudun abinda zaije yadawo taja Akeela cikin dakinta tare da fara kwantar mata da hankali,nan fa tafara lallashinta magana tafara mata kamar haka"inaso ki saurare ni kiji da kyau, ni babban matasalata dake wutan ciki taya bikinki saura kwanaki kifara bacin rai da hayaniya? Cikin muryan kuka Akeela tace"Haba Guggo ni sam abinda guy dinnan yakemin sam baya min dadi,haka sauran mazan suke?koko don yaga ina son shi shiyasa yake min haka?nikawai Guggo kisa mallakemin shi sai abinda nakeso za'ayi"Ajiyan zuciya Guggo Laure ta sauke tace"Ai wannan dole ne kisha kurumin ki dama kina tunanin zamu barshi haka ne?ai wallahi bazai yuwu ba,gashi yaro Yana neman zama mante malloniya,dole ya zama na yana tafin hannu mu mune muke juyasa wanda ko Aisha sai tarasa kwanciyar hankalin ta,cikin tsananin farin ciki Akeela tasaki dariya"yawwa Guggo na shiyasa nake matukar son ki nufa kin fimun Mom wallahi,domin Mom bata damu da damuwa ta ba"... Mtsewwww! Don Allah dena tadin wannan shashan wake maganar ta?cewan Guggo Laure. Wayan Akeela ne yayi ringin cikin sauri tadauka"hello baby's ya akayi ne?daga can bangaren aka amsa"ok to bari nazo dama ina sasan Guggo ne amma ganinan fitowa,takarisa maganar tana mikewa wayar kare a kunnenta tana fita,cikin jin dadi Guggo Laure ke duban ta don ko babu komai tana mata murnan shiga ahalin GALADIMA FAMILY,a fili tace"Wane Mujaheed?ai Akeela ba tsarar ka bace,kuma ba sa'ar ka bace,duk da nice nan na haifi iyayen ku amma kuma da banbanci"Guggo Laure tayi maganar tana wurgama iska harara. Dai-dai sanda ta isa wajen su Suby alokacin wayar ta tadanyi kara alamar message yashigo cikin wayar,cikin zumud ta dago wayar tana dubawa,sai dai abinda taci karo dashi yasa murmushin nata gushewa,da karfi ta furta"kan ubancan,lallai ma mutanen nan nizasu maida wata 'yar iska wai ko mene?jibi don Allah Suby,tayi maganar tana mika mata wayar ta. "Wai iya kacin abinda suka turo kenan?Suby tayi maganar tana duban wayar,cikin hasala Akeela tace"Gashi kuwa kina gani,amma gaskiya ba'a mun adalci ba,inada hidima fa sosai,ga event din gobe,ranar Friday Kuma kamu haba!tayi maganar tana yatsine fuska. "Ai shikenan sai kiyi maleji da abinda yasamu kawai muma abamu kasammu,wani banzan kallo ta aika mata dashi"bangane me kike nufi ba,abaku kasanku kamar Yaya kenan?bata fuska Suby tayi tare da kura mata ido. "Ea mana ko kinmanta ana bawa kawaye wani abune?aka idama kudin nan bata account dinki ya kamata

Table of Contents

Chapters

87 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});