Chapter 6
Chapter 6
toh. Cike da farin ciki har zuciyar Guggo Laure ta yashe baki tace"Alhamdulillah Allah mungode maka,a zuciya Guggo Laure tace"(ya ubangiji Allah yakai damu ga harawa,lallai Akeela duniya sabuwa,duniya nakine.) Allah yabada sa'a ubangiji yadorashi bisa kawunansu. Da Ameen Ammi ta amsa. Nan Guggo tamike tamata sallama kai tsaye sasan Mom tanufa. Mom taji dadin ganin Guggo don ko babu komai da mijin Guggo da baban Mom uwa daya uban daya,anan suka gaisa Guggo tace"gaskiya Rabi bakida kirki yanzu kiri² dan naman nan ma kindena aikomin dashi sai dai kikaiwa hajiya habi?haka amana yace? Dama ana saka alheri da mugunta?a fakaice mom ta watsama Guggo Laure harara,a zabiri kuwa dan marairaice fuska tayi tace"toh yazanyi Guggo?kiri² baban Aseef ba siyowa yakeyi ba sai lokaci zuwa lokaci,nima kaina baya isata balle nabaiwa wani. Guggo Laure ta kama baki tace"Oh a haka Hasheem sumumi sumumi Amma duk Wanda yaganku yaganku cikin hutu don ke tunda kika shugo cikin a halinmu zaka sheda. Mom tayi dariya tace"gaskiya ne Guggo,amma bajiya akace bakijin dadi ba? Guggo Laure tace"hmmm aikedai bari ai tafiyar nan ta dole nakeyinta,nan Guggo Laure tazauna tabawa Mom labarin duk wani qudurinta kaf nason hada auren Sauban da Akeela. Kirjin Mom ne yayi wani irin mummunan bugawa hankalinta yayi qololuwan tashi,a diririce Mom tace"Guggo wani Sauban din? Harara Guggo Laure ta maka mata tace"Sauban nawa ne a gidannan?to dan uwanta mana nake nufi. Guggo tace"Bari naje rabi yanzu zakiji ankira azahar. Gabadaya har Guggo Laure tagama maganarta tabar farlon Mom bataji ba sai da taji karar rufe kofa tajuyo a hautsine. Mikewa tayi cikin gigita da rudewa tace"Inah? Sauban da Akeela?wallahi bazai yuwuba bazan taba bari Sauban ya auri Akeela ba. Duk irin son da Rammat takeyi masa ana nufin zaitashi abanza ne?wallahi bazai yuwu ba,qanwata Ina ganin yanda takeson Sauban kamar zata rasa ransa,Rana tsaka azo da maganar wata shegiya Akeela?wallahi bazai yuwu ba,Ina wayata? Tayi maganar tare da nufan hanyar wani corridor cikin gigita. _TIRQASHI ANA WATA GA WATA._ _MEKE SHIRIN FARUWA NE?ME MOM TAKE NUFI?DUK WANNAN ABINDA AKEYI SHI ME GAYYA ME AIKIN MA BESAN ANAYI BA,KUDAI KU KASANCE DA ALQALAMIN ÕÙM ÃJMÃL🖊️_ Xahratty Ce🥰 Lallai Alqalami🖊️ yafi takobi 🗡️ 12/2/2023. [3/21, 22:27] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽🦳 Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar⤵️ A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page 05 _Bismillahir-rahmanir-raheem._ _______A tsananin rikice mom take shiyasa koda tashiga cikin bedroom dinta sam hankalin ta baikai wajen phone nata ba,fita tayi daga bedroom din tanufi wani corridor wanda kaitsaye ya sadata da parlon Abba,neman wayar tashiga yi sai dai duk iya neman da tayi bata gani ba ( _Nikoh nace su hajiya mom manya tsaban rudewa a bedroom dinki kika bar wayan😆_ ). Dan siririn tsaki taja tare da fita tanufi bedroom dinta dai,gabadaya ta hargitsa dakin bata gani ba,banda numfarfashi babu abinda takeyi cikin sa'a kuwa idanuwanta suka sauka akan bedside drower dinta,sake watso idanuwa tayi cike da tsananin mamaki,mikewa tayi ta dakko wayar tare da komawa tazauna a bakin gadon hannunta har rawa yakeyi wajen dialing number Rammat,ganin andauka ne yasa Mom kara wayar a kunne bakinta na rawa tace"Hello Rammat kina jina ne?kina gida? Daga can bangaren akace Eah, Mom ta cigaba da cewa"kiyi maza maza kizo inason ganinki yanzu fah,still dai da toh aka amsa mata. Katse kirar tayi inda tafara safa da marwa a cikin dakin. A bangaren su Guggo Laure kuwa bayan sallar azahar duk suka hallara a parlon na Galadima, Galadima,bodejo, Daddy,baba hasheem. Guggo Laure tace"Yaya ayi maganar da za'ayi don Allah saboda nisam bansan sharrin shedanu. Dan murmushi Galadima yayi yace"Laure kenan bari akira yaran duk aji ta bakunan su. Duban Daddy yayi yace"taleeb lalubomin Sauban a wayarsa daganan kace masa su taho da mashahuda.Da toh Daddy ya amsa sannan yafara neman Sauban a wayarsa. Cikin kankanin lokaci kuwa ya dauka inda Daddy yasanar masa da saqon Galadima. Ba'a dau lokaci ba yayi sallama mashahuda na biye da ita,duqawa sukayi cike da mutumtawa suna sake gaishesu,nan Baba Hasheem yadubi mashahuda yace"takira masa Akeela daganan tawuce,amsawa tayi da toh tare da miqewa. Basu wani jima ba itama tashigo sai wani sake karairaya take tamkar iccen da yake gaf da karyewa,samun gefen kafar Guggo Laure tayi ta zauna sannan tafara gaida su Daddy. Gyaran murya Galadima yayi yafara magana. "Toh Alhamdulillah Muhammad wannan taron da akayi akanku kune kai da kanwar ka Akeela gatanan!yayi maganar yana pointing din Akeela,yaci gaba"Toh 'yar uwata Kuma kanwata kakanka Laure gatanan tanaso musake danqon zumuncin mu ta hanyar hada auratayya tsakaninka da Akeela. Da sauri Sauban yadago tare da duban Galadima. "Ita kuma yarinya tana sonka shine nace kaima munason muji ta bakinka kana sonta kokuwa? Sauban mutum ne wanda sam baida boye² kaitsaye yake magana don watarana su Daddy har takaicin hakan sukeyi,bude baki yayi da sauri yace"wallahi Galadima bana sonta,nisam bata cikin jerin matan danake son na aura don haka ku bata haquri,saboda sam bana fatan abinda zai taba mana zumuncin m...... Ko kafin Sauban ya ida abinda zai fada Guggo Laure tafashe da kuka cikin tsananin fusata ta dubi Sauban tace"Baka Isa ba,baka isa ba muhammadu!ubanka Taleeb ma bai isaba balle kai karan kada miya,nikuke so ku watsama kasa a ido?mene nayi muku?lefi ne don Akeela nason ka? Akeela jininka ce kuma 'yar uwanka. "Ko babu komai so muke muqara danqon zumuntan mu. Sauban dafa kai yayi zuciyar sa na tsananin bugawa don har ransa shi baya son hadin zumunta. Cike da bacin rai bodejo tace"dakata don Allah Laure,wani zumunci kike maganar za'a gyara?a gyara ko a bata?yaro yafito yafada ra'ayinshi kuma a neme a tilasta sa,wallahi bazan lamunci cin kashin kowa ba a yanzu wannan son zuciyar taku tafara isatal! Tayi maganar tare da watsa ma kowa kallon banza harda Galadima ( _Omg🤔_ ) Mikewa Guggo Laure tayi cike da jin haushin bodejo tace"lallai ma Yaya bodejo sannu me jika kenan Akeela ba jikar ki bace sai Sauban?yanzu niba zan iya neman alfarman wani a gidan nan ayimun abu baaa?takarisa maganar tare da fashewa da kuka mai tsanani tamkar ba tsohuwa ba,gabadaya hankalin su yatashi idan kacire bodejo da Sauban. Bodejo tace"Laure nice bansan makircin ki ba?kukan d..... "Ya isa don Allah kubar maganar haka, Galadima ya katse bodejo. Wani kololuwan takaici bodejo taji a zafafe tanufi hanyar kofar parlon Galadima don fita,daga murya Galadima yayi yakira bodejo. Sai dai ko waiwaye batayi ba balle asa ran tsayawar ta. Jinjina kai Galadima yayi saboda hankalinsa yatashi,ransa Kuma yabaci,a zafafe ya daka ma Guggo Laure tsawa akan kukan da takeyi tamkar ba tsohuwa ba( _Koda aidama tsoho akwai rikici,sai dai guggo Laure macece see shu'uma._ ) Daddy ne yayi gyaran murya sannan ya dubi Guggo Laure yace"Am Guggo don Allah kiyahakuri kiyi shiru haka za'a San abinyi yanzu kuji gida insha Allah zakiji alkhairi. Galadima yace"Laure meyasa kikeso kibata zumunci gabadaya? Sakin baki Guggo Laure tayi tana duban Galadima,aituni zuciyar ta yayi mata wani fassaran saba. "Yaya! Saboda inason karfafa zumuncinmu shine zakace inaso na lalata?meyasa bodejo batason jinina? kuyahakuri insha Allah bazan sake maganar Akeela da Sauban ba,sai dai na haqura dakai da ahalin ka Yaya,don bazan zauna da wadanda basason jinina ba. Gabadaya a firgice suka
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87