Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 20

Chapter 20

Galadima Family Book 1 Complete Hausa Novel 1,275 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ranar auren sa da akayi kasani ai koh? "Nasani Mom sai dai hakan bedameni ba don sanin wacce zai aura ba kowa bace face bunsura,ai mom idan Sauban ya aure akeey beb ai yaci baya. Mom tace"Toh meya shafeka da cin bayansa?idan yaso ma yaci uban baya,don kullum ni burina kenan dan iskan yaro. Sallama Baba Hasheem yayi ya shigo. Amsawa sukayi nan suka fara yimasa sannu da zuwa,sosai baba hasheem yaji dadin ganin Aseef"A'ah mutanen kaduna yaushe Kuma aka iso? Dan sosa kai Aseef yayi yace"wallahi Baba yanzu bandane da shigowa ba. "Ok to ya kabarsu Kuma? "Lafiya lou wallahi Baba,dama nace Bari nazo na duba ku kwana biyu bamu shigo ba. "Kashiga wajen su Galadima? "A'ah yanzu zanshiga dai. Alhaji kenan to inbanda abinka zaiki shiga ne?dole dai yafara gaisheni tunda nice na haifi abina. "Gaskiya ne wannan,abinda Baba Hasheem yafada kenan yamike yashige corridor din bedroom dinsa. Cikin farin ciki Aseef ya dubi Mom "Please Mom da gaske zan aure zuhra saboda gaskiya yarinyar tayi kota ina! Mom tace"na taba maka wasa ne Aseef? Girgiza kai yayi da sauri. ******** "Kai gaskiya naji dadi Allah yama Bashir albarka ubangiji yasake hada kawunan su, Bodejo ke mgn. Daddy face dinshi dauke da murmushi yace"Ameen ai gabadaya kayan na 15 millions ne yahada musu babu abinda bai siya musu ba har kayan kitchen. Baba hasheem yace"Allah dai yasaka ma Yaya da alkhairi. Da Ameen gabadaya suka amsa, Galadima yace. "To yaushe zasu dawo? Daddy yace"insha Allah yace"kaitsaye ma gobe nan zai iso don yanason ganin Zuhra. Dariya Bodejo tayi tace"Kai sadeeq na sangarta yarinyar nan matuka. Dariya duk aka sanya. Washegari wajejen bayan magrib Daddy ne da Ammi ke zaune sunayin lunch,wayar Daddy ya nemi neman agaji,da sauri ya dauka Yana murmushi saboda sunan Abbie da yagani,sallama yayi. Nan aka fara magana tacan bangaren. "Eah nine lafiya kuwa?Ina me wayar yake ne?daga can bangaren aka sake magana. A gigice Daddy yamike yana furta" _INNALILLAHI WA INNA ILAIHIRRAJI'UN_,Ammi ma mikewa tayi tana Daddyn yara lafiya kuwa? "Sadeeq!Sadeeq!! Aisha Sadeeq yayi hatsari shida bilkisou. "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un a lokacin ne Baba Hasheem yashigo shima apartment din Daddy cikin rudu"Yaya!Yaya!! Dagaske ne? Wani yunkurawa Daddy yayi cikin jarumta ya nufo Baba Hasheem,Kama hannunshi yayi. _YANZU FA WASAN ZAI FARA MASOYA GALADIMA FAMILY_💃💃💃💃 Xahratty CE🥰 Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️ 13/3/23. [3/21, 22:27] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳 Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar⤵️ A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page 19/20 _____A gigice suka nufi apartment din Galadima a dai-dai nan wayar Daddy yafara ringing, cikin rudewa ya dauki wayar,daga can bangaren aka fara magana. "Alhaji Taufeeq majinyacin yana cikin wani hali don sai sunan ka yake ambata yana cewa kazo. Bakin Daddy yana rawa ya dubi Baba Hasheem yace"Hashim mutafi asibitin ko kasan ko wane asibiti ne? Baba Hashim yace"sun sanar dani muje kawai nan suka nufi motar Baba Hashim. Tsananin rudewa kuwa Mashahuda tashiga don duk abinda ke faruwa akan idon tane da tsananin gigita tashiga apartment din Bodejo tana Kiran sunanta. Bodejo dake zaune tana shafama Galadima man zafi a kafa ta dago tana cewa"ke kuwa Mashahuda wani irin Kira ne kikeyimin haka mai gigitar wa? A rude takariso tara da durqushewa a gabansu tana sauke numfashi akai-akai. "Bodejo Daddy sun tafi asibiti yanzu aka kira a waya Abbie da Ummie sunyi accident a hanyarsu ta tahowa daga airport. "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un wane Abbie din? Bodejo tayi maganar tana gyara zanin ta da yake neman sabulewa. Galadima yace"natsu Mashahuda kiyimana bayani. Nan Mashahuda ta sanar musu da duk abinda ke faruwa a lokacin ne Kuma Ammi, Mom,muneefa da yaseer suka shigo parlon. Cikin muryan tsawa Ammi tace"menene haka Mashahuda waya aikoki?haka ake fadan sako. Daga musu hannu Galadima yayi cikin muryan dattaku yace"duk ku zazzauna. "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un!!! Kalmar da Bodejo take ta fada kenan,hankalin ta yayi kololuwan tashi ga tsufa ga rudu,sai da Ammi da Mom suka kamata suka zaunar da ita. GALADIMA wayansa yaciro yafara neman layin Daddy,sai dai ba'a daukan kiran,maida kiran yayi ga Baba Hashim ba'a dau lokaci ba tadauka,cikin kamewa Galadima yayi sallama. Daga can Baba Hashim yadauka saboda a rude yake don muryansa har neman disashewa tayi saboda kuka. "Hashim lafiya meke faruwa ne? "Galadima ga munan dawowa yanzu,yakarisa maganar muryanshi na rawa. "Mekefaruwa ne anan ina tamabayar ka meya same abubakar?fashewa da kuka Baba Hashim yayi yace"Allah yadauki rayuwansa wanda yafimu sonsa ya amshe abinsa Galadima.Runtse ido Galadima yayi batare da yasake magana ba yakashe wayan. Cikin daburcewa Bodejo tace"malam meyasame abubakar din? "Gasunan a hanyar dawowa gida,amsar da yabata kenan a takaice. Dai-dai nan Zuhra tashigo parlon sai dai babu wanda ya lura da ita. "Don Allah malam kamin bayanin meya same dana abubakar? Bodejo tafada tana me fashewa da kuka. Sukansu su Ammi hankalinsu a tashe yake. "Kuyi masa addu'ah Allah yakarbi rayuwarsa, Allah yamasa cikawa......wani irin kara da aka kwala ta bayansu yasasu gabadaya juyawa. Zuhra ce a take anan tafadi sumammiya. Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un!!!!shine kalmar da gabadaya 'yan parlon ke ambata cikin tsananin rudewa, Ammi dasu mashahuda suka nufo wajen zuhra. Mom da Galadima suka nufi Bodejo saboda wani jiri da yadauke ta tanemi faduwa. 9:11 Kafin kace me gida yacika tam da jama'a bakajin komai sai tashin koke-koke na mata don ankawo Abbie gida,daga Daddy har Baba Hashim a gigice suke,me dauriyan ma Galadima ne. Makota duk sun cika gidan,ana haka sai ga Abba dasu mommy tare dasu Laila duk sun iso saboda shima sanda sukayi accident din ankirashi kaitsaye asibitin yanufa yacidda ai dan uwanshi yarasu sun nufo gida. Duk Wanda yaga ahalin nan a daren nan sai yayi musu kuka saboda tausayi, Zuhra kuwa tana apartment din Ammi ankira family doctor dinsu yaduba ta tare da samata drip da alluran bacci,saboda wasu sunbatu da mimmikewa da tafara. Gawar Abbie kuwa a daren suka shiryashi tsaf sai gobe karfe tara na safe za'a kaisa(kwanan keso,ake cewa Koh?🤔). Bodejo fifita su Mom ke mata saboda ta rude. Su Daddy kwana sukayi suna ma Abbie karatun kur'ani, taufeeq shikan shi a gigice yake yafita daga hayyacinsa. Washegari zuwa karfe takwas Galadima family yacika tam da jama'a dangi da masoya da makota,don abokan Abbie nanan Mai din da kaduna da yawa suna wajen, Maryam na Lagos ma ta iso abinka da jirgi itada mijinta da yaranta,labeeba dai suna hanya 'yan Canada. Mahaifiyar Ummie da kannenta maza Suma sun iso da hajiya Zainab. Duk Wanda yaga Zuhra sai ya tausaya mata saboda yanda takoma a kwana daya kawai ta gigice fuskarnan tayi jaa idanuwanta sunyi luhu luhu,mommy ce da Aunty Maryam rike da hannunta suka nufi babban parlon Galadima inda gawan Abbie take,mutane ne cike a parlon ana masa addu'ah,sallama sukayi suka shiga da ita,kowa hankalinsa yadawo gareta,dukar da ita Aunty Maryam tayi gaban gawar,dai-dai kunnenta ta mata magana"Banda kuka kinji? addu'ah zaki masa. Hawaye ne masu zafi suke rige-rigen zubo mata,hannunta na rawa tadan bude fuskan Abbie. Fuskan nan banda sheqi babu abinda yakeyi don zaka zata murmushi ma yakeyi kamar kace masa ya tashi. "Allah yajikan ka Abbie, Allah yagafarta maka ubangiji yamaka rahama, Allah yasadaka da mala'ikun rahama Abbie,kaine uwana

Table of Contents

Chapters

87 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});