Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 41

Chapter 41

Galadima Family Book 1 Complete Hausa Novel 1,291 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

shidin ba muharraminta bane,kuma dole zata bukaci wani abu kamar shiga toilet da sauran su. Wannan karan sake tamke fuska yayi yana maida duban shi gabadaya akansu yana kokarin magana, Abba ne yarigasa"Hakan ba matsala bane kawai kuje gida don muma munsan da hakan kuma munzauna a islamiya ba jahilai bane mu. Babu wanda ya sake magana a cikinsu duk tashi sukayi suka fita ko wanne da tunanin da yake a cikin zuciyar sa, Ummie kuwa bataji dadi ba ko kadan sai dai bazata iya nunawa,cikin sanyin jiki suka nufi hanyar fita,duban Taufeeq Daddy yace"maza kaje ka maidasu gida dare nayi,amsa yayi cike da girmamawa yana me bin bayan su,muryan Sauban suka tsinkayo"Daddy taya zanyi jinyar ta?naga hakan sam be dace ba wallahi ni bansan ma yanda zan kula da ita ba. Kafin wani yabashi answer doctor's din sun fito ko wanne na share zufa,karisowa Doctor Ahmad yayi Yana duban su Daddy"Alhaji idan babu damuwa zaku iya samu na a office,yana gama fadar haka yanufi office dinsa,kaitsaye rufa masa baya sukayi. Waje yabasu suka zauna,nan suka shiga gaggaisawa da juna zuwa can ya sauke ajiyar zuciya yana duban fuskokin su"To Alhamdulillah munyi nasarar shawo kan matsalar tata ba wani abubane face damuwa wanda ya haddasa mata jinin ta yadan hau kadan tare da ciwon kai kunsan hawan jini ga zazzabi kuma a gefe daya,sai dai insha Allah munyi nasarar gano matsalar Allah yakara lafiya,amma gaskiya kuyi kokarin ganin kunji meye damuwar tata domin kuwa idan aka zuba mata ido a haka to akwai matsala,ajiyan zuciya suka sauke gabadaya Abba ne yayi karfin halin magana"insha Allah likita zamu kiyaye Allah yakara mata lafiya"Da Ameen gabadaya wajen aka amsa dashi suna me mikewa,rakasu Doctor Ahmad yayi yana tambayar me zama,duban shi yayi yace"ga Sauban nan shi zai zauna da ita yayi jinyar nata,da mamaki yake duban su don yasan alakar dake tsakanin Sauban da zuhra batare da nauyin baki ba yace"Amma Alhaji ina ganin da ansamo 'yar uwanta macece tayi jinyar ta idan ma babu sai mu duba muku a nurse's din mu. Daddy ya danyi murmushi yace"Babu bukatan Doctor Ahmad don shidin mijinta ne...... Yana kare fadar hakan sukayi gaba abinsu, daga Sauban har Doctor Ahmad kamewa sukayi a tsaye kamar status saboda mamaki,wani murmushin jin dadi Doctor yayi,yana me dafe kafadar Sauban wanda yayi suman tsaye banda bugawa babu abinda zuciyan sa ke masa yarasa me yakeji a zuciyar sa,farin ciki yake ko bakin ciki?baisani ba,cikin tsananin murna Doctor yace"Na taya ka murna oga Sauban Ashe auren gata aka maka? congratulation!wucewa yayi yana cigaba da mamaki don shima yaso ace ya mallake Zuhra a matsayin matarsa,yana tsaye jikinsa na sake sanyi,ganin tsayuwar babu abinda zai masa yasa ya juya,direct dakin yanufa cikin tafiyar da na izza da kasaita,a hankali yaka ma handle din ya murda,a makoshi yayi sallama tare da kutsa kai cikin dakin da aka canza mata (VIP) idanuwan sa kuri akan kyakkyawar fuskan ta wanda yini guda kawai yasa ya yamutse saboda ciwo,kallonta yakeyi kawai yakeyi jikinsa na sake sanyi a gefe guda yana jin taya shi zai iya rayuwa da mata har biyu?to ta inama shi zaifara?tambayar da yayi ma kansa kenan.Haka ya samu kan kujerar dake gefen gadon nata ya zauna batare da ya dena kallon ta ba yana kissima abubuwa da dama akanta,duban agogo yayi yaga sha daya da kusan rabi ne ma na dare,lumshe ido yayi batare da yanajin dadin zaman kujerar ba. A can gida kuwa duk da mamakin su Daddy suka dawo tare da tambayar kawunan su a zuciyoyi mezesa suyi haka?shi kanshi Taufeeq mamaki ne fal ransa,sai dai rashin samun me Basu amsa yasa kowa yakasa furta komai,koda su Aunty Maryam suka isa apartment din Galadima tambayan su me jiki sukayi tare da me kwana da ita,cikin alhini suka basu amsa da wai Sauban ne zaiyi jinyar ta,ganin fuskokin tsofaffin sukayi normal babu wani alhini, Galadima yace"Hakan ma yayi Allah yabata lafiya ya kuma tada kafadun ta,da Ameen suka amsa jikinsu nasake sanyi da lamarin ahalin nasu masu cike da abubuwan mamaki.A sashin Ummie kuwa sun tadda Amma har tayi bacci abinta don dama kafa ya matsa mata, Adda Zainab ne keta sababi akan mezesa su Daddy suyi hakan?ita kuma Ummie takasa magana kan abinda yake faruwa,ajiyar zuciya Ummie tayi tace"bazan iya tambaya ba Adda domin koni dana haife Zuhra bankai bayin Allah nan sonta da kaunar ta,ni ina tunanin suna da kwakkwaran dalilin su nayin haka don dai haka kawai bazasu yanke wannan hukuncin ba. Adda Zainab tace"Hmm to ai shikenan Allah ya kyauta meson dangin miji ke dama sam bakison a fadi lefinsu koma dai menene?ai hakan dai bedace haba jama'a sai kace ana garin ga6a²,shiru ita dai Ummie tayi bata tanka ba.Hajiya Aliya ce tadubi Adda Zainab tace"Niko aminiya yaushe Alhaji iliyasu zai dawo ne?saboda munada biki acan gombe inaso da muje tare da kene,kinsan hajara na zata aurar da 'ya next week,cikin mamaki Adda Zainab ke duban hajiya Aliya tana sakin dariya"Eyye aminiya kina nufin hajara har zata aurar mu muna zaune?lallai aiko ya kamata muje ma hajara biki ai komai zaizo da sauki nima gobe zan koma nafara tarban dawowar shi don jibi zai dawo yace jirgin 4:00 zai biyo, cikin farin ciki hajiya Aliya tace"Kai naji dadi ai nida kaina ma zan tambaye shi domin nasan zaiji dadin hakan sosai,dariya Adda Zainab tayi tace"gaskiya kam zaiji dadi sosai Allah yadawo min dashi dai lafiya kinsan yatafi yana fushi danine don naki binsa sai a waya muka shirya,hajiya Aliya tace"Ai tafiye²n nan irin nasu ba kowace mace bace zata jura kinji kiyi zamanki anan wallahi, Adda Zainab tace"yanda kikajin nan. Ummie najinsu sai dai bata tanka ba don asanin kanta duk abinda za'a cema hajiya Zainab akan hajiya Aliya ba yarda zatayi ba saboda son da take mata,tasani yanda takeson hajiya Aliya bata mata irin wannan son tun suna secondry school,sabanin ita da take tsananin son yayar tata,mikewa tayi don nufan dayan sashin nata don duba sauran jama'ar nata nan tabarsu suna cigaba da hirar su,da wani irin mugun kallo Adda Zainab tabita dashi tanajin kamar tatashi ta makure ta tahuta. Bayan fitanta cikin dacin murya Adda Zainab tafara magana"Aminiya boka hatsabibi bai kyauta minba,ba haka kukayi dashi ba nidai duk aikin da yabani nayi nayi amma kina ganin ma idon ki babu abinda yayi aiki ni garas ma naga takari,gaskiya zan canza wani bokan ki samo min wani nikam bazan iyaba wallahi so ake ciwon zuciya da bakin ciki su kashe nine ko mene?Hajiya Aliya tace"Kash!Kash!! Dadina dake Aminiya gajin hakuri,munyi magana dashi nayi masa korafi sai dai yace lefin ki ne wallahi domin kuwa duk aikin da kikayi sun lalace sai dai besanar dani yanda akayi suka lalace ba,amma kinsan idan kika fadi wani magana mara dadi akan boka hatsabibi kema baki masa adalci ba,shekara nawa yana miki aiki kuma anga dacewa don kawai wannan anyi kuskuren da kecema kikaja sai kifada haka?wallahi banji dadi ba idan yajiki kuma babu ruwana.Adda Zainab tace"gaskiya ne idan nafada wani abu nayi butulci aikam zanje nane mesa da kaina domin magance matsala ta. Hajiya Aliya tace"Da dai yafi kam,haka suka cigaba da tattaunawa akan matsalolin su har suka raba dare. ********* Wajen karfe 2:40 ta farka a

Table of Contents

Chapters

87 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});