Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 26

Chapter 26

Galadima Family Book 1 Complete Hausa Novel 1,244 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

har wani irin sara masa yakeyi. Haka malam baba ya cigaba da aikinsa. Zuwa can yadubi galadima yace"Alhamdulillah malam Muhammad nayi nasarar magance matsalar nan sannan na hada musu wani dafa'i wanda insha Allah babu abinda zai sake faruwa a tsakanin su,komin tsafin me tsafi kuwa da yardan Allah. "Sannan akwai wasu addu'o'i da zan basu da ita da 'yan wanda zasu lazumci yinsa da yardan bi'iznillah babu abinda zaifaru. Duban Sauban yayi yace"Shima takwaran ka na hada mishi wasu zan bashi domin tabbas za'ayi kokarin bibiyar wanda ya lalata aikin koda kuwa ba'a gano shiba sai sunyi kokarin sabauta ko wanene. "Mungode malam baba Allah yasaka da alkhairi ubangiji yaja kwana Allah yayima rayuwa albarka. Cewar Daddy kenan cike da tsananin jin dadin yadda malam baban ya warware musu komai da yardan Allah da temakon sa. Godiya sukayi sosai inda Galadima yake cemai ga sadakan abinci nan yayi ma almajiran sa sannan anbiya mishi kujeran hajji. Nan yashiga godiya duk da ya nuna musu sunfi karfin haka a wajenshi Amma ina. ********* Sai yamma lis suka isa qauyen wajen bokan inda shima driver hajiya Aliya dan gari ne don suna shiri sosai ita dashi don har aikoshi tanayi wajensa a sirrince. Gidan da suka saba sauka a dan quyen gefen gidan boka nan suka sauka,zuwa bayan sallan isha'i suka shiga wajenshi. Da wani banzan kallo ya tarbe su,nan danan hajiya Aliya tasha jinin jikinta,a dan tulluwan kasan da suka saba zama suka nufa zasu zauna. "Kulllll! Ahirrr dinku Aliya ka kasa nan ku zauna. Jikisu har tsuma yakeyi saboda yanda yayi maganar. "Aljanu su huci zuciyar ka,shedanu su huci zuciyarka yakai mebiya mana bukatun matsalolin mu( _wa iyazubillah_) "Ya isa hajiya Aliya kunfi kowa sanin abinda kukamin kun batamin aikinda tunda nake babu aikin da nasha wuya akansa sama da wannan,me kuke zaton yafaru?yayi maganar yana zaro musu mummunan idanun saasu kama da attarugu saboda ja. Kunsan aljanu nawa aka konamin a aikin nan?tabbas wadanda sukayi aikin nan ba kananun bane,duk sharrin dan dagiya da masanu sai da aka konamin su,duk cikin aljanuna babu jajirtattu irin su. "Wallahi bazan kyale ko waye ba sai na dauki fansa akan abinda akayi musu koba yanzu ba. Su dai su hajiya Aliya sun kasa magana banda rawar jiki ba abind sukeyi. Duban dayan yayi yace"yanzu me kikeso a musu?don shiryawa sun ruga sunyi itada diyar ta sai dai wani zancen ba wannan ba. Jikinta na rawa tafara magana cikin rawar murya. "Duk da 'yar uwata ce ubanmu daya amma nayi mata wani irin tsana mafi muni, duk da cewa mahaifiyar ta tafifitani akanta tanuna min soyayyar da bata nuna mata ba amma inajin muguwar tsanar ta a zuciya ta, takasance ta taso da soyayyar mutane da dama ne a zuri'ah mu harda mahaifinmu,wallahi boka hatsabibi bana sonta kuma ba zan taba sonta ba,inason ka sabauta min bilkisou yanda ba zata moruba. "Hhhhhhhh boka hatsabibi ya shiga qyalyqala dariya,zuwa can ya daure face. "Aikin ki sai na sake nemo wasu aljanun kuma shedanu saboda kinsanta da rukon addini bata wasa da azkar to zanyi shiri na musamman akanta,don yanzu haka tana kwance a asibiti jinita ya hau a dalilin karya sihiri nan da akay ......... "Allah dai yakashe ta ma kihuta aminiya,cewar hajiya Aliya. Wani kallo boka ya watsa mata. "Ba Amin ba nine nan ajalinta,mutuwar ta a hannu na take,sai dai wannan aikin ba kamar ko wanne bane don inada tabbacin duk me zatayi se yaci,amma kema zakiyi wani aikin daga bangaren wasu ayyukan. "Ni Kuma?tayi tambayar tana zaro idanuwa. "Eah ke!wannan karan mata biyu zasuyi amfani dake,bi ma'ana zasu mu'amalance ki. "Kamarya yaya boka? Duban hajiya Aliya yayi yace"kiyi mata cikakken bayani. Nan hajiya Aliya tashiga yima aminiyar ta bayani yanda zata fahimta,ai bata bari rakarisa ba tadafe kirji tace. "Ni Zainab bantaba madigo ba kuma banjin zan iya aikatawa. Daga hajiya Aliya har boka daure fuska sukayi. Boka yace"to duk inda zaki babu me yimiki maganin matsalar ki muddin baki aikata wannan abin da nace ba. "Mtsewwww!hajiya Aliya taja tsaki tace kika ma aikata wadanda sukafi wannnan muni da sabo wannan ne bazaki iya aikatawa ba lallai baki shirya ganin nasara ba. "A'ah ba haka bane aminiya da girma na da komai aganni ina madigo? "Waye zai ganki?cewar hajiya Aliya. "Boka hatsabibi yace a gabansa za'ayi fah 😥 "Mtseww Kinga idan bazaki iya ba tashi mu tafi makwancin mu zuwa safe mu tafi gida. "A'ah matsalata dake saurin fushi aminiya,cewar hajiya Zainab. "Toh ai ke dince da kayan haushi,idan kin shirya kiyi magana. Da sauri ta daga kai alamun ta amince. Nan boka hatsabibi ya rufe ido yana wasu yare kafin kace wani abu wasu katta kattan mata biyu bakake sun shigo ta kofan,babu sutturan arziki a jikinsu. Ba hajiya Zainab kadaiba,hatta hajiya Aliya sai da ta hadiye wani irin miyau na firgita. ***** *KADUNA* **** Ansamu Ummie ta farfado tana tare dasu mommy, Amma da kannen ta maza, Abba ma yana asibitin don su Daddy ance suna hanya. Hawaye kawai takeyi tana ambatan sunan Zuhra. "Amma na manta da Zuhra a babin rayuwata wallahi ni naman ce wai bayan Taufeeq inada wata diyar,meyasa na aikata mata hakane fisabilillah? Takarisa maganar tana zubar da hawaye masu dumi da zafi. "Ba laifinki bane Ummie wannan duk wanda yagani ko yaji labari yasan aikine na sihiri akwai farraqu a lamarinku,ba gashi ba yanzu da akayi magani komai ya warware? Mommyn yara bazaki gane me nake nufi ba,Abbie ya rasu batare da na cika mishi burin shi ba naganin naja diyata a jiki,ya rasu yana tausayin diyar shi da fargaban halinda zata shiga na kiyayyata bayan bashi,kuma hakan baitaba shafan zaman mu ba. "Allah yasani duk wanda da sa hannunshi akan wannan lamarin ban yafe ba kuma sai Allah ya bimin hakki na. "Wallahi kuwa bazamu yafe ba, Amma tafada tana kuka. Dai-dai nan ne kuma su Daddy, Galadima, Bodejo, Ammi, Mom, Sauban, Zuhra suka shigo dakin bakunan su dauke da sallama. Ummie jikinta har rawa yake ta sauko daga bed din ta nufosu,zazzaro idanuwa takeyi kawai tana laluben ta inda zata ga Zuhra. Zuhra kuwa ganin ta nufo inda take ne yasa jikinta kama rawa ta runtse ido tare ruqunqume kwankwason Sauban gam,fadi take. "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un don Allah Ummie kiyahakuri babu abinda na miki please bazan kara ba,na hadaki da Allah please kiyahakuri wallahi. Shesshekan kukan da tadinga ji daga maban bantan bakuna ne ya sata bude ido. Ummie tagani a durqushe tana kuka mai sauti, Amma ma da Bodejo kukan sukeyi. Duk da haka jikinta rawa yakeyi takasa sakin Sauban don ita batasan tama rikeshi haka ba,Ammi ne ta matso tare da kamota tazo da ita har gaban Ummie inda take durkushe. "Zuhra Ummien ki tadawo gareki, Ummien ki mai sonki tadawo gareki dama banace miki ba?kidena jin tsoro kinga kinsata kuka koh? Kamar wawuya haka zuhra takoma tana kallon Ummie tana kallon Ammi. Kamo hannunta Ummie tayi wanda gabadaya ilahirin jikinta yashiga rawa tafara magana. "Zuhra diyata kiyafemin bansan abubuwan da nake mikiba a baya hasalima nina mance ma na haihu tun washegarin sunan na manta ki a shafin rayuwa ta,don Allah kiyafemin. "Ni maisonki ne,ni me kaunar kine,ina tsananin begenki,please diyata forgive me my babe. Xahratty CE🥰

Table of Contents

Chapters

87 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});