Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 21

Chapter 21

Galadima Family Book 1 Complete Hausa Novel 1,259 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kaine ubana wanda yafini sonka yadauke ka a lokacin da nake tsananin bukatan ka, Allah ne gata na kaine gatanaa.....takarisa maganar tana fashewa da wani irin kuka. "Abbie halinka nagari yab.....numfashinta ne yafara seezing da sauri Mommy ta kamata suka fita,kowa cike da tausayin ta yabita da kallo,anan aka fito da gawar. Nan fa gida yasake haumutsewa da koke-koke na mata, Laila ma atake anan ta fadi ta Suma garau. Guggo Laure da shigowan ta kenan da jiniyar kuka tafara"wayyo Allah mutuwa me yasa zaki Mana haka?me zesa kidaukar mana yaron kirki?ga sauran can,sai kika tafi mana da mai hakuri. Takarisa maganar tana Jan majina. Allahu akhbar kullu nafsin za'ikatul maut,duk Mai rai sai ya dandani dacin mutuwa Allah yajikan Abbie 🤧 Sai wajen la'asar ya taufeeq da Kareem da wani kanin Ummie suka daukota daga hospital sosai ta galabaita itama sannan mutuwan Abbie ba karamin girgiza ta yayi ba,takasa mance maganganunsa wadanda sosai su sukafi tasiri a zuciyar ta( _Bilkisou inaso kisani bana fatan na mutu banga kin daidaita da Zuhra ba._ ) sosai wannan maganar yake dawo mata a kai saboda sosai tafara tsorata da lamarin nata ita kanta hakan yasa hawayen idaniyar ta suka gaza tsayawa. Ammi ne da Mommy da Mom suka kariso tare da kama Ummie kaitsaye apartment din Abbie nanan suka nufa don su Amma da hajiya Zainab suna can zaune. Zazzabi ne me zafi ya saukar ma Zuhra saboda kukan da tasha gashi har muryanta ya dishe,mijin Aunty Safeena da mahaifiyar shi sai yayyen shi mata su biyu sunzo don Shuraim ma yajawo su a motar,su kansu sun tausaya ma ahalin musamman ma Zuhra don da alama Abbie irin mutanen nan ne masu tsayawa a rai. Koda Zuhra tafito don su gaisa da Shuraim kasawa tayi saboda kukan da yaci karfinta,ga abinci da sam ba cinsa take ba. Tabbas Galadima jarumin tsoho ne don kaf 'yayan sa yafisu dauriya kukan zuci kawai yakeyi wanda kowa yasan yafi na fili azaftarwa da radadi. A ranar Aunty Labeeba itama ta diro da mijinta sosai fa gida ya cika. *MALAYSIA* Sosai yashiga rudu da tashin hankali da rasuwar Abbie din,don har Saida zazzabi me zafi yanemi kwantar dashi,duk da a bayyane ba lallai ka fahimci hakan ba. Sosai Abba ya kwantar masa da hankali duk da yaso yazo kasar a ranar amma baisamu izinin haka a wajen na sama dashi ba dole ya hakura,sanar dashi halin da Ummie tashiga shima sai yasake gigitashi. A haka yadinga dai zuwa office din zazzabi nata cinsa a tsattsaye,duk da kullum cikin video call yake da Taufeeq ko Ammi akan jin halin da Ummie ke ciki. ****** Bayan kwana uku da rasuwar Abbie,anan ne wasu daga cikin dangi da 'yan uwa suka wawwatse sai dai na jikinsa suna nan. Anan Daddy yakira meeting parlon Galadima,sosai kowa ya halarta a cikin ahalin gidan,Banda Guggo Laure dai,'yayan Galadima kawai ake bukata. Nan Galadima ya bude taro da addu'ah yayi addu'o'i wa Abbie, Daddy kuma ya amshe. Nasiha maishiga jiki yafara yiwa Ummie,tare da sanar da ita abinda dan uwansa yamutu da burin ganin yacika shine shiryawan ta da diyar ta Daddy ya cigaba"Sadeeq yace muddin kika ja marainiyar Allah a jiki kingama masa komai,ga Hashim nan abinda yadinga maimaita wa kenan kafin Allah yadau rayuwansa yakuma CE shi yayafewa kowa don bashi da kullin kowa a ransa. "Bilkisou kiji tsoron Allah ki kula da diyarki ki cikama abubakar burinsa mudai a iya saninmu baki da matsala kuma Alhamdulillah a kullum abubakar cikin yabon kyawawan halayyarki yakeyi illa matsala guda shine wannan matsalar,Wai ko kin manta Zuhra nada ciwon zuciya ne?kinsan dalilin da yasa a koda yaushe abubakar ke debe mata kewa kenan?don Allah menene matsalar bilkisou? Cikin muryan kuka Ummie tace"inason ta amma narasa meyasa nakejin tsanar ta? wallahi ina kewanta da begenta sai dai sam banaso ta rabe inda nake. Gyararan murya Abba yayi yafara magana"Ina ganin Yaya kamar maganar Yaya Sadeeq gaskiya ne da koda yaushe yake cewa shi yana zargin sihiri a lamarin,nima kuma gaskiya na sake a minta,da sauri Aunty Maryam tace"wallahi kuwa Yaya nima haka nake gani. "Hmmm nidai nace saboda taya uwa zata ki danda ta duka ta haifesa?sannan ko son da aka haifi Zuhra Bilkisou na tsananin son ta daga baya ne komai ya canza,Ammi tayi maganar. Shidai Taufeeq kansa na duke don shikadai ne a yaran gida yake parlon. Baba Hashim yace"toh me zehana anemi malamai masana addinin islama aji ta bakinsu? "Wannan gaskiya ne Yaya, cewar Labeeba. GALADIMA ne yayi gyaran murya,gabadaya wajen yayi tsit magana yafara kamar haka. Xahratty CE🥰 Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️ 14/03/23. [3/21, 22:27] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳 Story&Written By *FATEEMA ZAHRA LAWAL* Marubuciyar⤵️ A DALILIN'YAR TSINTUWA. MIJIN ZAHRA. DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book. RUHIN AMRITA (FATALWA CE). Now *_GALADIMA FAMILY_* Page 21-22 _Bismillahir-rahmanir-raheem._ ___Sosai GALADIMA yayi nasihohi masu shiga jikin duk wani wanda yake zaune a wajen,inda a ka tsaida magana za'a ma wani aminin GALADIMA magana dake wani kauye anan maidugrin don masanin harkan sihiri ne kuma yana bada magani sosai,nan aka sake yiwa juna gaisuwa kafin kowa ya watse. Bayan kwana daya,ana masu amsan gaisuwa suka cigaba da tururuwar zuwa,hajiya Biba ma tazo ganin yanda Galadima family yasake tsaruwa ne yasa tasake kudira a ranta cewa lallai yakamata Rammat ta shigo gidannan,sawa tayi aka kaita sashin ammi,anan fa tadinga fadanci a wajen Ammi tare da yabon halayyan Sauban. Ammi tacika da mamakin hajiya Biba amma sai sam bata nuna ba,itakuwa Mom ta cika tayi Damm saboda yanda taga hajiya Biba na neman kwanta ma Ammi tayi wuff tace. "Hajiya kizo muje kiyima iyalen Abbie gaisuwa mana. Mikewa hajiya Biba tayi Rammat tana bayanta itama cike da kissa ta rissinawa Ammi tana mata sallama. Kaitsaye apartment din Abbie nanan suka isa sosai hajiya Biba tanuna jimaminta,itakuwa zuhra tana rakube gefen Ummie jikin kafar Adda zainab. A haka rayuwa ta cigaba da tafiya har yau gashi bakwan rasuwar Abbie a ranar ne kuma Sauban yadiro garin babu zato bare tsammani,idan kallesa baka isa ka tantance a yanayin da yake ba sai dai fuskar sa da take a dinke,ta gabanshi tazo ta wuce cikin sanyinta long hijjab ne a jikinta brown colour yayi mata kyau sosai,fuskar ta daka kalla kasan mutuwar tana dukanta. Ta wutsiyar Ido yabita da kallo har tashiga wajen Ammi,kaitsaye shikuwa apartment din Ummie yashiga bakinsa dauke da siririyar sallama,da Ummie suka fara hada ido,ai tuni tasaki kuka mai tsuma zuciya,da sassarfa yakariso gareta da sauri ya kama mata hannu. "A'ah Ummie don Allah kada kiyi kuka Abbie insha Allah ya dace,ko nima so kike kisanya ni kukan Ummie?please. Girgiza masa kai Ummie tashiga yi tanajan gunjin kukan hawaye wani na riga wani muryanta na rawa tace"Sauban Abbien yara ya tafi ya tafi yabarni da nauyij zuhra ya zanyi please? "Kiyahakuri don rashi mungriga da munyi Allah yajikan Abbie ubangiji yasada sa da rahamarsa. Da Ameen 'yan dakin suka amsa don a yau zasu bi jirgi su koma har da Ummien ma don tace can kaduna zata koma,shima Abba da mommy zasu tafi. ****** "Zuhra kifa dunga cin abinci koko so kike ki dora ma kanki wani lalurar? Ammi tayi maganar tana jawo Zuhra. Hawaye ne yashiga yimata sintiri, Laila takama hannunta"Zuhra

Table of Contents

Chapters

87 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});